Irin wannan matsala su akan kira da [Birth injuries] wato raunukan haihuwa.
Sukan samo asali ne ko dai a dalilin:
- Cystic fibrosis inda gland ɗin da ke Samar da majinar da ke taimakawa da saisaita numfashi ke samun matsala
- Ko fuskantar matsalar rashin jini a yayin goyon ciki zuwa lokacin haihuwa
- Ko ƙarancin iska yayin da jaririn ya faɗo musamman in ya taho da sauri
- ko sanadiyyar shigar ƙwayoyin cuta cikin laka (spinal cord) zuwa ga mayanin da ya rufe ƙwaƙwalwa wato (meninges) da akan kira da meningitis (sanƙarau).
- [Neonatal disorder]
- Hakan na faruwa ne ta sanadiyyar rashin samun cikakkiyar kulawa ga mai ɗauke juna biyu, saboda akwai irin abincin da ya kamata mace ta yawaita amfani da su a lokacin da take ɗauke da juna biyu
- Haka kuma akwai wanda bai kamata yawaita amfani da su ba
- Rashin zuwa Awo akai-akai
- Saboda yana da kyau macen da ke ɗauke da juna biyu ta ringa zuwa ANC domin duba lafiyarta da na jinjirin da take ɗauke da shi a cikinta.
- Rashin samun cikakkiyar kulawa takan haifar da matsala babba a lokacin haihuwa, kuma yana da kyau mu san cewa duk lokacin da mace take da juna biyu garkuwar jikinta tana raguwa saboda {Hormonal inbalance}, wato duk wani hormones nata zai fara yin (hypersecretion) ruɓanya aikinsa.
- Ko kuma haihuwa a gurin da yake ba cikakkiyar tsafta inda saboda raunin garkuwar jikin jariri ƙwayoyin cuta kan yi wuf su shiga huhunsa su yi ta hayayyafa cikin sekonni su galabaitar da jaririn inda hakan shi kan kai shi ga mutuwa.
- Jinkiri: Wani lokacin ma da sakacin matan sai an rasa yadda za a yi ake nufo mu inda tun a gida wani yaron ya riga ya galabaita ya gama cin karo da a lot of birth injuries,ko ya jirkice a ciki ko yayin yunƙurin naƙuda.
Shawara
A gaskiya mun so duk mai juna biyu ta shirya asibitin da za ta je ta haihu musamman mata masu haihuwar fari.
Domin karanta dalilin da yasa kake jin Kasala A Duk Sanda Nai Jima’i Ko Inzali Danna nan