Rabiu Musa Adam
Allah SWT ya ce:
“Lallai su matasa ne, sun yi imani da ubangijinsu sai muka kara musu shiriya”
MATASHIYA: WANENE “MATASHI”
Majalisar ɗinkin duniya dangane da abinda ya shafi shekaru, ta faɗi waye matashi. “Matashi shi ne wanda bai yi ƙasa da shekara goma sha biyar ba kuma bai wuce shekara ashirin da huɗu ba”. Idan muka dubi yanayi, cimaka da yankuna na duniya, za mu ga banbanci tsakanin masu waɗannan shekaru a zubi, yanayin girman jiki, wayewa, ilimi har ma da tunani.
Haka ma abin da ya shafi dokokin ƙasa zuwa wata ƙasar, za mu iya samun bambance banbance na masu waɗannan shekaru. Misali wasu ƙasashe daga shekara 18 shi ne matashi yake samun damar yin zaɓe ko izinin zaman kansa. A ƙasashe kamar Koriya ta Kudu, sai matashi ya kai shehara goma sha tara ko ma ashirin.
Tarayyar Afrika a nata ɓangaren, ta bayyana matashi shi ne wanda ya ke tsakanin shekara goma sha biyar zuwa talatin da biyar. Daga shekara goma sha biyar ɗabi’a, tunani da wasu halayyar mai wannan shekaru sukan canza.
Mai waɗannan shekaru yana taka wasu matakai masu mahimmanci a rayuwa, wanda ake buƙatar a kula sosai, sannan shi kansa matashi ya kula da su, ya yi ƙoƙarin yin amfani da su dan cin moriyar su nan gaba. Wasarairai da su da yin abin da ba shi ya dace ba a wannan lokacin ya na sanya mutum babbar nadama bayan shekarun sun wuce.
MATSAYIN MATASHI A WANNAN LOKACI A NAJERIYA
Najeriya ta na da tsare tsare masu kyau game da matasa amma a rubuce kawai. Kamar sauran ƙashashen duniya masu tasowa musamman na Afrika da Asiya. Gwamnatoci ba su fiye damuwa da abin da ya shafi matasa ba, ko dai saboda rashin sannanin mahimmancin su, gudumawarsu a gina al’umma da ci gaban ƙasa, ko kuma dan wani dalili na ƙashin kansu na siyasar su ta cikin gida.
Matashi a wannan ƙasa kusan shi ya ke tanadar wa kansa da kansa duk wani abu na gina rayuwarsa. Hukumomi ba sa ba da mahimmanci sosai dangane da abinda ya shafi wannan ɓangaren. Misali, abinda ya fi komai mahimmanci a rayuwar matashi babu kamar ilimi. Makarantun mu na sakandire kowa ya san hali da yanayin da suke ciki, babu wani kyakkyawan tsari da zai ƙarfafa gwiwar ɗalibi don zamowa wani abu nan gaba. Makarantun sakandire sun zama madakata ga da yawa daga cikin matasa musamman ‘ya’yan talakawa waɗanda ba sa iya karatu a makarantun kuɗi.
Matasa sun gama sakandire amma sun faɗi jarabawar gamawa, babu wani tanadi da hukumomi suke da shi na yadda za a yi da waɗannan matasan, daga nan sai su kiɗime, su rasa yadda za su ci gaba da rayuwa ga kuma buri. Wannan ya ke janyo wasu su fara shaye shaye don rage raɗaɗin zaman banza da yawon banza, wasu kuma su faɗa ayyukan ɓarna na yau da kullum. Kaɗan ne ake samu su nemar wa kansu sana’a don dogaro da kai.
A halin yanzu, ina makarantun mu na vocational da technical, suna nan, amma an yi watsi da su. A Arewa tun 1909 aka buɗe makarantar koyar da sana’a a Nasarawa inda ake koyar da saƙa, aikin kapenta da sauransu. A 1946 an sami bunƙasar wuraren koyar da sana’o’i inda aka buɗe wurare har goma sha huɗu a Arewa.
Na kawo wannan ne don kawai in nuna yadda makarantun koyar da sana’a suke da mahimmanci a da da yanzu. Za a iya amafani da waɗannan makarantu wurin saitawa da inganta rayuwar matasa a wannan ƙasa, don ba su damar komawa waɗannan makarantu in ba su sami damar yin nasara a jarabawar gama sakandire ba don su koyi san’a don dogaro da kai da kuma ɗauke musu kewar zama da yawon banza.
IRIN TANADE-TANADEN DA YA KAMATA A YI WA MATASHI:
Hukumomi a Najeriya suna da tanade-tanade masu yawa da inganci game da matasa a wannan ƙasa, amma ba a ba su mahimmanci wurin aiwatarwa, saboda wasu dalilai na shugabanni. Wani lokaci ana kallon aiwatar da waɗannan tanade-tanade da ba abin da za a iya ganin alfaninsu ne a yanzu yanzu ba. Su kuma ‘yan siayasa abin da suke so, shi ne sha yanzu magani yanzu, a gani a ƙasa don yaɗa manufofinsu da ɗorewar siyasar su.
Akwai tanade-tanaden da hukumomi suke da su na ilimantar da matasa, koya musu sana’o’i da abinda ya shafi wasanni. Abin da ya shafi ilimi da koyar da sana’o’i kullum hukumomi da ‘yan siyasa suna yin abinda za su iya, amma dai bai taka kara ya karya ba.
Abin da ya shafi wasanni shi ne har yanzu kamar an bar mu a baya musamman a nan Arewa.
A yanzu duk da addini da al’adar mu suna da tasiri mai yawa a rayuwar mu ta yau da kullum, amma dai a yanzu duniya ta ci gaban da ya kamata a ce mun tsunduma cikin abinda ya shafi wassani da motsa jiki wanda yanzu ya zama sana’a mai tagomashi a duniya. Banda ƙwallon ƙafa, akwai wasanni kamar ƙwallon kwando, ƙwallon hannu, ƙwallon raga, table tenis, badminton, guje guje, tsalle –tsalle, kokawa, iyo da sauran wasanni da ake gudanar da su ƙarƙashin kulawar hukumar wasanni ta duniya wato (Olympics).
A shekarun nan matasa ‘yan ƙalilan da sunayensu suka fito fili daga Arewa waɗanda suke buga ƙwallon ƙafa a duniya, an ga yadda suka samu ɗaukaka. Amma sauran ɓangarorin wasanni an yi buris da su, da ƙyar za ka sami ‘yan Arewa a sauran wasanni da na ambata a sama.
Idan hukumomi da ‘yan siyasa za su bai wa sauran ɓangarori na wasanni kulawa ta yadda za a samar da wuraren horar da matasa waɗannan wasanni, kamar yadda a Kano ɗaya daga cikin gwamnatocin da suka wuce aka gina makarantar horarwa kan wasanni. Faɗaɗa tunani wurin samar da ƙwararrun masu horar da wasanni iri–iri, a riƙa nemo matasa masu baiwar waɗannan wasanni ana ba su horo na musamman, sannan hukumomi su taimaka musu wurin shiga gasar wasanni na cikin gida da kuma na ƙasa da ƙasa.
Wannan wani tanadi ne mai kyau da zai rage wa matasa zaman banza, sannan za a samar musu da wani abin yi wanda ba lallai sai sun yi karatu mai zurfi ba, zai ba su dama su riƙe kansu da ‘yan uwansu ta hanyar abin da suke samu na kudade. Ƙari a kan haka shi ne, sauran matasa za su yi sha’awar waɗannan wasanni dan abinda suka ga ‘yanuwansu suka zama. Idan ba a manta ba akwai wata matashiya Tobi Amusan da ta lashe gasar tseren mita 100 a shekaran 2022.
Wannan abinda ya shafi wasanni an kawo shi ne a babin misali kawai, amma akwai damammaki da yawa da hukumomi suke wasarairai da su wanda zai ba wa matasa dama mai yawa a rayuwarsu don zama wani abu nan gaba ba tare da dogaro da gwamnati ba.
ABIN DA MATASHI YA KAMATA YA YI WA KANSA
A ƙashashen da suka ci gaba, hukumomi su suke yi wa matasa tanadi tun farko don a ɗora matashi a kan hanya, a ba shi ilimi mai kyau, a ba shi dama na koyon sana’a da sauransu. Amma a ƙasashen mu masu tasowa kamar yadda na faɗa, abin ba haka yake ba. Toh shin matashi don bai samu waɗannan tande-tanaden ba sai ya zauna ya kashe kansa da kansa yana ji yana gani? Shekarun samartaka wasu shekaru ne da yake bai wa wanda yake wannan mataki damammaki waɗanda ba su da iyaka.
Matashi yana da ƙarfin jiki, lokaci da ƙarancin tsoro, wanda ba a wannan shekarun yake ba yana da ƙarancin waɗannan abubuwa. A wannan shekarun matashi ji yake kamar ya ɗau duniya a ka saboda ƙarfin da yake ji jikinsa, ba wasu nauyi na yau da kullum a kansa da zai cinye masa lokaci, kamar hidimar iyali. Sannan matashi yana da ƙaracin tsoron yin duk abinda ya ke so, zai iya yin tafiye-tafiye masu nisan gaske, zai iya shiga ko yin duk wani abu mai haɗari ba tare da yin dogon tunani ba.
Waɗannan su suke bai wa matashi damar zama wani abu a rayuwarsa. Idan mutum ya girma ƙarfinsa ya fara ƙarewa wasu abubuwan ba zai iya yin su ba, lokacin sa kuma na aikinsa ne ko sana’arsa da kuma iyalansa, sannnan tsoron abinda zai iya kai wa ya komo. Misali tsoron mai zai faru ko wani hali iyalansa da ‘yanuwansa za su shiga idan ba ya nan duk waɗannan suna daƙile wanda ba matashi ba.
Ɗaya daga cikin manyan abubuwa da Najeriya ta ke da shi wanda ƙasashe da yawa babu, shi ne, duk ɗan Najeriya zai iya zama komai a ƙasar nan, abin nufi a nan, shi ne duk abin da kake so ka zama a Najeriya za ka iya zamowa, misali zama babban ɗan siyyasa, attajiri, babban jami’in gwamnati da sauransu.
Kullum muna gani waɗanda ba ‘ya’yan kowa ba, kuma su kansu ba kowa ba, suna zama manyan mutuane a ƙasar nan, ba za ka taɓa samun haka ba a wasu ƙashashe. A waɗannan ƙasashen idan ka taso a gidan takalawa, a haka za ka girma ka gama rayuwarka a wannan layin. Babu tsallake zuwa wani layin, wato abinda ake cewa “social mobility”.
Saboda haka, wannan dama ce mai kyau ga duk wani matashi da ya taso a Najeriya da ya yi ƙoƙarin samun ilimi ko da ba mai zurfi ba ne, ya sami sana’a ya riƙe, musamman idan a gidan su akwai sana’a, kada ya raina ta duk ƙanƙantar ta. Yanzu zamani ya canza za a iya zamanantar da duk wata sana’a, a tallata, kambama ta. Kada matashi ya kallafa wa kansa sai ya sami aikin gwamnati a yanzu, kada kuma ya yaudaru da abinda wasu suke samu ta hanya mara kyau a gwamnati.
Matashi ya rage wa kansa dogon buri. Duk arziƙin da Allah ya ƙaddara wa mutum sai ya same shi a duniya. Shi arziƙin ɗan Adam ana rubuta masa shi tun yana cikin mahaifiyarsa. Kamar yadda ya tabbata a hadisin Manzon Allah SAW da ga Abdullahi ibn Mas`ud, Bukhari da Muslim suka fitar da shi. Sannan babu wanda zai mutu har sai arzikinsa ya same shi, babu wanda ya isa ya tare masa shi.
Kawai a daure a nema ta hanyar halas, kada matashi ya yi gaggawar neman arzikinsa ta hanyar haramun. Manzon Allah SAW ya ke cewa, “Mala’ika Jibril ya faɗa min cewa babu wata rai da za ta mutu face ta sami arziƙin gaba ɗaya sannan kuma sai ta kai ajalinta. Ku ji tsaoron Allah ku kyautata nema. Kada ɗayan ku ya yi gaggawar neman arziƙinsa ta hauyar haram.
Kawai matasa ku tashi ku nema, Allah zai bayar. “Waɗanda suka yi gwagwarmaya za mu shiryar da su kan tafarkin mu, lallai Allah ya na tare da masu kyautatawa”
January 17th, 2025.
Danna nan don karanta Biyayya Ga Mahaifa
Edita:@rumasau-kallamu