Mataki Domin Kare Kanka Daga Kamuwa Da Ciwon Ƙoda

0
18

Mutane da dama basa bada aron hankalinsu ga irin gagarumin aikinda kodojinsu sukeji,kuma azahihirin gaskiya akalla mutum million 20 ke fama da ciwon koda a Nigeria (The Guardian by Chukwuma Muanya, 10th March 2022

Abubuwan Dake Janyo Ciwon Ƙoda 

Daga cikin abubuwan dake janyo ciwon ƙoda sun hada da ciwon sugar,hawan jini,ciwon zuciya,tarihin dangi akan ciwon ƙoda ko matsananciyar kiba. 

Matakai Domin Kare Kai Daga Kamuwa Da Ciwon Ƙoda. 
 • Zuwa Asibiti A Aunaka Akai-Akai 

Kamar yadda muke bawa ababen hawa muhimmanci,muke kaisu a doba lafiyarsu meyasa bama yiwa kanmu?

Anan akwai gwaji biyu da likitanka zai yimaka 

 • Awon fitsari domin ganin protein albumin 
 • Awon jini da ake kira glomerular filtration rate (GFR) domin gano kodojinka na aiki wajen cire ababe marasa amfani a jikinka (wastes) 
 • Kula Da Adadin Suga Cikin Jini 

Abubuwa da dama kan iya tasiri ajikin mutum,akan adadin suga dake cikin jini,wadanda sun hada da ababenda mutum bayada Iko akansu,kamar illness,hormones,stress. Idan adadin suga a cikin jini yawuce kima (higher blood sugar levels)  na janyo jiyojin jini su takure,su coshe, ta hakan kuma su illata kodar,Idan kasan kanada ciwon sugar,hanyar da tafi dacewa ka kare kanka daga kamuwa da ciwon koda ita ce kula da adadin suga cikin jini yadda yakamata. 

Karanta Abubuwan Daya Dace A Sani Akan Allurar Artemether

Daga  Cikin Hanyoyi Da Zakabi Sun Hada Da
 • Sauyi akan abincinka
 • Motsa jiki
 • Magunguna dake rage adadin suga cikin jini. 
 •  Kula Da Hawan Jini. 

Hawan jini na lalata ƙoda da kuma ƙara yuyuwar kamuwa da ciwon ƙoda,akwai magunguna da likitanka zai rubuta maka idan hawan jinin yayi sama sosai,bugu da kari akwai sauye-sauye game da yadda kake tafiyarda rayuwarka,wanda sun hada da rage/daina shan gishiri, daina shan giya,rage kiba da motsa jiki,duk kansu zasu taimaka wajen kula da hawan jinin.

 •  Cin Abinci Da Yake Dai-Dai Ga Lafiyarka

Yanada muhimmanci zaben abinci da yake dai-dai ga lafiyar zuciya da kuma sauran jiki baki daya,daga cikin illolin wadannan nau’ikan abinci sun hada da,fresh fruits,vegetables,whole grains,low fat or fat-free dairy products,kaci abincinda bayada illa ga lafiyarka,ka rage shan gishiri,kuma ka rage shan sugar. 

 •  Motsa Jiki 

Eh kwarai motsa jiki,motsa jiki na taimakawa wajen daidaita kiba da batada illa ga lafiya, sannan yana controlling blood pressure da cholesterol levels,motsa jiki na karfafa jiki da kara juriya,bugu da kari motsa jiki na rage yuyuwar kamuwa da cututtuka,kamarsu diabetes, ciwon zuciya,ciwon koda,daga cikin motsa jiki da zaka iya yi sun hada da tafiya kasa,gudu,hawan bene,tukin keke iyo cikin ruwa,da sauransu. 

 • Daina Shan Taba

Zuwa yanxu,kunsan irin Illolin shan taba,munyi video,kuma munyi rubutu akan taba sigari,shan taba sigari kan jawo cututtuka da dama dake illata kusan kowane sashe na jikin mutum,wadanda sun hada da koda,zaka iya daina shan taba kai kadai,ko kuma ka bukaci agaji wajen likita. 

 • Daina Amfani Da NSAIDs Fiye Da Ƙima 

Yin amfani da magunguna dake kashe zafi ko zogin ciwo ajiki da ake kira NSAIDs (non steroidal antiinflammatory drugs) na janyo ciwon koda,shan NSAIDs na lokaci mai tsawo musamman adadi mai yawa na rage wucewar jini cikin koda,wanda hakan na cutarda kodar. 

Domin karanta cikekken bayani akan Post Injection Inflammation: {Kumburi Bayan Anyi Allura} Danna nan 

labarin da ya wucePost Injection Inflammation: {Kumburi Bayan Anyi Allura}
Labarin na GabaAbubuwa Wanda Yakamata Mace Ta Kiyaye Lokacin Al’ada