Haƙuri da kau da kai game da kura-kuren kishiya; shi ne mafi girman abubuwan da suke wanzar da zaman lafiya a tsakanin kishiyoyi. Ga abin da Allah (Subahanahu Wata’ala) ya ce a game da muhimmancin haƙuri:
“Ka yi haƙuri a kan duk abin da ya same ka, haƙiƙa yin hakan na gaba cikin muhimman al’amura”.
Kyautata wa Junansu Zato:
Watsi da tseguma tare da nisanta munanan zace-zace marasa dalilai game da kishiya, shi ma yana daga cikin abubuwan da kishiyoyi ya kamata su yi, kuma dimantar kulawarmu da hakan, shi zai ba mu damar aiki da tarbiyyar da addininmu ya ɗora mu a kai ta kyautata wa junanmu zato. Allah (Subahanahu Wata’ala) ya ce:
Domin karanta Neman Aure Bisa Koyarwar Musulunci Danna nan
“Ina dai ma lokacin da kuka ji (mummunan zato da aka yi wa A’isha) uwar muminai maza da muminai mata sun yi wa junansu zaton alheri, kuma su ce wannan ai ƙage ne bayyanan ne”. (Suratun Nur,12).
Kuma an Karɓo hadisi daga Abu Huraira, Allah ya yarda da shi, ya ce: Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce: “Na hana ku mummunan zato, haƙiƙa, mummunan zato shi ne mafi ƙaryar zance”. (Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi).
Don karanta Ma’anar Aure danna koren rubutu
Sanin Haƙƙoƙinsu Da Kiyaye Su da Isar da Su a Junansu:
Kyautata wa kishiya da kuma mai da komai ba komai ba, dalili ne ƙwaƙƙwara da yake tabbatar da zaman lafiyar a tsakaninin kishiyoyi
Imamul Bukhari da Muslim sun rawaici hadisi da aka karɓo daga A’isha, Allah ya yarda da ita, ta ce: “Yayin da Saudat ƴar Zam’a (matar Annabi) ta manyanta ta ba wa A’isha ranar kwananta, sai Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya zama yana raba wa A’isha kwanan Sauda (ƙari a kan nata kwanan).
Wannan kyakkyawan misali ne da yake sanar da matanmu yadda ya kamata su zauna da kishiyoyinsu.
Domin Karanta Cikekken Littafin Danna nan