Muhimmancin Aure A Rayuwa

0
3177

Aure shi ne ƙashin bayan dauwamar jinsin halittar ɗan Adam, dabbobi da tsirrai a bayan ƙasa, aure sutura ce ta aminci, nutsuwa, ci gaba, buɗi da kwanciyar hankali.

Aure garkuwa ne mai kare mutuncin mutum da rufa masa asiri, kuma hanya ce ta samun sa’ada a duniya. A taƙaice muhimmanci, fa’idoji da hikimomin da suke cikin rayuwar aure za mu iya kallonsu ta ɓangarori biyar;Ahmiyyatuz zawaaj al-Fardiyyah war ruhiyyah, ahmiyyatuz zawaaj al-Ijtima’iyyah, ahmiyyatuz zawaaj assihhiyyah, ahmiyyatuz zawaaj al-Iqtisadiyyah, ahmiyyatuz zawaaj as-siyasiyyah.

Wato muhimmancin aure a kan ruhi, zamantakewa, lafiyar jiki, tattalin arziƙi da siyasar shugabanci.

Shaykh Salih Fauzan (Allah ya masa rahma) ya ce: “Aure yana da fa’idoji masu yawa; kiyaye mutum daga laifukan jinsi

  • Taƙaita musu kallon haram
  • Samun zuri’a da kiyaye nasaba
  • Samun nutsuwar ma’aurata da tabbatuwar amincin zuciya
  • Taimakekeniyar ma’aurata ga junansu
  • Gina nagartaccen iyali domin samun al’umma Musulmi tagari
  • Samun sakamakon ibadar tsayuwa da al’amuran gida da sauransu.
RUFEWA

Kiyaye ladubban zamantakewar aure, shi zai bai wa auren armashi da sakamako mafi inganci, wanda wannan sakamakon shi zai sanya al’umma ta zama a kan saiti da ci gaba, wanda akasin haka zai jefa al’umma cikin mummunar makoma. Allah Jalla wa Alaa ya kiyaye. Dr. Muhammad Sani Umar yana cewa: “Masu miyagun tunani sun ɗago kai, suna aiki dare da rana domin ganin cewa sun rushe ginin wannan al’umma wanda farkon tubalinsa an gina shi ne daga gida. Idan miji da mata suka sami haɗa kansu bisa turba ta Musulunci, to sai ka samu ‘ya’yansu sun taso cikin kyakkyawar tarbiyya, To amma da zarar aka samu kishiyar haka, wato miji da mata suka gina rayuwa ba a kan turba ba, to lamarin ‘ya’yansu ba zai yi kyau ba”.

Rabbana hab lana min azwaajina wa zurriyyatina qurrata a’ayunin waj’alna lil muttaqina imaama. Wa antal musta’aan wa alaikal balaagh wala haula wala quwwata illa billahil aliyyul azeem. Wa sallallahu wa sallam alaa nabiyyina Muhammad wa aalihi wa sahb ihi ajma’in.

Subhanakallahumma wa  bihamdika asshahadu an laa ilaha illa anta astaghfiruka wa atuubu ilaika.

karanta yadda za ki mayar da gidanki masarautarki  ko ladubban tarewa a gidan miji domin sauki cikakken littafin ladubban zamantakewar aure danna koren rubutu

labarin da ya wuceLadubban Tarewa A Gidan Miji
Labarin na GabaWannan Ita Ce Mace Tagari