Maganin Damuwa

0
306
MAGANIN DAMUWA
  1. Wani bincike da Hukamar Lafiya ta Duniya (WHO) ta gudanar a farkon wannan shekarar 2020 ya tabbatar da cewa kimanin mutane miliyan 264 a duniya suna fama da cutar damuwa. Kuma kusan mutane dubu 800 ne suke mutuwa ko su kashe kansu a kowace shekara saboda damuwa.
    Damuwa cuta ce ta ƙwaƙwalwa wacce take haifar da matsanancin baƙin ciki da ɓacin rai da fargaba da rashin jin daɗin rayuwa da amincewa kowa.
    Wanda ya kamu da wannan cuta sai ya rasa abin da zai yi ya ji dadin rayuwarsa , wannan ne yasa wasu suke kashe kansu, wai don su huta.
    Babban abinda yake haifar da damuwa shi ne  baƙin ciki kan abinda ya wuce da wanda ake ciki da kuma fargaba da tsoron abin da ake zaton zai faru nan gaba.Wato In mutum ya tara wa kansa ɓacin ran jiya ya haɗa da na yau ga kuma tunanin gobe ma haka za a tashi ,to dukkanin rukunan cutar damuwa sun tabbata ga mutum.
    A Musulunci, babu wata cuta da ba ta magani sai mutuwa. Kuma maganin Musulunci kan kowane irin ciwo shi ne kat, kuma kaifiyya.
    Musulunci zai ba ka riga-kafi, ya bayyana maka dalilan da suke jawo ciwo da maganin sa da kuma yadda za a yi amfani da shi a warke da iznin Allah.
    Ga waɗansu taƙaitattun bayanai da za su taimaka wajen magance damuwa da ɓacin rai Insha Allahu.
    DALILAN DAMUWA DA MAGANIN TA
    1.RASHIN GODIYAR ALLAH TA’ALA DA WADATAR ZUCI.
    Sau da yawa In mutum ya rasa wani abu da yake da shi ko kuma bai samu abin da yake so ba, sai ya mance da duk wata ni’ima da Allah ya yi masa,ya rinƙa jin shi rayuwarsa ba ta wani amfani. Wani ma abin da yake so ɗin ba ya cikin lalurar rayuwa, kuma babu rufin asirin da bai samu ba, amma duk da haka sai ya damu kansa da ƙunci saboda bai samu yadda ransa yake so ba.
    Maganin wannan shi ne, mutum ya gode wa Allah bisa ni’imomin da ya yi masa waɗanda ba za su ƙirgu ba, ya rinƙa duban na ƙasa da shi, kada ya rinƙa hangen na sama da shi.
    Wannan zai haifar wa mutum wadatar zuci da samun gamsuwa da yanayin da ake ciki.
    2.RASHIN YARDA DA HUKUNCIN ALLAH TA’ALA
    Allah Ta’ala shi ne mai iko a kan komai, shi ne mai yin yadda ya so a lokacin da ya so ga wanda ya so, ta yadda ya so.Rashin yarda da haka yakan jefa mutum cikin damuwa marar iyaka.
    Maganin wannan shi ne, cikakkiyar yarda da amincewa da dukkanin hukuncin da Allah ya ƙaddara a kanka ko ga waninka, koda kuwa ba haka kai kake so ba, saboda shi Allah Ta’ala ba a sa shi, ba a hana shi, ba a ce masa ga yadda zai yi,kuma ba a tashin hukuncinsa.
    3.KANGAREWA KA’IDODIN RAYUWA
    Allah Ta’ala ya tsara rayuwar duniya kan waɗansu dokoki da tsare-tsare waɗanda a kansu take tafiya.
    Duk wanda ya bi waɗannan dokoki zai zauna lafiya ya ji dadin rayuwarsa,wanda kuwa ya ƙi bin su, tabbas zai gamu da damuwa da tsaki a rayuwarsa.
    Misalin waɗannan ƙa’idoji:
    Allah ba ya kawo canji sai mutum/mutane sun canja salon rayuwarsu.
    _Duk abin da ka aikata sakamakonsa zai dawo maka.
    _Wanda ya dage, ya yi ƙoƙari shi ne zai samu nasara.
    _Zalunci sama da ƙasa shi ne yake ruguza al’umma.
    _Allah bai yi mutane iri ɗaya ba, kowa da halinsa da yanayinsa, sai kowa ya tsaya iya matsayinsa.
    _Kowane wuri akwai hanyar shigarsa.
    Rashin fahimtar waɗannan ƙa’idoji da aiki da su yana haifar da matsananciyar damuwa da ci baya a rayuwa.
    4.SAƁON ALLAH TA’ALA
    Saɓo ko zunubi shi ne karya dokokin Allah Ta’ala wanda ya haɗa da shiga haƙƙoƙin Allah da na bayinsa.
    Ƙin bin umarnin Allah da bauta masa kamar yadda ya yi umarni, da aikata abubuwan da ya hana ,da zaluntar mutane da tauye musu haƙƙoƙinsu, shi ne babban abin da yake haifar da ɓacin rai da damuwa. Saboda duk wanda ya hana wani barci tabbas shi ma ba zai yi barci ba, ko ya yi, sai dai da ido ɗaya.
    Sabo da bin Allah Ta’ala da bai wa kowa haƙƙinsa shi ne babban maganin damuwa.
    5.CIN HARAM DA ALMUBAZZARANCI
    Bin hanyoyin yaƙi halal yaki haram da son tara abin duniya ta kowane hali,da shirme da almubazzaranci da dukiya koda ta halal ce, shi ne musabbabin faɗawar mutane da dama cikin damuwa da baƙin ciki da ɓacin rai.
    Maganin wannan shi ne mutum ya zage damtse ya nemi halal kuma a yi amfani da abin da aka samu ta hanyar da ta dace, ba ƙauro ba barna.
    6.FIDDA RAI
    Fidda rai daga samun sauƙi da canji daga Allah Ta’ala babban zunubi ne, kuma yana jawo matsananciyar damuwa da bacin rai.
    Ya wajaba ga duk wanda yake cikin wani hali na damuwa ya cika zuciyarsa da kyakkyawan fata da zaton samun sauki da yayewar duk wani ƙunci da tashin hankali. Kuma mutum ya rabu da tsoro da fargabar abin da bai zo ba, saboda mai tsoron rashin lafiya, ya fi kamuwa da ita, haka mai tsoron talauci yakan zama abokin kut da kut ga talauci.
    7.CAMFI
    Camfi yana jefa mutane cikin damuwa.Misali camfa wata sana’a ko mace ko wurin zama wannan zunubi ne babba, kuma yana jawo damuwa da gurɓata rayuwa.
    In dai mutum yana son zaman lafiya da kwanciyar hankali to lallai ne ya dogara ga Allah Ta’ala ya yi fatali da camfe-camfe da shashanci.
    8.SHA’AWAR HARAM
    Sha’awar lalata ta maza ko mata tana jefa mai yin ta cikin damuwa, musamman idan bai samu damar cimma burinsa ba, In kuma ya samu, ba zai taɓa gamsuwa ba, saboda jini ba ya maganin ƙishirwa, haka dai za a yi ta rayuwa cikin damuwa da ɓacin rai.
    Maganin wannan shi ne jin tsoron Allah da kaucewa duk wani kallo da tunani da abota da ƙawance na haram.
    9.TSANANIN SON ABIN DUNIYA DA DOGON BURI
    Wannan ma yana haifar da damuwa da sanya a bi kowacce hanya, domin samun wannan ba kuma lallai ne a samu ba.
    Maganin wannan shi ne taƙaita buri da baya-baya da duniya.
    10.HASSADA
    Hassada ciwo ne babba, kuma zunubi ne mai girma wanda yake hana mai yin ta sakat a rayuwa.
    Maganin wannan shi ne a guji hassada a wanke zuciya.
    11.ZALUNCI
    Mutun ya yi zalunci ko a zalunce shi, yana haifar da damuwa.
    Maganin wannan adalci da haƙuri.
    12.TALAUCI
    Yana jawo babbar damuwa kamar yadda kowa ya sani.
    Magani shi ne haƙuri da dagewa wajen neman halal da wadatar zuci.
    Insha Allahu a rubutu na gaba za a kawo hanyoyin samun sauƙin musibu.
    Allah Ta’ala ya yaye mana dukkan damuwa duniya da lahira.
labarin da ya wuceNoma A Najeriya
Labarin na GabaMaganin Damuwa