Likita Ina Neman Taimako Haɗe Da Shawara Game Da Matsalar Ƙanƙantar Azzakari [Micro Penis]

0
101

Wannan na daga tarin tambayoyin gami da ƙorafin da a ko yaushe nake samu daga wasu cikin maza na sha kau da kai garesu, tare da ɗan tsaga bayani kaɗan cikin wasu rubuce-rubuce na, amma dai a yanzu abin ya yi yawan da dole na fito na yi bayani a iya kan wannan matsalar kurum. 

Haƙiƙa daga sanda mutum ya fara jin cewa an rage shi ta wannan ɓangaren to mataki ne da zai kai mutum ga rasa self confidence ɗinsa na namiji, yana kuma iya kai mutum ga damuwa da fargaba na ba gaira babu dalili wanda za su dabaibaye shi haka kurum. 

Sai dai kaso sama da 80% na masu irin wannan tunanin azzakarinsu ya kai tsaikon da ake so wanda ya dace da halittar su, zubin su da halaiyarsu dai-dai da na kowa kurum kallon kitse suke wa rogo! Amma a zahiri ƙalau suke.

Azzakari na fara girma ne jikin namiji daga shekara 11 sannan ya kammala girmansa zuwa 18yrs daga nan ya cika girman sa, don haka galibi daga shekara 20 shi kenan kurum abinda ka ganka da shi shi ne abunda Allah ya ba ka na tsayi ba za ka ƙara ba, domin kamar tsayi ne, daga shekara 21 shi ma ka gama tsayin da duk za ka yi. 

Kwata-kwata adadin masu fuskantar ƙanƙantar gaba a duniya wato Micro penis shi ne 0.015% cikin 100, wanda ke nuna kaso 99.85% duk azzakarinsu ya kai tsaiko sai de rashin godiyar Allah

Ina So Baki Ɗaya  Ku sani

A jima’i, binkicen masana game da azzakari an tabbatar da:

  • Mafi ƙanƙantar azzakari da in kana da shi shi ne za ka zargi kanka da matsalar ƙanƙantar gaba shi ne in ya gaza kai wa 3.6 inches kwatankwacin 9.16 centimeter sanda sha’awa ta kama mutum ya miƙe. 
  • Yayin da average wato tsayin da Allah a ƙallah kusan kowa inde ya kai toh babu zancen matsala shi ne: wanda yake (3.66 Inches wato 9.3centimeter) Idan an auna tsayin a sanda yake kwance wato flaccid kafin Erection, da kuma kai  wa tsawon 5.16 inches wato 13.12cm centimeters a sanda ya mike…. Wato Erection yayin sha’awa. 

Sharaɗin Kiyayewa 

Kafin gwajin ya kamata kowa ya sani yanayin wheather musamman lokacin sanyi ko yanayin zafi a inda yake da na’urar sanyaya ɗaki (AC) suna da tasiri wajen sanya shi ya kuɗe ciki don haka yanayin ɗumi shi ne zai sa a sami awo me kyau. 

Hakan tasa wasu kan ga gabansu ƙarami amma ba a nan abun yake ba domin galibi in ya miƙe su kansu suna ganinsa da girma musamman a masu masturbation saboda takurarku ce tasa fata ɓoye shi… don haka wannan normal ne babu buƙatar damuwa don ya kasance ƙarami amma in sha’awa ta taso kai achieving Erection ka gansa ya kai girman sa, ba ka da buƙatar ka dami kanka… 

Kamar yadda nace lokuta musamman na sanyi azzakari yakan ɓoye kansa ciki saboda canjin temperature.

Ba Ƙasa Da Ido Ake A Kalli Azzakari Ba

Idan kana so ka gane tsayin azzakarinka ba wai yadda kake ganinsa da ido ba ne, a a ka bari sai ka fito wanka ko kuwa yanayi me kyau sai ka sami irin ƙaton Mirror ɗin nan wato madubi sai ka tsaya ka ɗora hannuwanka a ƙugunka kai poster a sannan ne za ka gane zahirin tsayin azzakarinka sanda ya zamto kansa na pointing din ƙasa. 

A sannan ne in za ka auna sai ka sa ruler ɗinka ko tape ɗinka irin na awon teloli ka ɗora daga tushenta na gashin gabanka (BASE) zuwa ƙarshen penis glands ɗin wato wajen fitar fitsari (TIPS) sai ka ga numba nawa ka samu shi ne zai zamto tsayin azzakarinka 

Kuma an fi son gwajin ne sanda azzakari yake a miƙe wato aka sami Erection fiye da in yana kwance in ka ga ya miƙe ya yi ƙasa da 9.1centimeter (cm) Toh sannan ne za ka ce kana da ƙanƙantar azzakari wanda kuma galibi ɗan Nigeria ya wuce hakan. 

Idan Muka Duba Ƙididdigar Duniya Gaba Ɗaya

A kwai bayanai da shafin bayanai (WORLD DATA) suka fitar bisa survey da suka yi na jerin ƙasashen duniya tun daga ƙasar da mazajenta suka fi tsayin azzakari zuwa mafi ƙanƙanta, inda ƙasar ECUADOR  ita ce ƙasar da mazajenta suka fi ko ina tsayin jela da murabba’in AVERAGE tsayin da yakai 17.61 centimeters, sai ƙasar CAMEROON, BOLIVIA da SUDAN matsayin na 2, na 3 da na huɗu, yayin da ƙasar CAMBODIA ita ce average na tsayin jelar ‘yan ƙasarta 10.04centimeter, yayin da ƙasar Nigeria  ke matsayin ta 43 a duniya da mazajenta ke da AVERAGE na tsayin azzakari da ya kai 14.38cm centimeter. Wanda a hakan ma na san muna da mazaje masu yawa da azzakarinsu ya kai tsayin na wasu yan ƙasar Ecuador ɗin wato 17cm +

Sannan binkice ya nuna fiye da kaso 85% sun nuna gamsuwarsu da yadda duk azzakarin namiji yake matsayinsa na Average, in fact tsayin azzakari ba shi ne jima’i ba, iya sanin kalar mace da yadda za ka sarrafa ta ka tattabata Shi ne ke ba da gamsashhen jima’i, wasu magana a kunne yayin jima’i shi ke gamsar da su.

Don haka babu buƙatar ku je kuna kashe kanku, kuna sa kai a damuwa ba gaira babu dalili, ko ku yi ta shaye-shayen magungunan da ba za su amfane ku da komai ba.

Mu dai  likitoci ba mu da wani magani da sunan na ƙara tsayin azzakari, ko surgery shi ma babu, sai dai a yi wanda za a katsewa mutum majanyen da ke riƙe da azzakarin a can tushensa wato ligament domin ta zazzago shi ne ma wasu suke samun abu me ɗan nauyi su ɗaura a kanta suna tafiya yana lilo wai duk don ta zazzago…

Haka ko advance surgery sai dai ya zamo cosmetic kurum ka ga ina lafiya a ce azzakari sai an saka masa roba da sunan implant an tsai da shi kullum a haka duk da ba kowa ma ake wa hakan ba sai wanda rashin tsayin ya amsa rashin tsayi. 

Yana da kyau ku shiga nan domin karanta Dalilan Da Suke Sanya Mace Rashin Daukar Ciki

Fina Finan Batsa Da Maganganun Batsa Ba sa Komai Sai Lalata Tunani 

Kamar yadda na sha faɗa sau tari kalle-kallene na fina-finan batsa ke jawowa, wanda kuma na faɗa muku duk wannan ba azzakarin gaskiya ba ne, hatta abunda za ku ga ana fitarwa matsayin maniyyi wallahi ba maniyyi ba ne artificial cream ne aka haɗa shi… Wanda yake turo shi da syringe yake amfani, ɓoye kansa yake bayan camera man. A ƙalla ka sami mutum 12 a cikin ɗakin da ake shooting na porn, shi yasa komai za ka ga perfect…

Yau zan tabbatar muku da hakan a link ɗin da na sa muku ƙarshen wannan post ɗin, zai kai ku YouTube ku ga yadda suke haɗa pornographic scene ɗin.

Sai kuma lalacewar tarbiya da ƙarancin kunya domin mata a yanzu su ne kan gaba wajen ƴaɗa batsa a ko ina, za kai takaici ka ga irin abunda ‘ƴa’ƴan mu, ƙannen mu ke videos a kai suna ɗorawa a YouTube da sunan koya jima’i don neman kuɗi, ko kuma ka ga an ƙirƙiri group a Facebook da WhatsApp ana mata zalla amma ɓarnar da suke kare ma ba zai ci ba.

A haka duk sai su zo su yi ta tattauna hatta abinda ke faruwa a shimfiɗa saboda rashin mutunci na wasu matan, ka ji abubuwan ƙarya da gaskiya wasu su ji kuma su hau kai su zauna, daga ranar ta fara ganin gazawar mijin ta, ko ta kalli porn ta ɗauka duk gaskiya ne, mijin ta da ba shi da kaza ko ba ya iya minti kaza suna jima’i ba lafiyar sa ƙalau ba. 

Wani Abu Da Ba ku Sani Ba Shi ne 

Shi fa farjin mace baki ɗayansa FLEXIBLE ne, babu wata mace wai ita dunduɓus kurum sai dai in infection gare ta, amma Allah ya tsara shi ne ya sa masa transitional epithelium da duk yadda namiji yake zai dai-dai da shi in ya sanya gabansa, kamar roba ne, yana talewa, ya tsuke, ko ɗame,

Average na zurfin farji wanda galibi bai wuce wa shi ne 10centimeter fiye 90% na mata haka suke, kai me average 14cm Ka gayan ina za ka shigar da ragowar 4cm ɗin cikin 10cm?

Ni’imar Allah sakamakon can gaba bakin mahaifa ne shi yasa ko da ka kai 17cm ɗin ma kana iya jin ka shige baki ɗaya domin hakan zai kusata tips din penis dinka ga bakin mahaifa shi yasa in da rabon ciki kana yin release shi kenan maniyyinka zai nemi hanya ya shige cikin mahaifar cikin sauki.

Wannan bayanin zai zamto mabuɗin idanu ya zamto a dena ruɗarku da porn ko zantukan shirme, lafiya ƙalau kuke, ku mance da masu karanta muku wani ya ake kwanciya… duk su ma a finafinan batsa suke kawo muku wanda duk ƙarya ne galibi ba abunda kuke gani ba ne.

Allah ya taimake mu, ya shirya mana zuri’a baki ɗaya amin.

Domin karanta Me yasa Mata Ke Ganin Farin Ruwa Yana Fitowa  Kafin Ko Bayan Sanin Period Din Su? Danna nan

labarin da ya wuceMeyasa Mata Ke Ganin Farin Ruwa Yana Fitowa  Kafin Ko Bayan Sanin Period Din Su?
Labarin na GabaToshewar Magudanar Jini Da Shanyewar Ɓarin Jiki