Larurar Dannau [Sleep Paralysls] Da Yadda Za’a Magance

0
30

Dannau wani yanayi ne da mutane kan samu kansu ahalin bacci, yakan iya faruwa sau daya ga wasu a rayuwa, yayin da wasu kuma kan rika fuskantar yanayin akai-akai. Yanayi ne me kama.da mutuwa duk da yakan kasance mutum na acikin hayyacinsa farke saide sam yakan rasa ikon motsawa ko magana. 

Wani lokacin ma yakan zamo idon mutum abude zahiri duk da cikin bacci yake; abunda wasu kan kira da bacin zomo… toh saide hakan duk baisa mutanen dake kusa ko yake jin muryarsu fahimtar cewa yana cikin mawuyacin hali ko yana bukatar dauki an maquresa.

Shiyasa ga duk meson fahimtar me ake nufi da firgici toh dannau shine cikakken misalin firgici ko ince ihunka banza domin ko ihun kayi ba’a ji, ba’a san ma kanayi 

Alamomin Dannau

Mutane kan fuskanci ma bambantan alamu; Saidai duk yana daga alamun dannau 

Mutum yaji kamar annan-naɗesa cikin wani bargo me nauyi, ko kamar anɗaure hannuwa da kafafunsa a mike kamar gawa, wasu kuma suji kamar anshakesu sun kasa numfashi, wasu kamar wani abu ya kakare musu a mokogoro sun kasa shakar iska, wasu kanji sun kasa magana, wasu kuma su akaran kansu sunji suna maganar amma kuma babu wanda yake jinsu, sukan katsa motsa komi nasu, wasu kan rikajin tamkar mutuwa ce ta kusantosu

Meke Haddasa Hakan

Daya Daga Manyan Ababen Dake Haddasa Hakan Shine:

Karancin bacci,wato mutane masu fama da larurar rashin bacci, ko kuma wadanda suke kin kwanciya su samarwa da jikinsu isashshen bacci,haka nan samun canjin lokutan bacci kai tsaye watakila saboda yanayin aiki ko tafiya zuwa wata kasa da lokaci ya bambanta sosai 

Haka nan shan wasu magunguna dake aiki a ƙwaƙwalwa;kamar a mutane masu ciwon farfadiya,larurar halayya (personality disorders),ko kasancewa cikin tsananin halin matsi wato stress akoda yaushe,ko larurar hawan jini,ko larurar damuwa wato depression duk suna iya haddasa dannau. 

Idan kanason karanta Alamomin Cancer Danna nan 

Sai kuma halayyar kwanciya ta rigingine wato ta gadon baya  fuska na kallon sama.Sai mutane masu shan kwayoyi ko magunguna masu sanya maye.

Saide galibi mutane masu fuskantar karancin bacci sunfi fuskantar wannan matsala sama da sau 10 fiye da saura daga nan sai masu kwanciya ta gadon baya fuska asama.

Yaushe Dannau YafiI Faruwa

Yafi zuwa da safe,kode gabannin asuba, ko masu irin komawa baccin nan bayan sunyi sallah asuba karfe 6am na safe din nan.

Hakan na faruwa ne walau a farkon bacci wato yayin farkon baccin wato sanna mutum ya kwanta batare da jimawa ba,idan yakan ga abun tamkar na faruwa ne a tunani ba zahiri ba, saboda sanda bacci ya fara daukarka bakasani saide kaji ka shiga baccin kai tsaye amma inya zamto ka fara bacci amma kanajin tafiyarka zuwa cikin baccin counsiciously toh a lokacin zakaji ka kasa magana ko motsi yadda dannau ke zuwa kenan.

Sai kuma ƙarshen bacci wato gab da farkowa, domin sanda bacci yazo karshe duk da idanuwanka suna rufe kwayar idonka ke fara farkawa wanda hakan zaisa idanuwan su rika kadawa sosai yayin da duk sauran jikinka yake a sake wato relaxed, a daidai wannan lokacine mafarki kowanne iri kanzo. 

Toh Idan ya zamto idanuwan sun farka process din zaici gaba da gangarowa tsokokin wuyanka, kafafuwanka zuwa hannayenka, gadon baya sannan kafafunka sai kaji ka farko harda yin mika.

Domin karanta Abubuwa Da Ya Kamata Mace Ta Kiyaye Lokacin Al’ada Shiga nan

Toh amma idan bayan darkowar idanun jikinka ya cigaba da zamowa relaxed wato yai jinkirin farko saboda position din da kake ko kuwa bacci bai isa ba wata larura ce ta farko dakai hakan ke haddasa dannau kaji idonka biyu amma sauran jikinka yaki farkowa

Yadda Ake Magance Matsalar

Babu wani gwaji da likitoci keyi domin gano dannau, saide ga wanda abun ya tsananta akai akai takai ga har numfashinsa na daukewa akan binkici mutum ko yana dauke da wata damuwa abashi magani da zai kau da ita ko shawarwari, ko magance hawan jinin ya zamto under control ko yaushe.

  • Kyakyawan shirin kwanciya wato ya zamto kaya bamasu nauyi ba ajika, sannan ai alwala inda hali ga maza ko mata koda ana cikin haila, tare da addu’oi yayin kwanciya hakan nasa jiki samun nutsuwa da aminci koda cikin halin tsoro ake.
  • Kauracewa kwanciya ta rigingine,galibi wannan shine dalili ga mutanen dake kwance ta  gadon baya fuska na kallon sama. Don haka ku kwanta akowanne position amma.banda rigingine, zakuji kun dena da ikon Allah
  • Gyarawa tare da dorewa bisa tsarin bacci me kyau da zaisa kake samun baccin awa 6 zuwa 8 arana ko adare. kome kake in lokaci yayi rufe wayar nan ko kuma ka saita ta automatic take rufe kanta. 
  • Tabbatar da ingantacciyar tsaftar gurin kwanciya,akalla duk sati ake canza zanin gado da pillow case, ake sharewa tare da kakkabe gurin kwanciya kullum.
  • Baccin rana musamman tsakanin karfe 1:30 zuwa 2:30 na rana in ansami lokaci, kar baccin rana yake wuce awa 1 da rabi… tare da kauracewa kwanciya bayan karfe 3 na rana har zuwa magariba.baccin yamma ba abune mai kyau ba sam, saide larura.
  • Banda cin abinci mai nauyi ko motsa jiki kasa da awa 2 kafin lokacin kwanciya bacci.
  • Banda amfani da electronic items su waya da sauransu awa 1 kafin kwanciya bacci, wasu ma’auratan ma kan sawa kai dokar hana shiga dakin bacci da waya sam don asami lokacin juna.
  • Cikakken tsaftar baki, ake brush da kyau domin wasu bakinsu kan samar da miyau din bacci wanda in suka kwanta a rigingine miyau dinne ke toshe kafar numfashinsu wanda wannan abun tsorone shine mutuwa ka iya zuwa in abun bai saki mutum akan kari ba.Muddin Aka Kiyaye Wannan Za’a Ke Ƙwana Lafiya
Menene Abunyi Yayin Da Dannau Ke Afakuwa? 

Galibi yana zuwa cikin hayyaci ga mutane suna iya tunani tare da komi kurum motsi ko magana ke gagarar mutum don haka abunda ya kamata kayi yayin da kaji wannan daurin kazar kukun:

  • A ranka kai salati ka sanar da ubangiji shine matakin farko
  • Kai kokarin amfani da tsokokin idanunka wato ka jaraba runtse idonka tight ka rufesa ka rika budewa a hankali kaita maimaita haka.
  • Idan kana iya numfashi toh ka shaki iska deeply wato kai irin shakar iskarnan batare da ka tsaya fitar da ita ba har sai cikinka ya dago…. inkai haka kila saide kaji kamar anyaye ma labule ka farko.
  • Kana iya jaraba sanyawa ranka cewa gashinan kana kokarin motsa yatsun hannunka dana kafa,kaiIta jaraba amfani da yatsun farko kafin sauran sassan jiki hannu, kafafu da sauransu
  • Idan ya kasance acikin yanayin kana jin motsi ko muryar mutane ko kuwa wani ne ma daka sani kaji yana danneka a baccin toh ka canza wannan feelings din zuwa cewa wannan din fa da kakejin muryarsa kokari yake ya tasheka.
  • A duk irin yanayin da ka sami kanka na dannau kai kokarin jitunano wani abun mahimmi ka canza yanayin dashi har zuwa sanda zaka farko. Sannan ka zamo mai jaddada kalamar shahada ko Ayatul kursiyyu.
Zuwa Yanzo A Kimiyance

Babu wani sananne wanda ya mutu dalilin dannau koya hadu da wata illah, yanayi ne kurum dake bukatar hakuri da kwantar da hankali mafi tsayin lokacin da zakai ahaka bai wuce mintuna 3 saide tabbas kwai firgici, domin kana iya farkowa kaji kana zufa ko zuciyarka na bugawa farfar

Sannan babu wani alamu dake nuna aljani ne gaskiya,saboda mutanen da kan camfa haka ko zargi ga aljanu ko mayu da sauransu. Kamar yadda kukaji nace DISRUPTION ne na REM SLEEP saboda ai wasu dukkan adduo’i sunayi kafin kwanciya amma zakaga duk da haka suna fuskantar lamarin. Allah ya tsaremu

Domin karanta bayani akan Toshewar Magudanar Jini Da Shanyewar Ɓarin Jiki Danna nan

labarin da ya wuceToshewar Magudanar Jini Da Shanyewar Ɓarin Jiki
Labarin na GabaCututtuka Da Ake Dauka Ta Jima’i