Allah (Subhanahu wata’ala) yace:
( إِنَّ اللَّهَ لَا يَسْتَحْيِي أَن يَضْرِبَ مَثَلًا مَّا بَعُوضَةً فَمَا فَوْقَهَا ۚ فَأَمَّا الَّذِينَ آمَنُوا فَيَعْلَمُونَ أَنَّهُ الْحَقُّ مِن رَّبِّهِمْ ۖ وَأَمَّا الَّذِينَ كَفَرُوا فَيَقُولُونَ مَاذَا أَرَادَ اللَّهُ بِهَٰذَا مَثَلًا ۘ يُضِلُّ بِهِ كَثِيرًا وَيَهْدِي بِهِ كَثِيرًا ۚ وَمَا يُضِلُّ بِهِ إِلَّا الْفَاسِقِينَ )
البقرة (26) Al-Baqara
Lallai ne, Allah ba Ya jin kunyar Ya bayyana wani misãli, kowane iri ne, sauro da abin da yake bisa gare shi. To, amma waɗanda suka yi ĩmãni, sai su san cewa lallai shi ne gaskiya daga Ubangijin su, kuma amma waɗanda suka kãfirta, sai su ce: “Mẽne ne Allah Ya yi nufi da wannan ya zama misãli?” na ɓatar da wasu mãsu yawa da shi, kuma Yana shiryar da wasu mãsu yawa da shi, kuma bã Ya ɓatarwa da shi fãce fasiƙai.
A cikin Tafsirin Ibn Khathir As-Suddi ya karɓo daga Ibn Abbas, Ibn Mas’ud da wasu daga cikin Sahabbai cewar: Da Allah ya buga misalai guda 2 na munafukai” ( مَثَلُهُمْ كَمَثَلِ الَّذِي اسْتَوْقَدَ نَارًا ) البقرة (17) Al-Baqara
Misãlinsu shĩ ne kamar misãlin wanda ya hũra wuta, Da kuma: ( أَوْ كَصَيِّبٍ مِّنَ السَّمَاءِ ) البقرة (19) Al-Baqara
Ko kuwa kamar girgije mai zuba daga sama, Sai Munafukai suka ce: Allah ya fi ƙarfin ya buga misalai da waɗannan abubuwan Sai Allah (Subhanahu wata’ala) ya saukar da ita waccan ayar har zuwa: أُولَٰئِكَ هُمُ الْخَاسِرُونَ ) البقرة (27) Al-Baqara waɗannan sũ ne mãsu hasãra.
Sa’id yace: Ƙatada yace: “Allah ba ya jin kunyar faɗin gaskiya idan ya buga misali akan abu: babba ne ko ƙarami. Lokacin da Allah (Subhanahu wata’ala) ya buga misali da ƙwaro da gizo-gizo a littafin Sa, sai Munafukai suka ce: Me yasa Allah ya yi misali da waɗannan abubuwan. Sai Allaah ya saukar da:
( إِنَّ اللَّهَ لَا يَسْتَحْيِي أَن يَضْرِبَ مَثَلًا مَّا بَعُوضَةً فَمَا فَوْقَهَا ۚ البقرة (26) Al-Baqara
Lallai ne, Allah bã Ya jin kunyar Ya bayyana wani misãli, kõwane iri ne, sauro da abin da yake bisa gare shi.
Abu Jafar Ar-Razi ya karɓo daga Ar-Rabi bin Anas wanda ya yi sharhin wannan Ayar (2:26): “Wannan ne misalin da Allah ya bayar dangane da rayuwar wannan duniyar tamu”
“Sauro yana rayuwa ne indai har zai ci abinci amman yayin da cikinsa ya cika sai ya mutu. Wannan shi ne misalin wasu mutanen waɗanda Allah ya faɗa a cikin Qur’ani:
( فَلَمَّا نَسُوا مَا ذُكِّرُوا بِهِ فَتَحْنَا عَلَيْهِمْ أَبْوَابَ كُلِّ شَيْءٍ حَتَّىٰ إِذَا فَرِحُوا بِمَا أُوتُوا أَخَذْنَاهُم بَغْتَةً فَإِذَا هُم مُّبْلِسُونَ )
الأنعام (44) Al-An’aam
Sa’an nan kuma a lõkacin da suka manta da abin da aka tunãtar da su da shi, sai Muka bũɗe, a kansu, ƙõfõfin dukkan kõmai, har a lõkacin da suka yi farin ciki da abin da aka ba su, Muka kãmã su, kwatsam, sai gã su sun yi tsuru-tsuru.
A cikin waccan aya ta 26 (Da Allah ya yi misali da Sauro): فَمَا فَوْقَهَا ۚ (…da abin da yake bisa gare shi.) Wanda yana daga cikin halittun da ake ɗaukarsu da ƙasƙanci kuma mafi ƙanƙanta. Muslim ya rawaito Hadisin Aisha (Radiyallahu anha) tace: Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) yace: «مَا مِنْ مُسْلِمٍ يُشَاكُ شَوكَةً فَمَا فَوْقَهَا إِلَّا كُتِبَتْ لَهُ بِهَا دَرَجَةٌ، وَمُحِيَتْ عَنْهُ بِهَا خَطِيئَة»
“Babu musulmin da zai cutu silar taka ƙaya (فَمَا فَوْقَهَا) ko abinda ya fi ta girma, face Allah yasa an rubuta masa lada cikakke sannan a kankare masa zunubinsa” (Sahih Muslim)
Don haka Allah ya sanar da mu cewar babu wani abu ƙarami ko babba da ba za a iya misali da shi ba ko da kuwa ƙanƙantar sa ta kai Sauro ko gizo-gizo. Tun da har Allah (Subhanahu wata’ala) ya buga misali da sauro a cikin littafi Mai Tsarki, to tabbas sauro yana da abubuwan Al’ajabai. Ku gyara zama domin ilimantuwa da su.
Sauro ! Tun muna yara muke ji da ganin illar wannan ƙaramar halitta ga lafiyarmu. To amma ya kamata mu ƙara zurfafa tunani akan wannan halitta mai ban mamaki. Yayin da ɗan Adam yake da idanu guda 2 domin gani, shin ko ka san da cewar sauro yana da idanu sama da guda 100 masu suna mini eyes kuma kowanne guda 1 a cikinsa shi ma akwai sama da guda 100 da ake kira da lenses, kuma kowanne da irin aikinsa.
Dalilin hakan ne yasa ba za ka iya kashe shi farat ɗaya ba ko da kuwan ka biyo ta bayansa. Irin wannan dalilin ne yasa aka kwaikwayi idon sauron ta hanyar ƙirƙiro CCTV camera, drones, motoci masu tuƙa kansu da kansu da ake kira da “self driving cars”, da dai sauransu. Allahu Akbar !
Shin ko kun san da cewar macen sauro ce take cijo ba wai namijin ba ?
Shi aikin namijin shi ne: ya sadaukar da rayuwarsa ta hanyar jan hankalin mutum domin macen (wato matarsa) ta samu damar zuƙar jinin da za ta samar da isassun ƙwayayen da za ta ƙyanƙyashe ta yanda za a ƙara samun wasu ‘ya’yan sauron, kenan hakan yana nufin ta cikin jininmu suke samun ƙwayayensu, wanda a ƙalla macen sauro tana ƙyanƙyashe ƙwayaye guda 100 zuwa 200 a lokaci ɗaya, Allahu Akbar !
Allah mai yanda ya so !
Yayin da ya zamana Allah ya haliccemu da zuciya guda 1, shin ko kun san da cewar sauro yana da zuciya har guda 3 ?
Akwai left ventricle akwai right ventricle sannan kuma akwai central ventricle kuma cikin ikon Allah, kowacce da irin aikin da take yi a jikin sauron. Sauro ita ce halittar da ta fi kowacce halitta yawan kashe ɗan Adam ta hanyar saka masa cutar Malaria, Zika da kuma West Nile. A ƙalla da akwai ire-iren sauraye a duniya sama da 3,500 waɗanda suke satar jinin dabbobi kama daga micizai, kifaye da kuma mutane domin su samar da ƙwayayensu.
Sauro na iya ganin mutum a cikin mosquito net ba tare da wani shamaki na bango ba, a maimakon mu da muke amfani da haske domin gani, shi kuma sauro yana amfani da iskar Carbon dioxide ne wadda yakan iya shaƙar numfashinka daga nisan ƙafa 150, hakan ke ba su damar gano blood group ɗinka, wanda indai bai yi dai-dai da nasu ba, ba za su sha jinin ba, Allahu Akbar !
Allaah cikin iliminSa ya bawa Professor Jeffery Riffel (Malamin Biology a Jami’ar Washington ta Amurka) ikon gano dabi’un sauro dakuma yanda sauron yake tunani. Lokacinda ya bude qoqon kan sauron wanda ake kirada cuticle yaga qwaqwalwar sauron, kamar yanda ya zanatawa manema labarai. Sun gano hakanne bayan shafe shekaru samada 12 shi da abokan aikinsa (team)
Shin ko kun san sauro yana kaɗa fika-fikansa sau 1000 a cikin second 1 ?
Yayin da macen sauro take sokawa fatar mutum allurai 6 da suke a bakinta, a lokacin ne namijin sauro yake jan hankalin mutum don aikin macen ya kammala ba tare da mutum ya farga ba.
Duk da cewar ma kafin ka ji zafin cizon sai an ɗauki ‘yan sakwanni saboda allurar sedative da take tsirawa fata domin kashe zafin cizon, yayin da aikin ya kammala ita kuma ta riga ta bar fatar a lokacin ne zafin cizon zai fara tasiri akan fatar mutum, yayin da ka kai duka kuma tuni ta daɗe da tsotsar adadin jinin da take buƙata. Allahu Akbar !
Wannan duk ba abin mamaki ba ne domin kuwa idan muka koma cikin littafin Allah, Al-Qur’ani mai girma to za mu tabbatar da cewar ikon Allah ya wuce duk yanda ‘yar ƙaramar ƙwaƙwalwarmu take tunani. Tuni Allah ya faɗa a cikin Suratul Baqara aya ta 26. To a nan tunda ka ji misalin sauro ya fito a cikin Qurani kai ka san yana da abubuwan al’ajabi kam.
Wannan kaɗan daga cikin bayani ne akan halittar sauro, daya daga cikin ziliyoyin halittun Allah, duk Allah ya ba wa masu ilimin kimiyya wannan damar ne domin su gane ayoyinsa da suke sararin sama’uddunya da kuma kan duniyarmu ta Ard da muke rayuwa.
Domin karanta cikakken littafin danna nan
Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu