Kammalawa Daga Cikin Littafin Ka San Kanka

0
83

Warwara

Duk da na bayyana muhimmancin mutum ya gano kansa, zan iya cewa ba dole sai ka yi hakan ba. Gano kai wani aiki ne babba mai matuƙar wahala, da in ba ka yi sa’a ba zullumin da za ka shiga a ƙoƙarin gano kanka zai iya lahanta maka ma rayuwa, ya hana ka jin daɗinta.

Kamar yadda na fara ba da labari a farko, na daɗe ina son gane ni wane ne, kafin na gano kai na har ciwon damuwa sai da na yi, na ma fara karɓar magani a asibiti na ga abun ba mai ƙarewa ba ne na watsar, amma ban karaya ba, na ci gaba da tambayar kai na da kuma ƙoƙarin nemo amsoshin tambayoyin.

Ba zan ce iya ƙoƙarin gano kai na ne ya sa ni a damuwa ba, abubuwa ne da yawa suka haɗu, amma dole ko dai rashin sanin ni wane ne ya taimaka, ko kuma son gano ni wane ne ya ƙara ingiza abun. In kana ganin ba lallai ka iya jure wahalar da take cikin aikin gano kanka ba, ba kuma za ka iya rayuwa cikin haɗarin rashin sanin kanka ba, to ina ganin abu ɗaya za ka yi.

Ka bi wanda yafi ka sanin kanka sau da ƙafa. Duk abin da kake son sani ya turo an sanar da kai, duk abin da kake son aikatawa ya turo an koya maka. Na san za ka fahimci inda na dosa, ina nufin ka zama mutumin kirki mai biyayya wa Allah da manzonsa (tsira da aminci su tabbata gare shi) domin in dai ka tsaya kan hanyar da suka ɗauraka a kai, dole za ka amfanu kuma za ka amfanar, za a ƙaru da zuwanka duniya, kuma duk abubuwan da na lissafa a baya za su dinga zuwa maka a ɗabi’ance (naturally) ba tare da wani hoɓɓasa ba, kamar dai abin da ake cewa “autopilot”.

Idan ka yi wannan ka hutasar da kanka yawan tunani. Duk da cewa ita ma fa wannan hanyar ba sauƙi ne da ita ba, domin kana buƙatar ilimi da kuma aiki da ilimin, ilimi na gaske ba na wasa ba, aiki na gaske ba na wasa ba. Sai ka san ibada da mu’amala da haƙƙoƙin mutane a kanka da haƙƙoƙinka a kansu, da dabarun zaman lafiya da mutane, da yadda rayuwarka a cikinsu za ta amfane su kamar yadda ta magabata ta ke amfanarmu.

A iya ilimina (wanda ɗan kaɗan ne) ban san wani mutum da ya yi wata bajinta ba a duniya da bai zo wata gaɓa da ya san kansa ba. Kowa in za ka saurare shi, ko za ka karanta littafi ko rubutunsa ko tarihinsa za ka fahimci cewa daga cikin sa’ar da ya yi a rayuwa akwai gane shi wane ne da ya yi da wuri.

Don haka ko wanda ya zaɓi yin rayuwarsa kan tsari mai kyau zai zo gaɓar da zai san kansa, ko kuma ya dinga rayuwa kamar ta wanda ya riga da ya san kansa ko mai daren daɗewa. Akwai wani hadisi da sahabbai suke tambayar Annabin Allah mai tsira da aminci kan cewa tunda Allah ya riga da ya ƙaddara ƴan wuta da ƴan aljanna, ai ba buƙatar kowa ya yi komai, sai ya jira ƙaddararsa, sai ya ba su amsa da cewa “ku yi aiki, kowa za a sauƙaƙe masa abin da aka halicce shi don shi”.

Wannan yana nuna mana cewa ba a taɓa kafa hujja da ƙaddara, ko a zauna ana jiran rayuwa ta faru, manufar halittar shi ne ka rayu, ba ka zauna jiran rayuwar tana wucewa ba (waɗanda suka mutu a wurin kare addini Allah yace kar mu ɗauka a mace suke, a raye suke, wataƙila saboda sun mutu a kan manufa da bin tafarki, Allah ne mafi sani).

Don haka in ba za ka iya sanin kanka ba, to ka bi Allah ka huta, in za ka iya sanin kanka kuma ka samu riba biyu kenan, ka san kanka, kuma kana bin Allah a yadda kake don haka komai zai dinga zuwa maka a sauƙaƙe. Manufar rubuta wannan ɗan ƙaramin littafin shi ne karkato da hankalinmu kan yin rayuwa da manufa da tsari, ba kara zube ba.

In muna kara zube yanzu muka fara ganin cin kowanne irin kashi, ba za mu taɓa kwarjini ba, balle mu cimma wani abu, mu da ƙorafe-ƙorafe da ganin laifin juna mun ɗaura kenan har illa masha Allahu. In ka samu wannan littafin kada ka karanta shi ka ajiye shi, ka yi ƙoƙarin yin aiki da wasu abubuwan da ka ga za su iya dacewa da taka rayuwar.

Sani ba aiki ba ya canja komai, bambancinsa da rashin sani kaɗan ne. Allah na ke
roƙo ya ba mu dacewa duniya da lahira ya kuma azurta mu da kyakkyawan ƙarshe.
Kada a manta da yaɗa wannan saƙon dan amfanar ƴan’uwa gaba ɗaya, musamman matasa ƴan’uwana da ke ta faɗi tashin ganin sun gano kan rayuwa.

Wanan bayanin an ciro shi ne daga littafi mai taken Ka San Kanka wanda AHMAD SANI ya wallafa.

Danna nan don karanta Yadda Manufar Rayuwarka Take

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceYadda Manufar Rayuwarka Take
Labarin na GabaYadda Zubar Jini Yake Bayan Haihuwa
wikiHausa
wikiHausa kundin ilimi (insakulofidiya) ce da ke ilimantar da jama'a yara da manya da maza da mata wajen samun ilimi a saukake, cikin harshen Hausa.