Nankarwa (stretch marks) takan zamo mai tsananin ƙaiƙayi ko zafi ne, sa’annan kuma mai wahalar warkewar saboda haɗakar abubuwa guda biyu:
(a) Bubbuɗewa da kumburin fatar wurin da take
(b) Ƙoƙarin warkewar da fatar wurin take yi.
Yadda abin yake faruwa shi ne:
Nankarwa ta fi fitowa mace a jikinta, musamman a damtsen hannuwa, ko jikin nonuwa, ko cinyoyi, ko duwawu, ko, kwuiɓi, ko ciki, ko baya, ko sha-raɓa, da sauransu. Babban abinda yake kawo ta shi ne yin ƙiba, ko juna biyu, ko ramewa. Ma’ana, idan mace ta yi ƙiba, sa’annan ta rame daga baya, to, akwai yiwuwar nankarwa ta fito mata.
Haka nan, idan nonuwan mace suka yi girma sakamakon shayarwa, sa’annan, suka rage girma bayan ta daina shayarwa, to, akwai yiwuwar nankarwa ta fito mata. Haka nan yin ƙiba da yin rama a sauran sassan jiki.
Nankarwa ta fi fitowa mace a jikinta, musamman a damtsen hannuwa, ko jikin nonuwa, ko cinyoyi, ko duwawu, ko, kwuiɓi, ko ciki, ko baya, ko sha-raɓa, da sauransu. Babban abinda yake kawo ta shi ne yin ƙiba, ko juna biyu, ko ramewa. Ma’ana, idan mace ta yi ƙiba, sa’annan ta rame daga baya, to, akwai yiwuwar nankarwa ta fito mata.
Bubbuɗewar za ta haddasa yagewar zaren da yake haɗe tsakanin sassan fatar jiki (collagen) da kuma zaren da yake sanya fatar ta iya tattalewa (elasting). Daga nan sai waɗannan tabbai na nankarwa su fito ruɗu-ruɗu a jikin fata. Kuma tasirantuwar da fatar take yi (skin response) ne ga waɗannan abubuwan, yake haddasa kumburin da ƙaiƙayin ko jin zafi.
Warkewa (healing process) daga yagewar fata wacce nankarwa ta haifar, shi ma yana sanya jin ƙaiƙayi da kuma wahalar magancewa, musamman idan mace tana yawan sosawa. A nan, jijiyoyin jini za su riƙa bubbuɗewa (dilation) suka aikawa ƙwaƙwalwa sakon cewa zaren collagen da elastin na wurin sun yage, kuma akwai buƙatar su warke. To, a lokacin da ƙwaƙwalwa ta bayar da umurnin warkewar wurin, kuma sababbiin ƙwayoyin halittar cells (new skin cells) suke fitowa, wurin zai riƙa yin ƙaiƙayi.
Bushewar fatar nankarwa (dryness of stretch marks skin), sakamakon rashin shafa mayukan samar da damshi (moisturizers) a wurin, shi ma yana haifar da jin ƙaiƙayi sosai. Sa’annan yana sanya nankarwa ta yi ruɗu-ruɗu sosai, ta yi wahalar warkewa.
Rashin kaurin fatar nankarwa (thinning skin structure of the stretch marks) shi ma yana haddasa jin ƙaiƙayi da wahalar warkewa. Ma’ana, idan nankarwa ta fito, to, fatar wurin za ta zamo ba ta da kauri kamar yadda sauran fatar sassan jiki take, kuma hakan zai sanya jin ƙaiƙayi a wurin.
Bayan haka, rashin kaurin fatar zai sanya ta daɗe ba ta warke ba, musamman idan mace tana sosawa, ko kuma tana sanya matsattun tufafi suna yawan gugar wurin. Nau’in kumburin da nankarwa ta haddasa (nature of the stretch marks inflammation) shi ma yana haifar da jinkirin warkewa ko kuma ƙaiƙayin. Ma’ana, wata nankarwa tana fin wata yin ruɗu-ruɗu a jiki.
Don haka, gawargwadon tsananinta, gawargwadon yanayin ƙaiƙayinta da wahalar warkewar ta. Magungunan da ake yin amfani da su wajen magance nankarwa yawanci mayuka da sabulai ne masu samar da damshi a jikin fata. Sai kuma magungunan hana kumburi da ƙaiƙayin fata. Sa’annan yawanci magungunan suna rage tsananinta ne kawai, amma ba su gusar da ita gaba-ɗaya.
Don karanta yadda za a kula da fata danna nan
Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu