Hukunce-Hukunce, Ƙa’idoji Da Ladaban Zaɓe

0
28

Ko da yake a halin yanzu ba Shari’ar musulunci ake aiwatarwa ba a wannan ƙasa da kuma ƙasashen musulmi da dama na duniya, amma wannan ba zai sa musulmi su rungume hannuwansu su ƙi shiga harkokin gwamnati, da siyasa ba.

A matsayin larura sai a shiga a yi taka-tsantsan a rinƙa ƙoƙarin bin dokokin Shari’ar musulunci a duk inda musulmi ya tsinci kansa, ko a ƙasa ko tsakiya. Yana can sama. Wato ko yana da babban muƙami ko matsakaici ko na ƙasa haka kuma yana ɗan takara ne ko mai goyon baya.

Domin karanta Neman Aure Bisa Koyarwar Musulunci Danna nan

Malaman zamani sun yi saɓani akan hukuncin yin zaɓe da tsayawa takara a ƙarƙashin tsarin da ba na musulunci ba. 

Amma dai mafi yawancin malamai suna ganin halaccin yin hakan kasancewar musulmi ba mu da wani zaɓi na uku a halin yanzu. Akan haka ya kamata ga duk wani mai kishin addinin musulunci da musulmi mai ilimi da ƙwarewa da gogewa, mai ƙarfin zuciya da jarumta ya nemi zaɓe ta tsaftacciyar hanya ba tare da keta dokokin Allah da kuma tauye haƙƙoƙin mutane ba. 

Su kuma masu zaɓe su ji tsoron Allah su dubi cancanta kawai su zaɓi managarci mai Addini mai ilimi jarumi wanda ya damu da maslahar su wanda zai kare musu addininsu, dukiyoyinsu, rayukansu da mutuncinsu. 

Sannan jami’an zaɓe su ji tsoron Allah su guji maguɗi da murɗiya da sauya alƙaluma. Saboda son zuciya da ɗan wani abu da za a ba su. A yayin da ‘yan takara suke fafutukar neman a zaɓe su ya wajaba su kula da waɗannan dokoki da ladabai; 

Domin karanta bayani akan Jinya Da Likitancin Bahaushe Danna nan

  1. kada su yi wa masu zaɓe ƙarya wajen bayyana matsayinsu da cancantarsu a zaɓe kada su kasance masu tsanani ko da kawunan su da yabon kai, kada su ɗauki alƙawarin da su kansu sun san ba za su iya cikawa ba. 
  2. Su tsarkake niyyar su kasance suna neman wannan matsayi ne don kawai su taimaki musulunci da musulmi ba kuma tare da sun zalunci kowa ba, ko suna neman mulki ba ne domin su azurta kawunansu. 
  3. A guji al’mubazzaranci da watsi-watsi da dukiya ta hanyar shirme da fasiƙanci. A yi amfani da kuɗaɗen yaƙin neman zaɓe (campaign) wajen ayyukan alhairi wanda za su amfani mutane kai tsaye kamar sadaƙa ɗaukar nauyin karatun ‘ya’yan talakawa, tallafawa raunana da mabuƙata da sauransu. Banda sayen makamai da kayan maye banda kuma sayen ƙuri’a ko jami’an zaɓe da na tsaro ko wakilan wasu jam’iyyu mai cin amanar jam’iyyunsu. Saye ƙuri’u ko masu jefa ƙuri’a ko ba da toshiyar baki ga jami’an zaɓe da na tsaro haramun ne, yakamata ‘yan siyasa su kula. 
  4. A guji cin mutuncin juna da zage-zage da ƙazafi da yaɗa labaran ƙarya da sharri a lokacin yaƙin neman zaɓe.
  5. A guji gurɓata mahalli ta hanyar cire alamomin hanya da rufe allunan dokokin hanya da hotunan ‘yan takara da ɓata adon gari da irin waɗannan hotuna kamar liƙa su a jikin fitilu da shataletalen tituna da jikin garukan ma’aikatu da shaguna da gidaje. 
  6. Wajibi ne a guji maguɗin zaɓe ta kowanne irin salo da siga. 
  7. A guji rarraba kawunan mutane ta hanyar ƙabilanci ko bambancin addini ko yayata laifukan ‘yan hamayya da cin mutuncinsu ba ɓata musu suna. 
  8. Kada a ɗauki siyasa a matsayin wani abu na ko a muta ko a yi rai. 
  9. Bayan an yi zaɓe, an bayyana waɗanda suka yi nasara, ya wajaba waɗanda ba su yi nasara ba su yi haƙuri, su tara a gaba, su haɗa kai da waɗanda suka yi nasara domin kawo ci gaban ƙasa da al’umarta. 
  10. Kada a yi murnar hauka bayan sanar da nasarar zaɓe, ta yadda za a karairaye ko ma a mutu. Haka kuma wanda bai ci zaɓe ba shi ma kada ya ɗauki abin da zafi, ya yi haƙuri ya yi kyakkyawan fata ga wanda ya yii nasara, ya goya masa baya. 
  11. Haka su ma magoya baya su guji gaba da junansu akan wanda suke goyawa baya. Kada su rinƙa shaye-shaye da sare-sare da kashe-kashe. 

Domin Karanta Cikekken Littafin Danna nan 

labarin da ya wuceHukunci Da Abinda Allah Ya Saukar
Labarin na GabaHaƙƙoƙin Mabiya Akan Shugabanni