Hatsarin Shugabanci: Shugabanci komai ƙanƙantarsa wani nauyi ne babba a kan wanda ya hau kansa, wanda in ba a ɗauke shi an sauke shi daidai ba; in ba a yi gaskiya da adalci ba, in ba a riƙe amana ba; tabbas zai zama nadama da takaici ga wanda ya yi wannan shugabanci.
Da mun san hatsarin da yake cikin shugabanci koda an yi shi bisa gaskiya da riƙon amana; da babu wanda zai nemi a ba shi shugabanci; da sai an zo ana bin mutum ana haɗa shi da Allah don ya karɓi muƙami yana gudu yana a kai kasuwa. To amma rashin sanin hatsari da yake ciki; da kuma kallon da kwaɗayin ɗan roman da yake cikinsa, shi ne yasa ake ta yin kokawa; har ma ana kashe kuɗaɗe masu ciwo da ma roƙon Allah duk don a ɗare kan karagar mulki.
Ga wasu daga hadisan da shugaban halitta ya faɗa a kan hatsarin shugabanci:
Hadisi Na Ɗaya
An karɓo daga Abdullahi ɗan Umar (Radiyallahu Anhu) ya ce; “Na ji Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) yana cewa; “Kowane ɗaya daga cikinku makiyayi ne (shugaba ne) kuma za a tambaye shi a kan waɗanda aka ba shi kiwo; shugaba makiyayi ne kuma za a tambaye shi a kan waɗanda aka ba shi kiwo (mabiyansa), magidanci makiyayi ne a kan iyalansa kuma za a tambaye shi a kansu.
Matar aure mai kiwo ce a gidan mijinta kuma za a tambaye ta a kan waɗanda aka ba ta kiwo. Yaron gida/kanti makiyayi ne a cikin dukiyar uban gidansa; kuma; kowa za a tambaye shi a kan abin da aka ba shi kiwo. Dukkanninku makiyaya ne, kuma za a yi masa tambaya a kan abin da aka ba shi kiwo.
Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi.
Karin Bayani
Wannan hadisi ne mai girma da muhimmanci wanda ya ƙunshi abubuwa da dama kaɗan daga cikinsu su ne:
1. shugabanci kalma ce mai faɗi bai taƙaita a kan masu riƙe da madafan mulki ba, a’a duk wani wanda waɗansu suke ƙarƙashinsa komai rashin yawansu to shi ma shugaba ne, kamar yadda hadisin ya faɗa:
Mai mulki shugaba ne, mai gida shugaba ne a gidansa, matar aure shugaba ce a gidan mijinta, bara ko yaron gida ko angulun kanti, shugaba ne a kan dukiyar uban gidansa. Haka dai har shugaban aji da ɗalibai da na ƙungiyoyi da kwamitoci da sauransu.
2. Kowa za a yi masa hisabi ranar lahira; za a bincike shi kan yadda ya gudanar da shugabanci da aka ba shi.
3. Duk azabar da za a yi wa azzalumin shugaba; da kuma falala da rahamar da Allah yake yi wa adalin shugaba zai samu mai gida da uwargida, da yaron gida da sarki har zuwa shugaban ƙasa,babu bambanci, sai dai kuma kayan wani sun fi na wani yawa da nauyi.
4. A duk lokacin da ake maganar shugabanci yabo ko zargi alhairi ko sharri kafin ka yi tunanin shugaban ƙasa ko gwamna ko sarki ko wani na can sama; ka fara duba kanka ka yi wa kanka hisabi. Shi shugabancin da aka ba ka, kana kula da shi yadda ya kamata? Shin kana ba da haƙƙoƙin da suke kanka?.
Hadisi Na Biyu A Kan Hatsarin Shugabanci
An karɓo daga Anas ɗan Malik (Radiyallahu Anhu) ya ce: Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: “Haƙiƙa Allah zai tambayi kowane makiyayi a kan abin da aka ba shi kiwo, shin ya kiyaye shi ko ya tozarta shi? Har ma za a tambayi mutum a kan iyalansa”.
Ibn Hibban ne ya rawaito shi a cikin sahihinsa.
Karin Bayani
Lallai ne magidanta masu tozarta haƙƙoƙin iyalansu su bar ‘ya’yansu kamar marayu, matansu kamar kuyangi ba tarbiyya ba cikakkiyar lafiya har dabbobin da suke kiwatawa ma sai su fi iyalansu jin daɗinsu, su ji tsoron Allah su riƙe iyalansu da gaskiya su sani cewa amana ce Allah ya damƙa musu kuma za su yi bayani ranar ƙiyama kan wannan amanar.
Hadisi Na Uku A Kan Hatsarin Shugabanci
An karɓo daga Abu Hurairah (Radiyallahu Anhu) ya ce: Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: “Duk wanda ya zama alƙali haƙiƙa an yanka shi ba da wuƙa ba”.
Abu Dawud da Tirmizi ne suka rawaito shi.
Karin Bayani
Duk alƙalin da ya yi rashin gaskiya a kan aikinsa, haƙiƙa ya yi babbar asara ya halaka; ba wai rayuwarsa kawai ya rasa ba, har ma da addininsa wato wanda aka yanka da wuƙa zai fi shi samun sauƙin mutuwa da halaka. Wannan hadisi yana bayanin hatsarin da yake cikin alƙalanci; saboda haka ya zama wajibi ga alƙalai su yi taka tsantsan su rinƙa kwatanta gaskiya da adalci su guji zalunci, da cin hanci da murɗe gaskiya.
Hadisi Na Huɗu A Kan Hatsarin Shugabanci
An karɓo daga Auf ɗan Malik (Radiyallahu Anhu) haƙiƙa Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce; “In kuna so zan ba ku bayani a kan shugabanci ko yaya yake? Sai na ɗaga muryata na ce, “Yaya yake ya Ma’aikin Allah? Sai ya ce: “Farkonsa zargi ne, na biyunsa nadama ce, na ukunsa azaba a ranar ƙiyama sai dai wanda ya yi adalci”.
Bazzar da Ɗabarani ne suka rawaito shi.
Ƙarin Bayani
Wannan hadisi ne mai ɗimbin fa’ida da bayanin ɗabi’ar mulki duk daga taƙaitattun kalmominsa
- Mai mulki ba ya kuɓuta daga zargi da tuhuma da munana masa zato daga waɗanda yake mulka; da abokan hamayyarsa komai ƙoƙarinsa na kwatanta gaskiya. Haka zai ta shan suka da ƙalubale ta kowanne ɓangare, dukkanin idanu da kunnuwa suna kansa, komai ya faru shi ne ko bai sani ba, kuma ya fi ƙarfinsa.
– Yayin da abubuwa suka dagule, matsaloli suka kunno kai ta ko’ina, magoya baya suka fara juya baya ga shugaba, barazana da fargaba ta yawaita a gida da waje, shugaba yakan tsinci kansa a halin da- na-sani, da nadamar karɓar wannan shugabanci.
– Haka kuma bayan shugaba ya bar mulki musamman in an bi shi da jafa’i da bincike-binciken neman laifi da gazawa, wannan ma yana jefa masu mulki cikin kogin nadamar karɓar mulki.
– Mafi munin yanayi kuma shi ne, matsananciyar azaba da take jiran azzaluman shugabanni a lahira da tozarta da wulaƙanta tun daga duniya.
A taƙaice wannan hadisi yana ɗauke da tsoratarwa a kan shugabanci na zalunci da kwaɗaitarwa kan adalci saboda shi adalin shugaba babu ruwansa da wannan azabar.
Hadisi Na Biyar A Kan Hatsarin Shugabanci
An karɓo daga Abu Zarr (Radiyallahu Anhu) ya ce; “Na ce ya Ma’aikin Allah shin ba ka ba ni wani muƙami ba? Sai ya ɗora hannunsa a kan kafaɗata, sannan ya ce; “Ya kai Abu Zarrin haƙiƙa kai mutum ne mai rauni, shi kuma shugabanci amana ne, kuma yana jawo kunyata da nadama ranar ƙiyama; sai dai wanda ya kula da haƙƙoƙin shugabanci ya sauke nauyin da yake cikin shugabanci.
Hadisi Na Shida A Kan Hatsarin Shugabanci
An karɓo daga gare shi (Abu Zarr) Radiyallahu Anhu, haƙiƙa Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce da shi; “Ya kai Abu Zarr haƙiƙa na ga kai mutum ne mai rauni, kuma ina so gare ka abinda nake so ga kaina. Saboda haka, kada ka shugabanci koda mutum biyu, kuma kada ka karɓi riƙon dukiyar maraya.
Muslim da Abu Dawud da Hakim ne suka rawaito shi.
Ƙarin Bayani
Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) shugaba ne da yake lura da halin kowa kuma yake ba shi aikin da ya dace da shi.
Duk tsoron Allah na mutum da yawan ibadarsa bai kamata a ba shi shugabanci ba, in dai ba shi da ƙarfi da gogewa kan al’amuran mulki. Wannan ne ya sa Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ƙi ya ba wa Abu Zarr wani muƙami saboda ya san rauninsa da matsanancin sauƙin kansa da gudun duniya; har ma ya ba shi shawarar cewa ko da shugabancin mutum biyu aka ba shi kada ya karɓa.
Haka kuma kada ya karɓi ajiyar dukiyar marayu ba don yana tsoron zai cinye ba, a’a sai don gudun kada tausayi ya sa ya yi sadaka da wannan dukiyar.
Ɗan’uwa idan an faɗa wa Abu Zarr (Radiyallahu Anhu) duk da falalarsa; ina ga mutanen yanzu da za ka ga har kuɗi ake kashewa, ko a yi ta yin rigima a kan neman shugabanci, ba kuma tare da wata cikakkiyar cancanta ko manufa ko tsari ba.
Hadisi Na Bakwai A Kan Hatsarin Shugabanci
An karɓo daga Abu Hurairah (Radiyallahu Anhu) haƙiƙa Manzo Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce; “Haƙiƙa za ku rinƙa kwaɗayin shugabanci, kuma haƙiƙa zai zama sanadin nadama ranar alƙiyama. Madalla da mai shayarwa tir da mai yayewa”.
Bukhari da Nasa’i ne suka rawaito shi.
Ƙarin Bayani
Wannan abu da Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya faɗa na tsananin kwaɗayin shugabanci kamar a yanzu yake maganar. Sai ka ga ɗaruruwan mutane suna takarar kujera ɗaya; kuma a yanzu kowa so yake ya zama shugaba, sai ka ga komai da shugabansa; kuma har ana rigima a kan wannan shugabanci. Amma duka a ƙarshe nadama ce take biyo baya.
Mai shayarwa da mai yayewa shugabancin ake nufi, wato kamar yadda yaro yake jin daɗi lokacin da ake shayar da shi, kuma yake shan wahala da fama da laulayi iri-iri lokacin yaye shi to haka daɗin shugabanci yake a farkon da kuma wahala da damuwa da ake shiga in an sauka.
Hadisi Na Takwas A Kan Hatsarin Shugabanci
An karɓo daga Abu Hurairah (Radiyallahu Anhu) haƙiƙa Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce; “Kaicon sarakuna, kaicon wakilai, kaicon amintattu. Wallahi waɗansu mutane (waɗanda suka karɓi shugabanci) a ranar ƙiyama za su yi burin ina ma da a ce a ɗaure gashinsu a jikin tauraron surayya; su yi ta reto tsakanin sama da ƙasa a maimaikon shugabancin da suka riƙe.
Ibn Hibban da Hakim ne suka rawaito shi.
Hadisi Na Tara A Kan Hatsarin Shugabanci
An karɓo daga Abu Huraira (Radiyallahu Anhu) ya ce; “Na ji Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) yana cewa; “Zamani ya kusa zuwa da mutum zai yi burin gara a ce ina ma ya faɗo daga tauraron Surayya (zai fi masa sauƙi) a kan mulkin da ya yi komai ƙanƙantarsa”.
Hakim ne ya rawaito shi.
Ƙarin Bayani
Waɗannan hadisai guda biyu suna bayanin hatsarin shugabanci ta yadda mutum zai ji a ransa cewa gara a rataye shi da gashinsa a jikin tauraro ya yi ta reto; ko kuma a jefa shi daga can sama ya yi ƙasa ya ratattake a maimakon azabar da za a yi masa; saboda rashin adalci da gaskiya da ya gudanar a shugabancin.
Hadisi Na Goma A Kan Hatsarin Shugabanci
An karɓo daga Abdurrahman bin Samura (Radiyallahu Anhu) ya ce; Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce da shi; “Ya kai Abdurrahman ɗan Samura kada ka nemi shugabanci, saboda in ya zo maka ba tare da ka nema ba, Allah zai taimake ka a kansa; in kuwa aka ba ka shugabanci saboda nema da ka yi sai Allah ya bar ka da dabararka”.
Buhari da Muslim ne suka rawaito shi.
Ƙarin Bayani
Duk wanda ya san hatsarin shugabanci da makomarsa; ba zai iya nacewa ya yi ta kokawar sai ya sami muƙami ba. To irin wannan idan aka ga cancantar su aka tilasta musu lallai sai sun karɓi muƙamin za su sami tallafi da agaji daga Allah.
Wanda kuwa ya nace sai an ba shi muƙami musamman in bai cancanta ba ko kuma yana da wata muguwar manufa a ransa to ba zai yi wani abin kirki ba sai hauma-hauma da zalunci.
Domin karanta cikakken bayani a kan Hadisi Na Ɗaya A Kan Haramcin Goyon Bayan Azzaluman Shugabanni danna nan.
Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin; Shugabanci A Musulunci (Hadisai Tamanin Da Biyu A Kan Shugabanci); wanda Shehu Mansur Dala ya wallafa shi domin karanta cikakken Littafin danna nan.