Gaba: Rashin magana da juna bisa ga wani dalili wanda ya haɗa wasu mutane faɗa ko husuma ko jayayya da dai sauran su.
Saboda haka, gaba ba ta da wani amfani ga musulmi ko addinin musulunci, saboda addinin musulunci, addini ne wanda yake buƙatar mutanensa su dinga magana da juna, wasa da dariya haɗi da nishaɗantar da juna tare da kyautatawa juna, amma kuma ita gaba duk ta hana aikata haka.
Haka kuma Annabi Muhammad (Sallallahu alaihi wasallam) ya nuna mana irin sharrin da gaba take iya haifarwa ga al’umma, misali tana iya rushe zaman lafiya ga mutane, rashin samun gafarar Allah, rashin samun yarda ko amincewar Allah, rashin samun taimakon Allah da dai sauransu.
Sannan kuma ita gaba babu wani abu wanda take iya haifarwa , illar rashin jituwa atsakanin musulmi haɗi da daina ko rashin tatttaunawa da junansu, wanda shi kuma addinin musulunci baya buƙatar aikata haka, saboda shi musulunci addini ne na zaman lafiya
Bugu da ƙari kuma, gaba tana haifar da faɗa, rikici ko rigima atsakanin mutane haɗi da faɗin magan-ganu mara sa daɗi ko amfani ga addinin musulunci
Misali, idan wani mutumin wani gari yana gaba da wani mutumin wani garin, to wasu matsaloli za su iya faruwa atsakanin su, saboda shaiɗan yana murna da farin ciki, idan an samu wasu mutane suna gaba da juna.
Sannan kuma Allah (Subhanahu wata’ala) ba ya karɓan addu’ar mutanan da suke gaba da juna, ma’ana idan sun ɗaga hannunsu sun roƙi Allah (Subhanahu wata’ala), to Allah ba zai karɓi addur’ar su ba.
Haka kuma idan salihan bayin Allah sun yi addu’a ga mutane waɗanda suke da wata buƙata a wajen Allah, to ba za a sanya su a cikin addu’ar ba, har sai sun sasanta junan su haɗi da yafewa akan abin da ya wuce .
Misali mutum ɗan kasuwa ne ko wanda yake buƙatar Allah (Subhanahu wata’ala) ya kawo masa canji a cikin rayuwar sa, amma kuma yana gaba da wani mutum akan wani dalili, wanda ya haɗa su, to Allah ba zai karɓi addu’arsu ba, har sai ya daina yin gaba da wancan mutumin, saboda ita gaba tana hana addu’ar wucewa lafiya sumul ƙalau.
Musulmi ɗan uwan musulmi ne a duk inda yake a cikin faɗin duniyar nan, tatttaunawa, tausayawa, taimakawa, shawartawa da juna da dai sauransu, waɗannan su ne ake buƙata a tsakanin musulmai.
Saboda haka, ya kamata ‘yan uwana musulmai mu fahimci haɗarin da gaba take iya haifarwa haɗi da sharrin da ke cikinta. Sannan kuma gaba tana iya kawo rabuwar kai a tsakanin musulmai, saboda haka idan haka ya kasance a junansu, to maƙiya za su iya samun damar shiga tsakanin su, domin su raba kawunan su.
Misali kamar rukunin ko garken dabbobi ne, waɗanda suke fita kiwo tare da juna kullum, sai wata rana, wata dabbar daga cikin su, sai ta juyawa sauran baya, ta fita kiwo ita kaɗai, can sai ga zaki da kura nan sun tunkaro ta, sannan kuma ita kaɗai ce a cikin daji, shin akwai wata ƙofar gudu a gare ta?
Saboda haka, gaba kamar gini ne wanda ya rushe ko kuma jirgi ne wanda ya tashi sararin samaniya, sai kuma mai ya ƙare masa a sama, idan ya faɗo ƙasa, kun san abin da zai iya faruwa da jirgin.
Har ila yau, gaba tana iya haɗa ƙiyayya mai ɗorewa haɗi da wasiya akan aikata abu mara kyau da dai sauran su. Misali idan wani mutum yana gaba da wani mutum ko kuma akwai gaba a tsakanin su, to yakan iya sanarwa da ‘ya’yan sa waccan gaba take tsakanin su da wannan mutumin haɗi da jaddada musu matsayin sa akan wannan gaba.
Sannan kuma gaba takan iya haifar da sare-sare haɗi da kashe-kashe a cikin wasu guraran ko unguwannin da suke gaba da juna. Misali idan wani mutum faɗa ya haɗa su da wani mutum har sai da ya kai da sanadiyar sare-sare ga waɗancan mutanan, haka kuma wanda ya samu raunin mai yawa, to mutanen sa za su iya ɗaukar mataki akan aikata haka (fansa), kamar su rama abin da aka yi wa ɗan uwan su ko hana mutanen wancan layin shiga layin unguwar su.
Saboda aikata haka yana iya kawo rabuwar zukatan musulmai, rashin kulawa da juna, tausayawa juna haɗi da asarar jinane ko kuma rayuka ga waɗanda ba su ji ba su gani ba.
Sannan kuma Allah (Subhanahu wata’ala) yace “ku ji tsoran fitinar da za ta faɗawa mutane baki ɗaya”, ma’ana idan wani ko wasu mutane suka janyo rigima a cikin wani gari ko jiha ko kuma ƙasa baki ɗaya, to zai iya shafar kowane mutum, haka kuma su waɗancan mutanan da suka haifar da wannan rigimar, to laifin aikata haka yana kan su.
Misali idan wani mutum ya koyawa wani mutum karatul Alƙur’ani mai girma, sana’a ko kuma dukkanin wani aikin alheri, to Allah (Subhanahu wata’ala) zai ba shi lada mai yawa a duk lokacin da shi wancan mutumin ya aikata haka.
Kamar mutumin da ya koyawa wani mutumin aikata aikin sharri ne kamar su ƙarya, zina, sata, fushi, gulma da dai sauran su, to a duk lokacin da shi wannan mutumin ya aikata haka, to shi ma za a rubuta masa zunubi mai yawa akan hukuncin koyar da saɓawa Allah (Subhanahu wata’ala) da manzon Sa (Sallallahu alaihi wasallam) .
Saboda Annabi Muhammad (Sallallahu alaihi wasallam) yace “Duk wanda ya shiryar da mutane akan hanyar (aikata) alheri, to shi ma za a rubuta masa ladan kwatan-kwacin wanda ya aikata haka”. Misali idan wani ko kuma wasu mutane (ƙungiya) a cikin unguwa ko a gari suna ganin waɗansu mutane suna aikata abu mara kyau da amfani ga mutanen wannan unguwar ko garin, sai su yi yunƙurin hana su aikata haka, to Allah (Subhanahu wata’ala) zai ba su lada mai yawa saboda ƙoƙarin hana yaɗuwar ɓarna a doran ƙasa.
Saboda haka waɗanda suke yunkurin haddasa gaba a tsakanin mutane, to su sani fa kamar waɗanda suke umarni ne da aikata ɓarna ko sabon Allah (Subhanahu wata’ala) a doran ƙasa da dai sauransu.
Sannan kuma dukkanin wanda ya yi umarni da a saɓawa Allah (Subhanahu wata’ala) a doron ƙasa, to ya san hukuncin sa haɗi da makomar sa a ranar lahira, ma’ana gidan wutane gidan sa a ranar lahira, saboda umarnin da ya yi na bijirewa Allah (Subhanahu wata’ala), bayan kuma Allah ne ya halicce su, ya kuma raya su, sannan kuma ya ba su abin da zai yi musu amfani a rayuwar su.
Saboda haka, ya kamata dukkanin abin da mutum zai aikata ko kuma muke so a ran mu za mu aikata a cikin rayuwar mu ta yau da kullum, to yana da matuƙar kyau mu tsaya mu yi tunanin sosai kafin mu aikata haka, saboda mu samu damar wucewa kan gadar tsira ranar lahira lafiya sumul ƙalau.
Bugu da ƙari kuma, yana da mahimmanci akan musulmi ya san hukunce-hukuncen irin abubuwan da yake aikatawa a rayuwar sa ko kuma ya dinga tambayar malamai hukuncin aikata kaza da kaza da fatan Allah(Subhanahu wata’ala) zai daidaita zukatan mu, ameen summa ameen.
Domin karanta Hani Akan Yin Gori danna nan
Edita; RMK