Duba: Shi ne bincikar abin da zai iya faruwa da wani abu nan gaba. Duba ta hanyar taurari shi ake kira da “Astrology” (yana da bambanci da “Astronomy” da take nufin kimiyyar taurari), shi kuma duba ta hanyar zanen ƙasa (ramli) shi ake kira da “Geomancy”.
Waɗannan ilimai, kamar na bayansu, su ma suna da asali daga mutanen Hindu. Saboda asalin ilimin za a same shi a cikin manyan litittafinsu kamar Beda, inda aka samo “Bedic astrology”, da kuma abubuwan da aka ruwaito a litittafansu a yaren Sanskirt. Tun a zamanin Greek ana haɗe ilimin “Astronomy” da “Astrology” guri guda.
Ptolemy a cikin littafinsa da ya yi bayani akan ilimin falaki (Astronomy), a inda ya haɗa da bayanin “Astrology” da kuma yadda yake tafiya a fahimtarsa. Yana faɗar cewa, waɗansu abubuwan suna faruwa ne dai-dai da yanayin tafiyar taurari da kuma tafiyar rana da watanni. Don haka idan aka san yadda taurari suke, to za a iya gano yadda gaba za ta kasance. Ta haka zamu gane cewa ilimin taurari ya gangaro musulunci daga iliman Greeks ne.
Ibn Khaldun a cikin Muƙaddima, yana cewa akwai buƙatar a san cewa babu wani bincike na haƙiƙa da yake tabbatar da tafiyar taurari da kuma faruwar waɗansu lamura.Wato dai tafiyar falaki ba ta nuna wani abu “supernatural” kamar na tsafi ko bokanci ko kuma faruwar wani abu a nan gaba.
Sir Isaac Newton, kamar yadda aka ruwaito a cikin littafin “Cambridge Companion to Newton”, ya ba da labarin cewa ya tattauna da wani masanin ilimin taurari (Astrology) sai yake gaya masa haƙiƙar ilimin ba gaskiya ba ne amma hanyar cin abincinsu ce!
Masana halayyar ɗan Adam (psychologists) sun tabbatar da cewa abin da yasa mutane suke aminta da gaskiyar ilimin taurari shi ne yadda suke ganin abu yana faruwa, bayan an faɗa musu zai faru. A haƙiƙar lamari ba faruwa yake dai-dai da yadda aka gaya musu ba.
Ɗan Adam yana da saurin manta abubuwa ne, don haka idan mai ilimin taurari ya ce abu zai faru to mutum mantawa yake har sai wani lokaci can idan abu makamancin hakan ya faru, to sai ya yi zaton wanda aka taɓa gaya masa zai faru, shi ne ya faru ɗin.
Misali, idan nace mahaifinka zai mutu bayan na yi duba, to mantawa za kai da na taɓa gaya maka har sai bayan ya mutu ɗin, wataƙila da ƙarin shekaru masu yawa, kawai sai ka tuna maganar sai ka ce ai dama na taɓa duba maka hakan zai faru! Wannan shi ne abin da suka ce game da yadda abubuwa suke faruwa a ilimin “Astrology”.
Don Karanta Physiology da Hausa danna nan
Edita; Rumasa’u M. Kallamu