Haƙiƙa akan haifo wasu yaran cikin amniotic sac ba tare da ta yage iya yaran sun fito ba. Yana da kyau mu fahimta faruwar hakan ba wani matsala ba ne, a cikin cikin ita wannan sac ko in ce jakar haɗe take da jikin mahaifa ita ce ke samar wa da jariri iska sanda yake cikin mahaifa (placenta).
Amma a yayin da haihuwa ta zo ita sac ɗin kan yage ta yadda hakan ke ba wa huhun jariri (lungs) damar fara ɗaukar iska da kansa, maimakon sac ɗin da da take ba shi.
Hatta a asibiti wasu ba ta yagewa jami’an lafiya ne ke farka ta da hannunsu ba tare da kowa ma ya sani ba sai dai ku ga jaririn kurum.
Don haka haifo su cikin sac ba matsala ba ne. Allah yasa mu gama haife-haife lafiya.
Danna nan domin karanta yadda ake yi wa jarirai huɗubar haihuwa
Edita; Rumasa’u M. Kallamu