Hadisi Na Ɗaya A Kan Haramcin Goyon Bayan Azzaluman Shugabanni

0
844

An karɓo daga Abu Huraira (Radiyallahu Anhu) ya ce: Wanda ya yi zaman ƙauye zai yi jafa’i, wanda yake farauta zai gafala, wanda yake zuwa ƙofofin shugaba zai fitinu, mutuƙar bawa ya kusanci shugaba, zai ƙara nisa ga Allah”.
Ahmad da Abu Dawud da Nasa’i da Tirmizi ne suka rawaito shi.

ƘARIN BAYANI
Ɗabi’ar zaman ƙauye tana sanya mutum ya kasance mai wauta, saboda ƙarancin wayewa da ilmi, wannan bayanin ɗabi’a da halin da ake ciki.
Wanda yake shagala da farauta a daji zai kasance gafalalle saboda rashin samun lokacin neman ilmi da ibada, kullum yana dawa yana bin dabbobi.
Bin azzaluman shugabanni da goya musu baya da taimaka musu a kan zalunci da ɓarna, babban zunubi ne wanda zai zama fitina ga addini da duniyar mai wannan halin, kuma da wuya ka ga an rabu lafiya.
Kuma koda shugaba bai shahara da zalunci ba, haƙiƙa yin baya-baya da shi ya fi alhairi da kuma kare mutum daga fitinar son mulki da kwaɗayin abin duniya da raina ni’imar da Allah Ta’ala ya yi maka.
Amma mutumin da yake da kyakkyawar niyya da manufa da tsoron Allah da kamewa babu laifi a gare shi, idan yana kusantar shugabanni domin yi musu nasiha da haska musu ayyukan alhairi da ya kamata su yi, da faɗakar da su kan waɗansu matsaloli da ya dace a ce sun mayar da hankali a kansu .

Domin karanta cikakken bayani a kan Hadisi Na Biyu A kan Haramcin Goyon Bayan Azzaluman Shugabanni danna nan.

Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Shugabanci A Musulunci (Hadisai Tamanin Da Biyu A Kan Shugabanci) wanda Shehu Mansur Dala ya wallafa shi domin karanta cikakken Littafin danna nan.

labarin da ya wuceHadisi Na Goma Sha Biyu A Kan Falalar Adalci Da Tausaya Wa Mabiya Da Illolin Gallaza Musu
Labarin na GabaSallar Asham Da Raka’o’inta