Gyambon Ƙoda [Pyelonephritis]

0
26

Ganin kalmar pyelonephritis rubuce a conclusion ɗin mafi yawan scannings musamman na ultrasound abu ne kusan ba ɓaƙo ba,musamman ga mata,akan ga hakan akai-akai.

Toh saidai da yawa cikin masu turawa ai scanning ɗin musamman ƙananun jami’an lafiya in ankawo basusan irin yaren da ya dace suyiwa mara lafiya bayani dashi ba yadda zai gamsu,ya fahimci larurarsa.

Na sha samun inda da yawa kurum kancewa mutum gwajinsa ya nuna yana da ciwon ƙoda,wanda a ƙarshe hakan na matuƙar ɗugunzumawa tare da tashin hankalin mai larurar,musamman in yana da masaniya akan illar ciwon ƙoda, alhalin ciwon Sam ba irin wancan na ƙodar bane,laifin name bayanin ne.

Domin karanta bayani akan Idan Kaji Tamkar Wani Abu Ya Tsayamun A Maƙoshi [Lump Sensation In Throat ] Danna nan

Da yawa kan zo suce ance suna da ciwon ƙoda,amma kana bincikawa sai ka samu pyelonephritis ne ashe. 

Ya dace musani fayelonefiritis eh matsala a jikin ƙoda amma ba hausar data dace bane ka fassara sa da cewa me ita na dauke da ciwon ƙoda,wannan kuskure ne babba,domin ba kidney failure bane,shi gyambo ne kurum kamar yadda kake iya jin rauni a hannu ko wani sashi na jiki inka yanke ko ƙone.

Pyelonephritis matsala ce ta gyambo a jikin koda amma bata riga ta zama ciwon koda ba,domin sai matsala ta shafi nephron inda ake tace fitsari,jini da sauran muhimman jiki ya zamto duk sinadaran jiki sun birki ce sannan ne ya zama ciwon ƙoda.

Pyelonephritis Yaren Kimiyya Ne Dake Nufin:
  • PYELO= Mara
  • NEPHRO= Ƙoda
  • ITIS= Rauni ko gymabo

Don haka ahade yana nufin samun rauni ko gyambo a marar ƙodar mutum inda fitsari ke taruwa na ƙarshe kafin ya tsirgo ya biyo bututun mafitsara (ureters) zuwa mafitsara (bladder),wannan shine Ma’anar pyelonephritis. 

In kuka kalli hoton ƙasan wannan post ɗin,duk zaku gani a rubuce anyi nuni da sunayen kowanne sashi na jikin ƙoɗar, wajen wannan farin shine pelvis,nan ne mahaɗar fitsari kafin ya fara tsirgowa inya taru.

Kusan fitsari tafe yake da guba wato toxins da zauri saboda abubuwa ne da ƙoda ta tace marasa kyau da jiki baya buƙatarsu,ita kuma mafitsarar da yake fita wato kan azzakarin mu ko yaushe shine ke yin ƙasa in zamuyi fitsari,a wasu ma in halittar mai tsayi ce dab take kamar zata dunguri ƙasa,wani ma sai yasa hannu ya ɗan ɗaga ta,inko toilet din da ake zama ce dama dungurar jikin tukunyar kashin za take yi.

Toh haka ma a mata su mafitsararsu bata da tsayi irin na maza duk mun san haka,hakan ke nuna babu zurfi tsakanin cikin mafitsarar zuwa waje,kuma haka bai da nisa da duburarsu,wannan yasa wannan kusancin na mafitsararsu da gun tsuguno ba wuya sun kwashi ƙwayoyin cuta,ko kuwa wajen tsarki ai kuskuren taɓo dubura sannan adawo da hannu zuwa farji nan ma na jawo contamination na ƙwayoyin cuta.

To shi kuma namiji In yazo ya sadu da mace wannan ƙwayoyin cutar na iya bi su shiga ƙwaroron azzakarinsa zuwa mafitsara,haka duk kowa na iya dauka a bandaki mara tsafta ga marasa aure,to wannan ƙwayoyin cutar ne ke shiga ta ƙwaroron mafitsara suje mafitsarar suyi sama zuwa ƙoda,to anan ne suke taruwa insunje marar ƙoɗar sai suyita zagaye cikin fitsari wato supersaturation,har su haifar da rauni su fara zaizaye gurin.

Wani bun in suka taru har sukan doɗe,su toshe bututun mafitsarar inda kusan fitsari dama ko kamaka yai kaƙi zuwa kayi zata cin jikinka,don haka yau da gobe sai afara jin alamun matsalar kadan-kadan,dama galibi da zafin fitsari akan fara,walau farkon fara fitsari,ko in yaje tsakiya,ko a ƙarshen fitsarin. 

A Hankali Sai Afara Jin Sauran Alamomin:
  • Zazzaɓi-zazzaɓi saboda ƙwayoyin  cutar dake cikin fitsari
  • Ciwon kuiɓin ciki,daga ƙasan ƙashin haƙarƙari na ƙarshe ta baya
  • Rashin iya kwanciya batare da juye juye ba
  • Tashin zuciya,Jin zafin fitsari ya qaru
  • Fitsari ya riƙa fita kaɗan-kaɗan, da sauransu

Amma ba duk sai anji wannan ba amma dai galibi dama ciwon kuiɓin cikin kan sa mutane dole suzo asibiti saboda sun fara kasa jure ciwon,ko ansha maganin rage zogi saidai aji sauƙi na dan lokaci.

Matsalar wani lokacin kanyi wahalar sha’ani,saboda ƙwayoyin cutar dakan bijirewa magani,yana daga matsalar da nake jan hankali a kan mutane su dai na shan magani daka rukunin antibiotics irinsu ampiclox,augmentin,amoxicillin da sauransu domin masu irin wannan halayyar sunfi fuskantar wahalar warkewa saboda bijirewar ƙwayoyin lcutar ga magani.

Domin karanta Ciwon Yatsan Hannu Na Gaga Cikin Ciwukan Hannu Mafi Raɗaɗin Ciwo Danna nan

Amma dai ana bada magani akalla na kwana 7 zuwa sati biyu ko uku,ana warkewa tangaran.wannan matsalar bata cika kaiwa ga lalacewar ƙoda saide in halayyar ko in kula din mutum takai matuka wajen ko in kula da gidadanci.

Kamar yadda gyambo ko a hannu yake In babu kulawa yakan riƙa wari koma hannun ya lalace,to itama inbaka bada kulawa ba to shine zatai wahalar magancewa ko ya kai ga lalata ƙoda baki ɗaya ta kashe ta,amma ba abune da aka fiye gani ba,

Haka tana wahalar magani ga mutanen da daga fara shan magani sun soma jin sauki ke watsi da magani alhalin basu gama kwanakin da likita ya baka ba… Toh zata iya dawowa matsalar in kwayoyin cutar basu mutu ba. Don haka in ana fama da daya daga cikin alamomin to a nufi likita a binkita.

Domin karanta Me Ke Jawo Karancin Numfashi Ga Jarirai Bayan An Haifesu Danna nan 

labarin da ya wuceMe Ke Jawo Karancin Numfashi Ga Jarirai Bayan An Haifesu
Labarin na GabaNakan Ji Tamkar Wani Abu Ya Tsayamun A Maƙoshi [Lump Sensation In Throat ]