Gudunmawar Iyaye Wajen Gina Al’umma

0
36

Tarbiyyar Al’umma abu ne da ya zama wajibi a wanzar da shi domin shi ne abu na farko da idan aka same shi komai zai tafi daidai. Tarbiya da gyaran al’umma sun fara ne tun daga gida a wajen Mahaifiya don haka dole Uwa ta zama mai kyakkyawar ɗabi’a. Mata su ne ginin duk wani gida da kuma al’umma don haka dole a ba su fifiko saboda kusancinsu da ƙananan yara.

Iyayen mu da kakanninmu, idan za su kai ‘ya’yansu makaranta haɗawa suke yi da na maƙwabta haka zalika duk lokacin bikin sallah za ka ga ba su bambanta ‘ya’yansu da na maƙwabtansu. Suna tunanin cewa idan ya kasance tarbiyyar ɗa na da na makwabcina da tunanin su ya zama ɗaya akwai tabbaci mai ƙarfi na cewar zan zauna lafiya kuma babu wani abu na fargaba da zai faru ko da zai faru zai zo da sauƙi.

Hakan ya na nuna mana cewa a cikin Al’umma iyaye suke da babbar gudumawa wajen gina al’ummarsu, kuma hakan na nuna mana cewa yaro ba na mutun ɗaya ba ne. Ba ka jiran sai ka haihu kafin ka ba da tarbiyya. Sannan ba sai kana da ƙani ba domin idan ba ka haihu ba yan’ uwanka sun haihu idan ba ka da ƙani cikin ahalin ku akwai yara koma ba yara, kai kanka ba tsira ka yi ba idan ya kasance Al’ummar da kake rayuwa cikinta basu da Tarbiyya.
Anyi wani lokaci yara da yawa sun yi karatu kuma sun samu tarbiyya ba tare da saka hannun iyayen su ba domin kowa yana tsoron yaran sa su lalace.

Hakan yasa suka zaɓi haɗa kan yaran su dana ‘yan uwa da maƙwabta domin su kasance duk iri ɗaya. Da yawa za ka ji iyayen mu suna ba mu labari ai Baban su wane ne ya kai ni makaranta. Duk mai ya ja hakan? Ba komai ba ne sai neman zaman lafiya domin Bahaushe yana cewa “WAKE ƊAYA KE ƁATA GARI”. Wannan kuma duk na cikin dabara na iyaye da hangen nesa irin nasu bisa tarbiyar ‘ya’yansu da na maƙwabta shi yasa a lokacin da ake haka yara suke darajta iyayen wasu saboda sun ba su gudumawa tamkar iyayensu.

Muhimmancin Tarbiyya A wurin Ginin Al’umma.

Mai tarbiyya yakan taimakawa wajen samar da yara manyan gobe masu nagarta da kawo cigaban al’umma. Mai tarbiyya yakan samu karɓuwa a cikin ai’umma. Mai tarbiyya yakan zama da hikima, mutum yakan iya zama abin misali ga wani. Tarbiyya kan sa mutum ya yi magana cikin nutsuwa.

Mai tarbiyya yana iya shugabantar jama’a yadda ya dace. Mai tarbiyya yakan san daraja da kimar mutum. Mai tarbiyya yakan zama mai ibada. Mai tarbiyya yakan zama da haƙuri da juriya. Mai tarbiyya yana tsoron Allah.

Yana da kyau a ɓangaren matasa su zama masu baiwa iyaye gudunmawa da taimako wurin kulawa da na ƙasa da su. Sannan abinda ya fi komai muhimmanci shi ne mu guji aikata duk wani abu mai muni domin da su ne na ƙasa za su yi koyi, idan suka lalace ta yaya za su iya gyara wani.

Yana da kyau nuna wa yara muhimmancin zuwa makaranta da dagewa su yi karatu tare da fahimtar da su ga barin duk wani abu mara amfani ga rayuwarsu. Haka zalika yana da kyau mu rinƙa tsawatarwa wurin umarni da kyakkyawa da barin mummuna. Domin idan mutane suka zama nagartattu duk za mu tsira.

Idan Al’ummar da kake ciki tana da tarbiyya toh za ka rayu cikin kwanciyar hankali. Idan kuwa har kana fatan hakan, ya zama dole ka ba da gudunmawa wurin tabbatar da Tarbiyya cikin Al’umma. Tarbiyya aikin mu ne duka bai kamata mu naɗe hannu mu jira sai mun haihu ba, domin idan muka gyara kafin mu haihu mun ragewa kan mu aiki.

Danna nan don karanta Me Za Ka Yi Idan Ɗan Uwanka Zai Mutu?

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceHarara Garke (STRABISMUS)
Labarin na GabaRahamar Ubangiji Ga Bayinsa
Faruq Adamu
Sunana Faruq Adamu. Mu'assasin Gidauniyar Less-Privileged and Almajiri Initiative. Gidauniya Mai Rajin Taimakawa Mabukata, Dakuma Inganta Tare da Zamanantar da Tsarin Ilimi Na Almajirci a Nijeriya.