Fitsarin Jini (BLOOD IN UTRINE)

1
164

Fitsarin jini alama ce da ke nuni da cututtuka na mafitsara abu ne wanda mutum ya kamata ya damu sosai matuƙa

Menene Yake Kawo Fitsarin Jini?
  • Sanyin mafitsara
  • Sanyin Ƙoda
  • Duwatsun Ƙoda
  • Rauni a Ƙoda
  • Ciwon BPH
  • Kansar mafitsara ko Ƙoda
  • Cututtukan jini
  • Magunguna kamar magungunan kansa ko penicillin 
  • Tsargiya
Sanyin Mafitsara:

Sanyin mafitsara sanyi ne da ke shafar mafitsararka, idan kana da shi, toh za ka rinƙa yawan fita fitsari a kodayaushe musamman da daddare (sau biyu zuwa uku).

Domin sanin menene Ciwon Suga (Diabetes) Shiga nan

Alamominsa Sun Haɗa Da:
  • Yawan fitsari
  • Tashi da daddare yin fitsari (tashi cikin dare sama da sau biyu)
  • Jin zafi lokacin yin fitsari
  • Ganin jini a cikin fitsari
  • Ciwon gefen ciki bayan ciwon mara

Mutum na kamuwa da sanyin mafitsara a lokacin da aka samu kumburi ko ƙwayar cuta ta shiga cikin mafitsara, mata sun fi saurin kamuwa da wannan ciwo akan maza.

Haka zalika masu ciki da wanda al’adar su ta ɗauke suna da saurin yiwuwar kamuwa da wannan ciwo.

Sanyin Ƙoda:

Sanyi ne na ƙoda (infection) yana faruwa ne a lokacin da ƙwayar cutar bacteria ta shiga cikin ƙoda yakan zo da waɗannan alamomi bayan ciwon ciki daga gefe:

  • Ciwon baya
  • Rashin son cin abinci (anorexia),
  • Amai ko tashin zuciya
  • Zazzaɓi.
  • Yawan fitsari ko zafin fitsari 
Duwatsun Ƙoda:

Duwatsun ƙoda na daga cikin cututtukan da ke kawo fitsarin jini, waɗannan duwatsu dai waɗansu duwatsu ne da ke fitowa a ƙoda daga daskarewar datti da gishiri da ke cikin ƙodar.

Alamomin Sa Sun Ƙunshi:
  • Yawan fitsari
  • Azababban ciwon mara
  • Ciwo a gefen mara wanda yake zuwa har cinya
  • Rashin iya yin fitsari
Rauni A Ƙoda:

A lokacin da mutun ya yi rauni a ƙoda ta hanyar faɗuwa, buguwa, hatsari, yakan fuskanci wannan matsala ta fitsarin jini har sai wannan rauni ya warke. 

Ciwon BPH 

Wannan ciwo ne da mutum ke samunsa a lokacin da ‘prostrate ɗinsa’ (prostrate shi ke samar wa sperm cells sinadaran da suke buƙata wajen gudanar da aikinsu a jiki) ya kumbura, mutun kan iya kamuwa da shi a lokacin da ya haura shekaru 50.

Alamomin Sa Sun Ƙunshi:
  • Yawan fita fitsari da rana da dare
  • Jin azababban matsin fitsari
  • Rashin iya riƙe fitsari
  • Jin wahala idan aka zo yin fitsari
  • Fitowar fitsari da ƙyar
  • Jin raguwar fitsari a cikin mara

Kansar Mafitsara Ko Ƙoda

Kansar mafitsara ko ƙoda kan sa mutum ya yi ta fitsarin jini.

Alamomin Ta Sun Ƙunshi:

  • Zafin fitsari
  • Yawan fita fitsari
  • Kumburin mara ko gefen ciki
  • Rama
  • Rashin son cin abinci
  • Ƙonewar jini
  • Haki
  • Ciwon baya da sauransu.

Tsargiya.

Tsargiya na daga cikin abubuwan da ke kawo fitsarin jini, ana kamuwa da ita ne a lokacin da mutum yake yawan wanka a cikin kududdufi ko kogi. Bayan fitsarin jini takan zo da alamomi irin na sanyin mafitsara.

Yana da kyau ku karanta wannan Yan Mata Masu Shirin Yin Aure Da Amare Da Kuma Masu Sabon Ciki Kar ku ga Kamar Na Takura Muku Da Maganar Folic Acid

Maganin Fitsarin Jini

Abu mafi muhimmanci shi ne a je asibiti domin samun kulawa ta musamman daga ƙwararru, magani ya danganta da abubuwan da ke kawo fitsarin jinin binciken da za a yi maka a asibiti don gano asalin me ke saka fitsarin jini.

  •  Gwajin fitsari
  • Hoton mafitsara da ƙoda
  • Gwajin jini 

A mafi lokuta abubuwan da ke kawo fitsarin jini suna buƙatar a kwantar a asibiti domin yin cikakken magani.

Fitsarin jini ba abu ba ne wanda za ka yi wasa da shi ko ka tsaya karɓe karɓen magungunan gargajiya, abin da ya fi dacewa shi ne a je asibiti a ga likita.

Domin karanta bayani akan Cutar Mafitsara (UTI) Danna nan

labarin da ya wuceCutar Mafitsara (UTI)
Labarin na GabaFamily Planning Injection (Noristerat) (Norist)

SHARHI ƊAYA