Barkanmu da kasancewa a fannin girke-girkenmu na WikiHausa, za mu koyi yadda ake faten wake da doya. Tare da ni Hafsat Shettima.
Abubuwan haɗawa:
- Wake (½ kofi)
- Doya peeled and washed (gwargwadon buƙata)
- Attaruhu Jajjagaggen 5 (ko gwargwadon buƙata)
- Jajjagaggen Tattasai 2
- Jajjagaggen Albasa 2
- Kifi busasshe
- Cray fish niƙaƙƙe
- Manja
- Ogu leave Yankakken
- Maggi
- Curry
- Jajjagaggen Tafarnuwa
Yadda ake haɗawa
- Da farko za a dafa wake ya nuna sai a ajiye a gefe.
- A cikin wata tukunya mai zurfi, a saka manjan, sannan a yanka albasa ya ɗan fara soyuwa, sai ki zuba kayan miyanki, maggi, curry da tafarnuwa idan ya soyu, sai ki zuba ruwa ya ɗan tafasa.
- Sai ki zuba doya da ogu da kifi sannan a rufe ya yi kamar minti 10-15 ko kuma idan doyar ta yi laushi, sai ki zuba wake a juya. A yi a hankali wurin juyawa kar waken ya farfashe.
- A bar shi na minti 4-5 sannan a sauke.
- A ci da fanke ko a haka.
Domin koyan Yadda ake farfesun kayan ciki a sauƙaƙe danna wannan koren rubutun