Fassarar Huɗubar Juma’a Rubutacciya daga Masallaci mai Alfarma 14th March 2025

0
54

Aminu Bashir

Mai Huɗuba: Sheikh Dr Abdurrahman bin Abdul-Aziz Assudais

Mai Fassara: Malam Salisu Alhaji Abdullahi

Transcribe: Aminu Bashir

Shugaban Sashi: Dr Abdurrahman Muhammad Sani Yakubu

Huɗuba Ta Farko:

Dukkan yabo ya tabbata ga Allah, muna gode Masa tsarki ya tabbata gare Shi, muna neman taimakonSa da gafararSa, Ya keɓance mu da lokaci na ayyukan ɗa’a, madalla da tafki irinsa, duk wanda ya yi gaggawa zuwa gare shi zai kai ga samun ƙololuwar yardar Allah.

Godiya ta tabbata gare Ka godiya dawwamammiya a bisa ni’imomin da ba su da adadi bare su kare. Kuma muna roƙon Sa datarwa da godiyarSa lallai ita godiya ta kasance mai bayyana ni’imomin abin bauta ce. Kuma ina shaidawa lallai babu abin bauta bisa cancanta sai Allah, Shi kaɗai Yake ba Shi da abokin tarayya, shaidar da za mu samu mazauni a gidan Aljanna ta dalilinta.

Kuma ina shaidawa lallai Annabinmu kuma abin koyinmu Muhammad bawan Allah ne kuma ManzonSa, mafi alherin wanda ya yi azumi da sallar dare, sai ya kasance ɗaya tilo wurin falala. Ya Allah ya Ubangijinmu Ka yi daɗin tsira ga Annabi Muhammad, a matsayinsa na shayabo kuma abin yabo, da Alayensa tsarkaka nagartattu, waɗanda suka kai ga samun daraja da jagoranci a watan taƙawa, da Sahabbansa masu daraja waɗanda suka ƙarar da watan Ramadana suna masu ruku’u da sujjada, da Tabi’ai da waɗanda suka bi su da kyautatawa suna masu fatan samun kyakykyawar ƙarshe, da aminci mai yawa, muddin mutum zai wayi gari ko ya yini cikin kyautatawa.

Bayan haka;

Ya ku bayin Allah!

Ku ji tsoron Allah Ubangijinku, domin tsoron shi ne ƙashin bayan azumi da manufarsa, kuma shi ne haƙiƙaninsa da ma’anarsa, Allah Ya ce: ((Ya ku waɗanda kuka yi imani an wajabta muku azumi kamar yadda aka wajabta wa waɗanda suka gabace ku don ku samu taƙawa)).

Ya kai ɗan Adam ka yi sauri wurin neman taƙawa, kuma ka yi gaggawa zuwa ga aikata alheri matuƙar an saurara maka. Me yafi taƙawa kyawu! kuma me yafi hanyarta zama shiriya!, da ita ne mutum yake samun ɗaukaka da aikinsa.

Ya ku taron Muminai!

A yayin da al’ummar Musulmi suke ni’imtuwa da dawwamammen ƙamshin watansu mai albarka, da kwanakinsa masu yalwa da asali, kuma suke shiga ƙarƙarshin inuwarsar alkhairansa mai faɗi, wanda aka ƙawata shi da mafi kyawun mayafi, kuma suke kwankwaɗar ruwansa garɗi, suke shan ruwansa mai ƙosarwa, suke haskaka da haskensa, kuma suke more kwanakinsa masu banƙaye, kwatsam sai ga shi watan ya raba, watan alheri da kyauta da kyautatawa, watan da ƙoramunsa suka gudana da ayyukan ɗa’a, furannin alheri da ayyukan nagarta suke hudowa daga cikinsa, kuma Musulmi suke sauraron manufofinsa da sirrorinsa cikin shauƙi, kuma suke yi shiru suna masu sauraron manufofinsa tabbatattu da labaransa cikin nutsuwa, kwanakinsa kuma suna kwararowa da ayyukan neman kusanci ga Allah da farin ciki, dararensa suna haskaka da ayoyin da ake karantarwa da haske, wani lokaci ne da Allah Mai rahama Ya sanya albarka a cikinsa, kuma Alƙur’ani ya wanzar da shi ((Watan Ramadana wanda aka saukar da Alƙur’ani a cikinsa, shiriya ne ga mutane kuma ayoyi ne bayyanannu na shiriya, kuma mai rarrabewa)).

Ya ku taron Musulmi!

Haƙiƙa Allah Maɗaukakin Sarki Ya shar’anta azumi don Musulmi ya sabunta kyawawan ɗabi’unsa na bauta, kuma ya sake motsa yunƙurinshi na ayyukan alheri, sai ya samu ɗaukaka a cikin darajojin imani, ya kuma siffantu da siffofin ma’abota nagarta da kyautatawa, ta yadda Shari’a mai hikima ba ta tsaya game da azumi a kan abin da yake fili ba, bari dai, ta ƙetare haka zuwa ɗaukakar ruhi da ɗaukakan rai da kiyaye shi da tsakake gaɓɓai, da ɗaukaka shi daga lamari na zahiri zuwa sasannin matsayi da ɗaukaka na imani, don haka ne ma Allah Maɗaukakin Sarki Ya keɓance wannan bauta ban da sauran ibadu, kamar yadda ya zo a Sahihaini cewa: (Dukkan ayyukan ɗan Adam nasa ne, ban da azumi, domin shi Nawa ne, kuma Ni ne Zan ba da sakamakonsa).

(Watan Ramadana) wani wata ne da Allah Ya ba shi matsayi, don Allah Ya ji tausayin wanda hanyoyi suka ƙuntata gare shi. (Allah) Shi ne Mai tausayin mu, shin akwai wani ma’abocin buƙata da ya kira Allah Mai rahama da zuciya mai cike da kunya sannan ya taɓe.

Ya ku al’ummar Muminai!

Waɗannan kwanaki masu albarka dama ce mai kyau da za a amfana da ita wajen bibiyan rai da gyara aiki, da yin watsi da saɓani da rarrabuwar kai, da alƙalantar da hankali da harshen tattaunawa, da taimakekeniya a kan ayyukan nagarta da taƙawa, saboda abin da wannan wata mai karamci yake ɗauke da shi na darusa masu girma na rigegeniya wajen yin alherai da kyawawan ayyuka, Allah Maɗaukakin Sarki Ya ce: ((Ku yi gaggawar aikata alheri)).

Imami Ibnul-Ƙayyim Allah Ya masa rahama ya ce: “Shiriyar Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ita ce mafi cikar shiriya a cikin watan Ramadan, kuma mafi girma wajen tabbatar da manufa, sannan mafi sauƙi ga rayuka, kuma daga cikin shiriyarsa tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi a cikin watan Ramadana akwai: Yawaita nau’uka mabanbanta na ibadu, kuma Jibrilu amincin Allah ya tabbata a gare shi ya kasance yana taya shi muraja’ar Alƙur’ani, kuma ya kasance yana Yawaita sadaka da kyautatawa a cikinsa, da karatun Alƙur’ani, da Salla, da zikiri, da i’itikafi, kuma ya kasance yana keɓance shi da wasu ibadu da ba ya keɓance wani watan na daban da su”.

Ya ku bayin Allah! Ku gaggauta tattara ƙoƙarinku, ku tafke ɗaurin ɗamararku, ku bayyana wa Allah alheri daga gare ku, ku farkar da zukatanku daga angajen munanan tunani, kuma ku kame idanuwanku daga kallon ababen da aka hana ku kallo, Mai rabo shi ne wanda ya ƙawatu da adon ayyukan ɗa’a, kuma ya gyastu daga hasken jama’a.

Ya ku taron masu azumi, masu salla, kuma masu kyauta! ((Haƙiƙa kuna da kyakkyawan abin koyi daga Manzon Allah)). Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance ya fi kowa yawaita kyauta a cikin mutane, kuma yafi yawaita kyauta a watan Ramadana (Ya kasance ya fi yawaita kyauta sama da sakakkiyar iska). Bukhari da Muslim ne suka rawaito.

Don haka ku yawaita kyauta da baiwa a wata mai daraja, lallai ku yi kyauta ya ku masu karamci da daraja, daga cikin abin da Allah Ya kwararo muku na arziki, ku shimfiɗa hannayenku da kyauta da baiwa, don ku gusar da damuwowin waɗanda ake bi ba shi da hakan, da talaucin mabuƙata, da rashin ma’abota baƙin ciki, da fitar da garƙamammu da suke jiran taimakonku kuma suke hangen agajinku da kyautatawarku daga gidajen yari ((kuma duk abin da kuka ciyar (don Allah), to Shi ne zai ba ku madadinsa, Shi ne kuwa Fiyayyen masu arzutawa)).

Ya zo a Sahihaini daga Hadisin Abu Huraira Allah Ya ƙara masa yarda, lallai Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: (Babu wani yini da bayi za su wayi gari a cikinsa face Mala’iku biyu sun sauko a cikinsa, sai ɗayansu ya ce: Ya Allah Ka maye wa duk wanda ya ciyar gurbin abin da ya ciyar, ɗayan kuma sai ya ce: Ya Allah Ka lalata dukiyar duk wanda ya ƙi ciyarwa). Su kuma mutane ɗayan biyu ne, wanda aka datar da shi kuma aka jiƙanshi, da kuma marowaci da aka haramta wa rahamar Allah, don haka ku saki hannayenku da alheri don amfanar da wani.

Sannan ayyukanku na alheri ya zama ƙarƙashin amintacciyar inuwa, da cibiyoyi nagartattu, kuma Cibiyar Sarki Salman na ayyukan agaji da taimakon mutane, da Dandalin Ihsan na ayyukan agaji misalai ne masu kyau a kan matsayan wannan ƙasa mai albarka, da kwaɗaituwar shugabanninta wajen ƙarfafa ayyukan agaji da taimakon mutane, a nan za a jinjina wa gidauniyar ƙasa ta ayyukan agaji ta hanyar Dandalin Ihsan, da ƙarfafawa mai girma da yake samu daga shugabanni Allah Ya kiyaye su, wanda hakan yake nuna ƙoƙarin wannan ƙasa mai albarka tun daga lokacin kafa ta wajen taimakon ayyukan agaji da ƙarfafa su, wanda hakan zai wajabta taimakawa da ƙarfafawa wajen isar da saƙonsu na Addini, da karantarwa, da zamantakewa, da agaji, da kiwon lafiya, da ayyukan agaji da taimakon mutane a mataki na duniya a bisa tsarin cigaba na zamani.

Kamar yadda kuma hakan zai taimaka wajen dakile ɗabi’ar barace-barace wacce mabaraci da wanda ake roƙa suke cutuwa da ita, domin ita ɗabi’a ce mummuna, wacce cutarwata take bayyane, mai yaɗa laifuka, kuma tana hana aiki da ƙoƙarin neman na kai, kamar yadda kuma ta saɓa wa tsare-tsare da aka gindaya, da gamammun ladubba, da tsarin cigaba, kuma tana zaburarwa a kan kasala da zaman banza, sannan kuma tana ɓata kyawawan ɗabi’u a cikin al’ummomi.

Madalla da ibada da aikin neman kusanci na fitar zakka da ta wajaba da bayar da sadaka, a cikin waɗannan kwanuka masu albarka. Allah Ya ce: (Ka karɓi wata sadaka daga dukiyarsu, kana mai tsarkake su da ita).

Madalla da yawaita baiwa da ciyarwa da kula da waƙafi da wasiyyoyi da kiyaye tsarin gudanar da waƙafi cikin ayyukan alheri, don ta bambanta da wanzuwa da ƙayataccen tsari, da fayyacewa da amana, da lura da abin zai tabbatar da gamammiyyar maslaha, kamar gina asibitoci da cibiyoyin maganin ciwon ƙoda, da samar da hanyoyi, da gina sabbin gidaje, da haƙan rijiyoyi, da shayar da ruwa, da yaɗa ilimi mai amfani, kamar Tauhidi, da taimakon tsangayoyin Alƙur’ani, da sadaukar da Alƙur’anai, da Litattafan Sunna da hukunce-hukunce, da sadakoki masu gudana bayan rai, na daga dukkan abin da zai haifar da gamammen amfani, da fagage na bunƙasawa, kuma masu hannu da shuni da manyan ‘yan kasuwa su kasance su ne ababen koyi cikin haka, kuma bayyana sadaka da fito da ita fili zai iya kasancewa shi ne ya fi falala a wasu lokuta, domin koyi da kwaikwayo, abin da zai girmama lada ya wanzar da tasiri, Allah Ya ce: (Duk abin da kuka bayar na alheri, to, za a cikashe muku ladansa kuma ku ba za a zalunce ku ba).

Saboda haka, ya ku bayin Allah!

Ku ɗaura ɗamarar aiki, matuƙar kuna da ragowar kwanaki, kuna masu ribatar abin da ya yi saura na ayyukan alheri cikin wannan watan, musamman kwanaki goman ƙarshe, don samun mafi girman lada, Allah Maɗaukakin Sarki Yana cewa: (Allah Yana nufin sauƙaƙa wa gare ku, kuma ba Ya nufin tsananta muku, kuma don ku cika ƙirge kuma ku girmama Allah saboda abin da Ya shiryar da ku a kai, kuma don ku gode Masa).

Allah Ya albarkace mu da Alƙur’ani da Sunna, Ya amfanar da mu kuma Ya ɗaukaka darajarmu da abin da ke cikinsu na ayoyi bayyannu da hikima, ina faɗin wannan magana tawa, kuma ina neman gafarar Allah Mai girma da ɗaukaka gare mu da sauran Musulmi daga dukkan wani laifi da zunubi, saboda haka, ku nemi gafararSa kuma ku tuba zuwa gare Shi, lallai Ubangijina tabbas Mai yawan gafara ne Mai jinƙai.

Danna nan don karanta Azumi

Huɗuba Ta Biyu:

Dukkan yabo ya tabbata ga Allah, muna gaggawa da sauri wajen neman kusanci gare Shi da azumi, ina shaidawa lallai babu abin bauta bisa cancanta sai Allah, Shi kaɗai ba Shi da abokin tarayya, muna fatan Ya tunkuɗe mana sharri daga gare mu.

Kuma ina shaidawa lallai Annabinmu Muhammadu bawan Allah ne kuma ManzonSa, mafi girman mutumin da ya amfanar da talikai, Allah Ya masa daɗin salati da albarka, da Alayensa da Sahabbansa, mafi alherin waɗanda azumi ya gyara halayensu da ɗabi’unsu, da Tabi’ai da waɗanda suka bi bayansu da kyautatawa, muddin Ramadana zai kwaranyo da hawaye daga idanuwan masu tuba, kuma Ya masa ƙarin sallama mai yawa.

Bayan haka:

Ku kiyaye dokokin Allah ya ku bayin Allah, ku yawaita kyawawan ayyuka da fatan karɓuwarsu a watan rahama da gafara da kyatatawa, kuma ku bi bayansu da godiyar Ma’abocin ni’ima da ba ta yankewa, saboda da yardarsa za ku rabauta, kuma izuwa ga ni’imominsa za ku tafi.

Ya ku taron Muminai!

Watan Ramadana wata ne na ƙoƙari da himma da aiki, watan samun nasarori da tabbatar da su, domin a cikin watan Ramadana ta shekara ta biyu bayan Hijira ne Musulmi suka ci nasarar a yaƙinsu na farko mafi girma, wato yaƙin Badar, sannan sai nasarorin Musulmi suka cigaba da samuwa a gabashin duniya da yammacinta, kuma dayawa daga cikin waɗannnan nasarorin sun kasance ne a wannan wata mai albarka, don haka ya ku bayin Allah ku jefar da kasala da rauni da nawa daga gare ku, ku yi riƙo da sabuban samun rabauta da nasara, na tawakkali da ƙoƙari da himma, kuma ku fuskanci goman ƙarshe da himma mai ƙarfi matsananciya, don koyi da Annabinku mai daraja.

An rawaito daga Uwar Muminai A’isha Allah Ya ƙara mata yarda, ta ce: “Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana ƙoƙari a kwanaki goma na ƙarshe irin ƙoƙarin da ba ya yi a waninsu”. Bukhari da Muslim ne suka rawaito.

Kuma ya zo a Hadisi ingantacce: “Cewa lallai Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance idan goman ƙarshe ya shigo sai ya ɗaure ɗamararsa, kuma ya raya darensa, kuma ya farkar da iyalansa”. Don haka kuma ku ɗaure ɗamara kuma ku raya dararensa, idanuwanku su zubar da hawayen nadama. Saboda Ubangijina Mai gafara ne Mai jinƙai Mai ƙaunarmu, Mai haƙuri, Mai karamci, kuma Mai yawan ni’ima.

Ya ku masu azumi kuma masu tsayuwar dare!

Ina muku albishir da ni’imomi da za ku samu a waɗannan ‘yan kwanaki kaɗan masu albarka, ku yi ƙoƙarin neman kusanci zuwa ga Ubangijinku ta hanyar ayyuka na farillai da nafiloli, ku kuma riski abin da ya kuɓuce muku na manyan ayyuka, kuma ku kwankwaɗi zumar ƙulla alaƙa da Ubangijinku da kyawawan salloli da i’itikafi da roƙon Allah da addu’a, domin har yanzu dama ba ta gushe ba, kuma kasuwanci bai gushe ba yana mai albarka, ga wanda ya salwantar da kwanakin Ramadana kuma ya tozarta su, ya bi da ransa hanyoyin sakaci sai ya halakar da shi.

Kuma a cikin wannan wata mai girma kuma watan alkhairai, ana so a yawaita kyawawan addu’o’i, domin haƙiƙa Allah Ya sanya addu’a a tsakiyar ayoyin azumi kamar yadda Ya ce: (Kuma idan bayiNa suka tambaye ka game da Ni, to, ka ce Ina kusa, Ina karɓar addu’ar mai addu’a idan ya roƙe Ni).

Saboda haka, ku ɗaga hannayenku sama kuna masu ƙasƙantar da kai gare Shi ta hanyar addu’a ga kawunanku da iyalanku da ƙasarku da al’ummarku, kuma ku yi wa Allah Tsarkakakken Sarki magiya ta hanyar addu’a, ku kai Masa kokenku da roƙonku, a kan Ya taimaki ‘yan’uwanku masu rauni da waɗanda annoba ta sauka musu, da waɗanda suke ƙarƙashin zalunci a ko’ina, ku roƙi Allah Ya yaye baƙincikinsu da damuwarsu, Ya kwaranye tsananinsu da ƙuncinsu, lallai Shi Maji roƙo ne kuma Mai karɓar addu’a.

Wannan kenan:

Ku yi salati da sallama – Allah Ya muku rahama – ga Annabin rahama da shiriya, mafificin masu azumi, kuma mafi darajar masu tsayuwar dare, kamar yadda Ubangijinku Ubangijin talikai Ya umurce ku, sai Ya ce kuma dama Shi ne Mafi gaskiyar masu zance: ((Lallai Allah da Mala’ikunSa suna salati ga Annabi, ya ku waɗanda kuka yi imani ku yi salati a gare shi da sallama mai yawa)).

Kuma ya zo a Hadisi ingantacce cewa: (Duk wanda ya yi salati a gare ni sau ɗaya, to, Allah Zai masa salati sau goma). Ya Ubangiji Ka yi daɗin tsira a gare shi a duk lokacin da taurari suka haskaka a duhun dare da ƙarshen dare. Ka haɗa da Alayensa da dukkan Sahabbai gaba ɗaya, waɗanda suka dace da falala kuma suka kasance mafiya kyawun tarihi

Ya Allah Ka yi salati da sallama ga Annabinmu Muhammad da Alayensa nagartattu tsarkaka, da Sahabbansa masu hasken fuska masu albarka, da Halifofinsa shiryayyu – Abubakar da Umar da Usman, da Ali – da sauran Sahabbai bakiɗaya, da Tabi’ai da waɗanda suka bi bayansu da kyautatawa har zuwa Ranar sakamako, Ka haɗa mu tare da su cikin falalarKa da kyautarKa da karamcinKa, ya Mafi karamcin masu karamci.

Ya Allah Ka ɗora mu a bisa tafarkin masu taƙawa kuma mutanen kirki, kuma Ka sanya mu daga cikin bayinKa na ƙwarai zaɓaɓɓu, kuma Ka yi mana tagomashi da ‘yantuwa daga wuta gabaɗayanmu, don tausayinKa ya Mabuwayi ya Mai yawan gafara. Ya Allah Ka ɗaukaka Musulunci da Musulmai, Ka kare shingen addini, Ka sanya wannan ƙasa ta zamto mai aminci da kwanciyar hankali, da yalwa da wadata, da sauran ƙasashen Musulmai.

Ya Allah, Ka amintar da mu a cikin ƙasashenmu, ka datar da shuwagabanninmu da jagororinmu, Ka ƙarfafi Shugabanmu kuma Jagoranmu da gaskiya da dace.

Ya Allah Ka datar da Shugabanmu Hadimin Masallatai biyu masu alfarma da Magajinsa ga abin da yake ɗaukaka ne ga Musulunci da kuma gyaruwa ne ga Musulmi, da kuma abin da yake alheri ne da shiriya ga mutane da ƙasa, Ka saka musu da mafi alherin sakamako bisa abin da suka gabatar da wanda suke gabatarwa na hidindimu masu girma da mafi kyawun kula ga Masallatai biyu masu alfarma da maniyyata da masu umara da maziyarta.

Ya Allah ka datar da dukkan shuwagabannin Musulmi. Ya Allah Ka datar da jami’an tsaronmu da masu dako a iyakokinmu. Ya Allah duk wanda yake nufatarmu da Musulunci da Musulmi da wani sharri, Ka sa ya shagala da kansa, Ka mayar da mugun nufinsa a kansa, Ka sanya halakarsa cikin dabararsa, ya Maji roƙon bayi.

Ya Allah, Ka haɗa kan al’umma akan Alƙur’ani da Sunna, ya Ma’abocin kyauta da falala da baiwa. Ya Allah ba a iya karya rundunarKa, kuma alƙawarinKa ba ya sauyawa, Ka tseratar da masu rauni daga cikin Musulmi a ko’ina, Ka taimaki ‘yan’uwanmu a Falasɗinu, Ka kare Masallacin ƙudus, ka sa zama mai ɗaukaka da buwaya har zuwa Ranar sakamako.

Ya Allah kamar yadda Ka taimaki masoyanKa a ranar yaƙin Badar, ranar da aka rabe tsakanin ƙarya da gaskiya, Ka taimake su a kowane zamani da kowane wuri.

Ya Allah Ka halakar da maƙiyansu, Ka tarwatsa taronsu, Ka sanya su su zamto izina ga masu ɗaukar izina. Ya Allah lallai Kai Mai afuwa ne Kana son afuwa, saboda haka, Ka yafe mana ((Ya Allah, Ka ba mu kyakkyawa a duniya Ka bamu kyakkyawa a Lahira, Ka tsare mu daga azabar wuta)). ((Tsarki ya tabbata ga Ubangijinka Ubangijin buwaya daga abin da suke siffantawa, aminci ya tabbata ga Manzanni, godiya ta tabbata ga Ubangijin talikai).

Don karanta Yaƙe-yaƙen Annabi SAW A Watan Ramadan danna nan

Edita:@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceFalalar Gaggauta Shan Ruwa
Labarin na GabaYadda Ake Yin Umara (Umrah) Dalla-dalla