Turawa sun zo sun iske ƙasar Hausa cike da ilmin abin da ya shafi karatu da rubutu a cikin Hausar ajami, kenan ko da Bature ya zo ƙasar Hausa ya iske su da ilmin zamani. Masana da dama kamar su (Magaji, 1982 da Sa`idu, 1985 da Hafsat Tsiga, 1987 da Yahya, 1988 da Ampah, 1989 da da Dogara, 2008 da Sulaiman, 2008 da Gusau, 2008 da Malumfashi, 2009,) sun kawo bayanai gwargwado masu gamsarwa game da samuwar rubutun boko da yadda ya yi tasiri a ƙasar Hausa.
Abin da kurum za a ƙara a nan bai wuce cewa an fara samun ɓurɓishin labarin ƙasar Hausa a wurin Turawa ta hannun Al-Hassan Ibn Muhammad Al-Wizas Al-Fasi, wato Leo Africanus wanda aka tsare a kurkuku a ƙasar Italiya inda ya bayyana a cikin littafinsa Na Bakwai ziyarar da ya kai ƙasar Barno da wasu daulolin na Hausa a tsakanin 1513 zuwa 1515. Samun wannan littafi shi ya ba mutanen ƙasar Turai haske kan yanayin ƙasa da rayuwa a wasu ƙasashe na Afirka ta Yamma.
Wannan haske da ƙasashen Turai suka samu game da ƙasashen Afirka, shi ya sanya suka fara ƙoƙarin turo mutanensu domin su dubo musu abin da ke faruwa a wannan yanki na Afirka. An samar da ƙungiyoyi masu manufofi daban-daban, musamman waɗanda za su binciko ainihin yanayin ciki da wajen Afirka.
(Yahaya, 1988:75) ya ruwaito Turawa masu yawon gano Afirka na farko hankalinsu ya fi karkata ne kan labaran ƙasar wuraren da suka ziyarta kamar kogunansu, tuddai, tsirrai, bishiyoyi, albarkatun ƙasa, sunayen garuruwa da fasalin mazaunansu, da tsarin mulkinsu, da cinike-cinikensu da sauransu. Saboda haka, su ba su ƙarfafa bincike kan harsunan waɗannan mutanen ba.
Daga ƙarni na 18 zuwa na 19 ne aka fara turo masu bincike, musamman bincike kan al`adu da harsuna da addinan ƙasashen Afirka. Akwai ƙungiyar ‘yan mishan wadda ta zo Afirka a daidai wannan lokaci ƙarƙashin jagorancin J.F Schon, da C. H. Robinson, da Hans Vischer, da G.P Bargery da wasunsu da dama.
Daga hannun waɗannan `yan mishan ɗin da `yan leƙen asiri labaran ƙasar Hausa da jama`arta suka isa ƙasashen Turai. Wasunsu kuwa kamar su Robinson, da Miller, da Richardson, da Ryder, da Burgin dama sun zauna a Tripoli sun koyi harshen Hausa, wannan ya sa ko da suka zo ƙasar Hausar ba su sha wata wahala ba, kuma wasu daga cikin su sun zagaya, kuma sun zauna a sassan ƙasar ta Hausa, daga baya suka koma gida suka bayyana abubuwan da suka gano, wasu kuma suka ci gaba da rayuwa a ƙasar suna ayyukan yaɗa addini. (Malumfashi, 2009).
Zaman waɗannan mutane a ƙasar Hausa ya ba su damar fara samar da abubuwan karantawa daga abin da suka ji, wanda wannan ya taimaka ƙwarai da gaske wurin gina adabin Hausa da al`adun Hausawa. J.F Schon shi ne zaƙaƙuri, kuma fitacce wurin rubuce-rubuce cikin Hausa a Turai a cikin ƙarni na 19. Bayan shi akwai irin su G.P Bargery, da W.R. S. Miller, da Hans Vischer waɗanda duk ƙungiyar mishan ta C.M.S ta turo su.
Wannan zuwan bakin Turawa ya zama tubali wajen juya adabin bakan Hausa ya koma a rubuce a karo na biyu. Za a iya cewa kusan tun daga wannan lokacin ne aka fara mai da labarai da tatsuniya da karin maganganu da maganganun azanci da kuma al`adun Hausawa a rubuce cikin Hausar boko.
Kusan daga ƙarshen wannan ƙarni na 19 zuwa farkon ƙarni na 20 ne aka samar da litattafai masu yawa da suke ɗauke da wannan fasalin, wasu daga cikinsu sun haɗa da ; Hausaland na C.H. Robinson (1893), da Spécimens of Hausa Literature na C. H. Robinson (1896), da Hausa Notes na W.R. Miller (1901), da Batu Na Abubuan Hausa na W.H. Brooks (1903), da Littafe Na Tatsunniyoyi Na Hausa na Frank Edgar (1911), da Hausa Superstitions and Customs na Tremearne (1913), da sauransu dai da dama. (Yahaya, 1988:81).
Bayan `yan Mishan da suka mamaye ƙasar Hausa, sai kuma Turawa `yan mulkin mallaka suka diro wa ƙasar. A daidai 1900 ne gwamnatin Ingila ta miƙa wa Gwamna Lugga jan ragamar mulkin Nijeriya ta arewa. Daga kama aikin shi na Gwamna ya fara aiwatar da wasu canje-canje. Ya tumɓuke tutar Royal Niger Company a Lakwaja ya sanya ta mulkin Ingila.
Ya tashi hedikwatar jihar arewa daga Lakwajar ya mai da ta Zungeru. Ya dinga aika wa sarakunan ƙasar Hausa da su ba da kai, wasu sun bi, wasu kuwa suka ƙi. Ya tura da sojoji garuruwan na ƙasar Hausa kamar Zariya da Yola da Daura da Bauci da Barno da Katsina sai Sakkwato, inda bayan hijirar sarkin musulmi Attahiru suka ƙulla yarjejeniya bayan an fafata (Yahaya, 1988:89).
Bayan Turawan mulkin mallaka sun ci ƙasar Hausa, dama sun iske harsashin da ƙungiyoyin mishan suka assasa na koyon karatu da rubutun boko, ga kuma na ajami da Larabci da ya daɗe tare da al’ummar, sai suka gina makarantun boko bisa wannan harsashi, duk rubutu da karatu aka ci gaba da yin su cikin Hausar boko.
Saboda haka, kusan daga wannan lokacin ne aka fi samar da ayyuka wajen adana labaran gargajiya na Hausa a rubuce. Daga wannan lokacin ne, wato a farkon ƙarni na ishirin lokacin da Turawan mulkin mallaka suka mamaye ƙasar Hausa ƙarƙashin jagorancin gwamna Lugga, sun yi iyakar bakin ƙoƙarinsu domin su tafi da hanyar rubutu ta Ajami da Larabci, don cimma burinsu na mulkin mallaka da ayyukan mishan, amma ba a je ko`ina ba suka kasa.
Wasu daga cikinsu suka ba hukumomin mulkin mallakar shawarar lallai hukumar ta sake salo, domin kar a bar Hausawa wurin samun ayyukan gwamnati. Shi kan shi gwamna Lugga sai ya hango cewa dole ne ya sami ma’aikata `yan ƙasa waɗanda za su taimaka masa wajen gudanar da harkokin mulki a ofisoshin gwamnati a bisa tsari irin na Turai, kafin a samu yin haka kuwa, dole sai an kafa makarantun ilmin boko, haka kuma hukumomi sun lura ya kamata a ba al`ummar Hausa ilmin da mulkin mallaka ya zo da shi, wato karatu da rubutu irin na Ingilishi, maimakon wanda suke da shi na Larabci da Ajami. Wannan shi ne ya haifar da buɗe makarantun boko a arewacin Nijeriya daga Turawan Mulkin Mallaka.
Bayan samuwa da bunƙasuwar makarantu da malamai a sassa da Lardunan Arewa, sai wata matsala ta kunno kai, wannan matsalar kuwa ita ce ta samar da litattafan koyarwa a waɗannan makarantun. Ganin wannan matsalar na neman kawo tsaiko ga makarantun nan, sai Gwamnatin jihar Arewa ta kafa hukumar fassara (Translations Bureau ) a shekarar 1929, An ɗora wa wannan hukuma ta fassara nauyin samar da litattafai ta hanyar fassara daga wasu harsuna musamman Larabci da Turanci zuwa Hausa.
Sannan kuma ta taimaka wurin wallafa litattafai cikin harshen Hausa, ta kuma shirya litattafai domin manya da ƙanana don karantarwa a makarantu, daga ƙarshe kuma ta taimaka wa `yan ƙasa su yi wallafar ƙagaggun labaran cikin Hausa. Wannan hukuma ta yi aiki ƙwarai da gaske wurin samar da litattafan da aka sa ta samar.
Domin faɗaɗa aikin wannan hukuma ne ya sanya a shekarar 1933, aka canza wa wannan hukuma ta fassara suna zuwa hukumar Talifi (Literature Bureau) domin ta faɗaɗa daga aikin da hukumar fassara ke yi. Wannan hukuma ta Talifi ta yi ta ƙarfafa bayar da ilmin boko, ta kuma samu goyon baya daga `yan ƙasa, daga baya ta ga ya kamata a faɗaɗa wannan shirin ya haɗu da tarihin ƙasa da sauransu. Saboda haka sai aka samar da Jaridar mai suna ‘Jaridar Arewa’ wadda ake bugawa cikin harsunan Hausa da Larabci, da kuma Turanci, har zuwa shekarar 1939 da aka samar da Gaskiya ta fi Kwabo.
Ayyukan wannan hukuma sun ci gaba har cikin 1945, amma fa duk wannan aikin da wannan hukumar ke yi, ba ta da injunan ɗab`i nata na kanta, sukan tsara aikinsu, su aika da su maɗaba’a ta Jos, ko Kaduna ko kuma Ikko, in kuma ta yi ƙamari sai a tura da shi Ingila. Domin a samu wurin buga litattafai da jarida da sauran talife-talifen da hanzari a hukumar, sai Gwamnan Nijeriya na wannan lokacin Sir Arthur Richards ya nemi Gwamnatin Ingila ta taimaka wa hukumar Talifi da kuɗin sayen Injunan buga litattafai da kuma na gina kamfanin wallafa.
Wannan ne ya sa aka kafa kamfanin Gaskiya wanda ake kira Gaskiya Corporation a Tudun Jukun cikin garin Zariya a shekarar 1945. Shi wannan kamfani na Gaskiya Corporation shi ne ya ci gaba da ɗaukar nauyin wallafa duk litattfai da jaridar da Hukumar Talifi ke samarwa. Ire-Iren waɗannan litattafn sun haɗa da ; Ka Koyi Karatu, da Ka Ƙara Karatu, da Ka Yi Ta Karatu, da Bala Da Babiya, da Yawo Duniya Haji Baba, da Mango Park Mabuɗin Kwara da sauransu da dama. (Yahaya, 1988:97).
A shekarar 1953, Gwamnan jihar arewa na lokacin Sir Bryan Sherwood Smith (Mai Wandon Karfe) ya kafa wani kwamiti na yaƙi da jahilci, wannan kwamitin ya duba hanyoyin da suka kamata a bi domin samar da ilimin zamani. Sannan kuma suka ba da shawarar hanyar da za a bi domin a yi yaƙi da jahilci, ita ce a samar da litattafai cikin Hausa rubutun boko da na ajami da kuma wallafa litattafai cikin harsunan arewa.
Wannan ne ya sa aka samar da Hukumar Yaƙi Da Jahilci Ta Arewacin Nijeriya, Northern Region Literacy Agency, (NORLA) a shekarar 1954, aka naɗa mata shugaba wani Bature W.F. Jefferies, daga nan sai aka ɗauke nauyin buga Litattafai daga Gaskiya zuwa NORLA, kuma yawancin ma`aikatan Gaskiya ɗin suka koma NORLA ɗin. Hukumar NORLA ta yi matuƙar ƙoƙari wurin samar da litattafai, domin a iya cewa babu wata hukuma da ta yi aikin da hukumar NORLA ta yi.
Baya ga litattfan yaƙi da jahilci da wannan hukuma ta samar, ta kuma wallafa litattfai don makarantu da sauran jama`a masu son abin karantawa don ƙaruwa da ilimi ko don nishaɗi.
Haka kuma NORLA ta sake buga wasu litattafai da hukumomin baya suka samar, daga cikin litattafan da NORLA ta samar akwai na addini; Ibada Da Hukunci, da Jagorar Mai Sallah, da Tarbiyya ga mutum, da sauransu. Akwai na labaran hira ; Bayan Wuya sai Daɗi, da Sauna, da Nagari Na kowa, da Tauraruwar Hamada, da Da’u Fataken Dare da sauransu. Akwai kuma na tarihi kamar su ; Sarauniyar Zazzau, da Zuwan Turawa Nijeriya ta Arewa, da Wali Ɗanmarna da sauransu.
Bayan litattafai da hukumar NORLA take tsarawa, ta kuma rinƙa buga jaridu na kusan kowane lardi, duk da cewar kuma jaridar Gaskiya wadda dama ita ta kowane lardi ne tana nan tana fitowa. Ita dai Hukumar NORLA duk da wannan jan aiki da ta yi, ta samu matsala, inda a 1959 ta durƙushe saboda hada-hadar siyasa da ta mamaye arewacin Nijeriya.
`Yan kuɗaɗen da hukumar ke samu daga Gwamnatin Jihar Arewa suka tsaya, daga nan sai hukumar ta mutu. Ita dai wannna hukuma ta NORLA ta yi zamani ne daga 1954 zuwa 1959, amma sauran kayan aikin hukumar sai suka koma kamfanin Gaskiya inda aka ci gaba da kula da su, sannan kuma kamfanin na Gaskiya ya ci gaba da buga litattafan da hukumar NORLA take bugawa.
Da tafiya ta yi tafiya ne Gwamnatin jihar Arewa ta lura ayyukan sun yi wa kamfanin Gaskiya yawa, wannna ne ya sanya aka ɗauke aikin buga jaridar Gaskiya ta fi kwabo daga kamfanin Gaskiya, domin a rage masa aiki, aka bar su da buga litattafai kurum. Da gwamnati ta ga aikin ya yi yawa, sai ta yi ƙoƙarin samun wani kamfani wanda zai ci gaba da wannan aikin. Wannan ne ya sanya aka nemo kamfanin Macmillan daga Ingila inda aka ƙulla yarjejeniya da shi aka samar da kamfanin wallafa na NNPC (Northern Nigeria Publishing Company) a watan Oktoba na 1966.
An sakar wa kamfanin NNPC mara na ya zaɓi duk littafin da ya ga dama bugawa, shi kuma kamfanin Gaskiya sai aka bar shi kurum a matsayin kamfanin kasuwanci. Sannan kuma shi wannna kamfani na NNPC yana karɓar litattafai daga marubuta Hausa domin ya buga musu.
Wannnan kamfani shi ma ya sake buga wasu daga cikin litattafan da hukumomin baya suka samar, wasu daga cikin litattafan da suka samar sun haɗa da ; Tauraruwa Mai Wutsiya na Umaru Dembo, da Uwar Gulma na A.M. Sanda, da Daren Sha Biyu na Ibrahim Yaro, da Iliya Ɗan Mai Ƙarfi na Ahmadu Ingawa, da Matar Mutum Ƙabarinsa na Bashir Roukbah, da dai sauransu da dama, wasu na addini ne, yayin da wasu waƙoƙi ne ko labarai ko kuma wasa kwaikwayo.
Bayan wannan kamfani na NNPC da gwamnati ta samar, akwai wasu kamfanonin wallafa na raya al`adun Hausawa da samar da ƙagaggun litattafan Hausa. Akwai kamfanin litattafai na Oxford wanda ya koma Úniversity Press Limited’ (U.P.L), akwai kuma kamfanin Longman, shi ma na tallar litattafai ne, akwai kamfanin Thomas Nelson, akwai kamfanin Alhuda-huda Publishers, da Ilesanmi, da Truimph Publishers da dai sauransu da dama .
A shekarar 1978 ne, kamfanin NNPC ya sanya gasar samar da ƙagaggun labaran Hausa da kuma wasan kwaikwayo. A tarihin ƙagaggun labaran Hausa, a iya cewa wannan gasa ita ce ta biyu, marubuta da yawa sun shiga wannan gasa, amma daga ƙarshe aka fitar da waɗanda suka lashe gasar kamar haka;
- Mallakin Zuciyata na Sulaiman Ibrahim Katsina
- So Aljannar Duniya na Hafsat A. Abdulwaheed
- Amadi Na Malam Amah na Magaji Ɗanbatta
Bayan wannan gasa da kamfanin NNPC ya samar, akwai wata gasa da za a iya kira ta uku a shekarar 1982, wadda ma’aikatar al’adun gargajiya ta tarayya ta shirya don bunƙasa manyan harsunan Nijeriya. Mutane wajen 30 sun shiga wannan gasar, amma dai an zaɓi guda bakwai waɗanda ake jin sun yi fice aka buga su, waɗanda aka zaɓa kuwa su ne;
- Turmin Danya Na Sulaiman Ibrahim Katsina
- Zaɓi Naka Na Munir Mohammed Katsina
- Ƙarshen Alewa Ƙasa Na Bature Gagare
- Tsumangiyar Kan Hanya Na Musa Muhammad Bello
- Dausayin Soyayya Na Bello Sa`id
- Soyayya Ta Fi Kuɗi Na Hadi Alƙanci
- Wasa Ƙwaƙwalwa Na Mohammed Yahuza
Daga wannan lokaci ne abubuwan ɗab’i suka fara sauya fasali a arewacin Nijeriya, harkar samar da ƙagaggun labaran Hausa suka fara ɗaukar wani sabon salo, samar da litattafan sai suka tashi daga kamfanonin na hukuma ko waɗanda hukumar ta amince da su, sai marubuta suka fara samar da litattafansu, suna fiddo su, sannan kuma fasali da jigon litattafan duk suka sauya daga yadda aka san su, suka koma na wasu jigogi daban, wannan sabon fasali shi ne masana suka bayyana da Adabin Kasuwar Kano ko Labaran Soyayya, ko ƙagaggun Labaran Hausa da sauransu, kamar yadda za mu gani a babi na gaba.
Naɗewa
A wannan babin an kalli samuwar ƙagaggun labaran Hausa kama daga tatsunniya da tarihihi da labari da kuma ƙissa har zuwa lokacin da suka canza fasali suka tashi daga na ‘KA’ suka koma a rubuce wato bayan haɗuwar Hausawa da baƙi (Larabawa da Turawa).
Sannan an ga yadda aka fara samar da karatu da rubutu a ƙasar Hausa da kuma yadda aka samar da ƙagaggun littattafan labaran Hausa daga gasa, wanda wannan ya kasance tamkar mabuɗin farko wajen samar da abin da ake kira Adabin Kasuwar Kano.
Wannan bayani an ciro shi ne daga rubutaccen kundi mai taken: ADABIN KASUWAR KANO: Nazari da Sharhi Game da Ƙagaggun Labaran Hausa (1984-2008) wanda Bashir Abu Sabe 07/211111002 (M.A Hausa Studies) USMANU ƊANFODIYO UNIVERSITY, SOKOTO, NIGERIA ya wallafa.
Don karanta Ƙagaggun Labaran Hausa Na Zamani danna nan
Edita@rumasau-kallamu