Falalar Tafiya Masallaci

0
49

Tafiya masallaci domin yin ɗaya daga cikin salloli biyar bayan alwala. Alokacin da mutum ya ƙare alwala idan na miji ne duk takun da zaiyi ko ɗaga ƙafa yayin tafiyar sai an ɗaga darajar sa an yafe masa zunuban sa,hakama kuma mace lokacin da take tafiya wajan da za tayi sallah,ita nan ne masallacin ta.

Anaso mutum yayi tafiya cikin nutsuwa domin tara lada mai yawa.
Isowar sa masallaci ko kuma isowar ta wajan da take yin sallah,idan da dama anaso ayi nafila raka’a 2 kafin sallar farilla.

Ga sunayen nafilfilin salloli biyar da yadda ake gabatar da su.
Ana kiran su da larabci (Assunanur rawaatibi,Assunanun attabi’atu lil fara’idi). ma’anar su a harshen hausa jerarrun sunnoni.

Domin karanta cikakken bayani a kan Tsayuwar Watan Ramadan danna nan.

Idan da asuba ne ana yin raka’a biyu wacce ake kiranta da larabci (raka’ataanil fajri) ma’ana raka biyu lokacin fitowar alfijir, idan azahar ne ana yin raka’a biyu ko huɗu kafin sallar azahar, sannan kuma raka’a biyu bayan sallar azahar,idan da la’asar ne kuma raka’a biyu kafin sallar la’asar,idan da magriba ce raka’a biyu bayan sallar magriba,idan da isha’i ne raka’a biyu bayan sallar Isha’i.shine yawan su yakai raka’a 14 idan mutum yayi huɗu kafin azahar idan kuma biyu yayi,sun tashi raka’a 12 kenan.

Idan mutum yayi sallama yana zaune inda yake bayan nafila kafin sallar farilla,mala’iku zasu dinga masa adu’a suna cewa Allah ya masa rahama,ya masa gafara,yayi masa afuwa matsawar baiyi hadasi ba kuma bai cuci wani a lokacin, wannan falalar duk ɗaya ne ga mace ko na miji.

Domin karanta Sharuɗan Wajabcin Azumin Watan Ramadan Danna nan 

labarin da ya wuceYadda Ake Zaman Jiran Liman Bayan Nafila
Labarin na GabaYadda Zaki Inganta Hallayarki Da Ɗabi’u Masu Kyau
wikiHausa
wikiHausa kundin ilimi (insakulofidiya) ce da ke ilimantar da jama'a yara da manya da maza da mata wajen samun ilimi a saukake, cikin harshen Hausa.