Falalar Malamai Da Ta’aziyyar Masani Shehu Ahmad Bamba (Ƙala Haddasana)

0
8

Sahabi Aliyu R.A ya faɗa ga Jabir ɗan Abdullahi R.A cewa “Duniya ta dogara ne a kan abu huɗu; Addini, da Malami, da mai yin aiki da ilimin sa, sai Jahili wanda ba ya girman kai wajen neman sani, da kuma Mawadaci wanda ba ya rowa da dukiyar sa.

Marigayi Sheikh Dr.  Ahmad Bamba ya faɗa mana cewa ilimi ba komai ba ne sai sanin abu a zuciya da kuma gaskatar sa a zahiri, yayin da jahilci ke nuni da kiyaye abu a zuciya wanda a zahirance ba gaskiya ba ne. Saboda haka a  cewar sa ba kawai rashin sanin abu ake kira jahilci ba, a a har ma da sani gami da riƙo na abinda bai gaskata ba.

Rayuwa irin ta Dr Ahmad madubi ce ga ɗaukacin al’ummar musulmi. Shi mutum ne mai kyakkyawar fahimta ga lamurran addini, amma mai zafafawa wajen kare martaba irin ta Annabi Muhammad s.a.w.

Mai kimanin shekaru 82 da haihuwa, wanda ya rasu a yau Jummu’a 7/1/2021, Marigayi Dr Ahmad Bamba ya shafe ɗaukacin rayuwar sa wajen nema da kuma bayar da sani. Ya shafe sama da shekaru 20 yana ɗaukar darasi a Madina, masallacin Annabi Muhammad s.a.w.

Sannan ya fassara Littafin Muwaɗɗa wallafar Imamuna Maliku ɗan Anas daga harshen larabci zuwa harshen Hausa, baya da karantarwar sa ga manyan littattafai irin su Sahih Bukhari, Sahih Muslim, Sunnani Darimi, da makamantan su duk a cikin harshen Hausa.

Tabbas, rasuwar sa babbar asara ce ga kafatanin al’ummar musulmi musamman Hausawa.Ya zo a cikin littafin ‘Al ilmu Huwal Imamu’ na Shekh Ibrahim Nyasi cewa Hanyar aljanna ta na hannun mutane guda huɗu; Malami, da mai gudun duniya da mai ibada da kuma mai jihadi fi sabilillahi. Shi Malami idan ya kasance mai gaskiya ne cikin zuciyar sa, tabbas Allah zai azurta shi da Hikima.

Duk kuwa wanda aka bai wa Hikima alal haƙiƙa an ba shi gagarumar baiwa a nan duniya da gobe lahira kamar yadda yadda ya zo a cikin littafin Allah Alqurani. An tambayi Ɗan Mubarak cewa su wanene mutane?, sai yace ‘Malamai’, sai aka ce masa su wanene sarakuna?

Sai yace masu gudun duniya, sai aka ce su wanene ƙasƙantattu?, sai yace masu cin duniya da addini. Don haka, ana iya cewa lallai malamai mutane ne masu daraja a cikin al’umma. Abdul-Aswad yana cewa babu wani abu wanda yafi Ilimi ɗaukaka. Sarakuna masu yin hukunci ne ga jama’a, yayin da Malamai ke yin hukunci a garesu.

AHNAF R.A yana cewa Malamai sun kusa kasancewa iyayen giji.. dukkan ɗaukakar da ba a ƙarfafe ta da ilimi ba, ƙarshen ta ƙasƙanci ce. Annabi Muhammad s.a.w ya faɗa cewa “Malamai, su ne magada Annabawa” (Tirmizi, Abu Dawood da Ibn Maja duk sun ruwaito shi)

Allah Ta’ala kuwa ya faɗa cewa “Iyaka dai masu jin tsoron Allah su ne Malamai” (Suratul Fathi, 28). Babu buƙatar zafafa yabo ga marigayi Mallam Ahmad Bamba, domin shi ba mai son yabo ko kwarzantawa ba ne a zamanin rayuwar sa, amma shi ne wanda ya jaddada Sunnah a ƙasar Hausa bayan da ta ɗauko dusashewa.

Shi mutum ne wanda yake son Allah da Manzon sa, wanda yake tarbiyantar zukatan bayin Allah a kan bautar Allah ta tsanin manzon sa Annabi Muhammad s.a.w da mayar da lamurra a gareshi, kuma mutum ne maras kwaɗayi, mai darrajanta ilimi da darrajanta kansa, gami da faɗar gaskiya walau ga shuwagabanni ko ga mabiyansu.

Allahu Akbar, shi mutum ne mai daraja a duniyar musulunci, tushen darajar sa kuwa bai wuce ga riƙon sa ga sunnar Annabi Muhammad s.a.w ba, da tsantsenin sa kai kace shi ne Imam Maliku bn Anas ko Imam Hasanul Basri. Haƙiƙa, rayuwar sa ta kasance abar koyi ga al’ummar musulmi.

Wani sashen masana sun faɗa cewa An fifita Imam Hasanul Basri a kan sauran Tabi’ai, saboda abubuwa guda 5;-

1. Ba ya umarni da aikata wani aiki face ya fara aikatawa.

2. Ba ya hanuwa ga barin wani aiki face ya fara hanuwa daga gareshi.

3. Duk wanda ya nemi wani abu daga abinda Allah ya hore masa zai ba shi.

4. Ya kasance tana wadatuwa da ilimin sa ga barin neman wani abu a wajen mutane.

5. Ya kasance ciki da wajen sa duk ɗaya ne.

Tabbas, duk waɗannan siffofi guda biyar sun tabbata ga Marigayi Shekh Ahmad Ibrahim Bamba. Ga shi kuma ya samu cikawa irin tasa.. da fatan Allah ya rahamshe su duka amin.

Abdullah bin ‘Amr Ibnul ‘Ash ya ruwaito daga Annabi Muhammad s.a.w cewa “Lallai, Allah ba ya ɗauke ilimi daga hanawar sa ga bayin sa. Sai dai yana ɗauke ilimi ne daga mutuwar malamai ta yadda tsarkakan mutane za su gushe, sai mutane su naɗa wawayen mutane a shugabanci. Sannan idan aka tambaye su, sai su yi magana ba da ilimi ba. Sai su taɓe kuma su yi asara.” (Al-Bukhari da Muslim suka ruwaito).

Kaicho da rashin babban masani Dr Ahmad Bamba, to amma ya kamata kowa ya sani wannan duniya ba abar dawwama ba ce. Tabbas, kowanne mai rai zai ɗanɗana mutuwa. Kuma tabbas, yadda Dr Ahmad ya koma ga mahaliccin sa, kowannen mu lokaci yake jira domin komawa zuwa ga Allah. Don haka ya kamata mu shagaltu wajen aiki da koyarwarsa, da neman ilimi, da bin Allah da kuma neman dacewar Allah da samun Aljanna.

Da fatan Allah ya gafartawa Dr Ahmad Ibrahim Bamba, Allah ya tallafi bayan sa amin.

Danna nan don karanta Cin Zarafin Ƙananun Yara Da Kariya A Bisa Haka

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceTatsuniyar ‎Gizo Da Namun Daji
Labarin na GabaHadisi Na Huɗu A Kan Falalar Adalci Da Tausayawa Mabiya Da Illolin Gallaza Musu
Sadiq Tukur Gwarzo
Sadiq Tukur Gwarzo marubuci ne mai binciken tarihi da son taskance ilimi da taimakon al'umma.