An karɓo daga Abu Musal Ash’ari (RA) ya ce: Manzon Allah (S.A.W.) ya ce: da ni, shin ba na shiryar da kai ba zuwa ga taska daga taskokin Aljanna? Sai na ce: ” Shirya da ni” sai ya ce: “Laa haula wala ƙuwwata illa billahi“
(Bukhari 6384, Muslim 2704).
Ana yawaita faɗin “la haula wala ƙuwwata illa billahi” domin neman taimakon Allah kan dukkan abin da ya gagari mutum ko yake da wahala a gare shi.