Falalar I’itikafi

0
713

I’itikafi shi ne tarewa a masallaci domin yin ibada. Ana son yin I’itikafi a kwanaki goma na ƙarshen Ramadan, kamar yadda Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasalam) ya kasance yana yin ittikafi har Allah ya karɓi ransa.

An karɓo daga A’isha (Radiyallahu anha) ta ce: Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasalam) ya kasance yana i’itikafi a goman ƙarshe na Ramadan har Allah ya karɓi ransa. iyalansa ma sun yi i’itikafi bayan wafatinsa. (Bukahri 2026 Muslim 1172).

Domin karanta cikakken bayani a kan Falalar Raya Daren Lailatul Kadari danna nan.

Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Ingantattun Nafiloli Da Falalarsu wanda Usman Abubakar Muhammad (Shehu Mansur Dala) ya wallafa shi domin karanta cikakken littafin danna nan.

labarin da ya wuceFalalar Raya Daren Lailatul Ƙadari
Labarin na GabaƘara Yawaita Ibadu Da Alhairi A Goman Ƙarshe Na Ramadan