Falalar Ba Da Sadaka Ga Ɗan Uwan Da Yake Gaba Da Kai

0
19

An Karɓo daga Hakim (Radiyallahu Anhu) ya ce: wani mutum ya tambayi Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) cewa wacce sadaka ce mafificiya?

Sai ya ce: “sadaka da ka bawa ɗan’uwan da yake gaba dakai”. (Imam Ahmad 14896). 

FALALAR DASA BISHIYA 

An karɓo daga Jabir (Radiyallahu Anhu) ya ce: “Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: “Duk musulmin da ya dasa bishiya, za a rubuta masa lada duk lokacin da aka ci wannan dashe. Ko aka sata, ko naman dawa ya ci ko tsuntsu ya ci, ko aka ragi dashen.”(Bukhari 2320, Mslim 1552). 

FALALAR YIN SADAKA A ASIRCE 

An karɓo daga Abu Harairata (Radiyallahu Anhu) yace: Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) “Mutane bakwai Allah zai sanya su a cikin inuwarsa a yinin da babu wata inuwa sai inuwarsa:

  1. Shugaba mai adalci. 
  2. Matashi da ya taso kan bautar Allah. 
  3. Mutumin da zuciyarsa take a rataye a masallaci. 
  4. Da mutane da suke ƙaunar juna saboda Allah, suka haɗu a haka. Suka rabu a haka. 
  5. Da mutumin da kyakkyawar mace mai matsayi ta neme shi, sai ya ce: Ni ina tsoron Allah. 
  6. Da mutumin da yayi sadaka a ɓoye ta yadda hagunsa ba ta san abinda da damansa ta bayar ba. 
  7. Da mutumin da ya tuna Allah yana shi kaɗai har ya yi ƙwalla. (Bukhari 1423, Muslim 1031). 

Domin karanta bayani akan Falalar Kuka Ranar Ashura Danna nan 

FALALAR BA WA ƊAN UWA SADAKA 

An karɓo daga Salman ɗan Amr (Radiyallahu Anhu) haƙiƙa Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) yace: “Bai wa miskini sadaka lada ɗaya ne bai wa ɗan uwa sadaka lada biyu ne” (Ladan sadaka da ladan sada zumunta) (Tirmizi 658). 

FALALAR SASSAUCI GA WANDA AKE BI BASHI 

An karɓo daga Adul Yasar (Radiyallahu Anhu) ya ce: Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: “Wanda ya yi jinkiri ga wanda yake cikin ƙunci ko ya yafe masa abinda yake binsa, Allah zai sanya shi a cikin inuwarsa” (Muslim: 3014). 

SADAKA TANA KAWAR DA MUSIBA 

An karɓo daga Mu’awiyya Ibn Haidah (Radiyallahu Anhu) ya ce: Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: “Haƙiƙa yin sadaka a asirce tana gusar da fushin Ubangiji, Kuma a haƙiƙan ayyukan alhairi suna kawar da mummUnar faɗuwa”(Musibu da Asarori) Ɗabarani 951, Sahihul Jami’il Sagir (3759).

MU YI ALHAIRI, MU GUJI ROWA 

An Karbo daga Abu Hurairata (Radiyallahu Anhu) ya ce: Haƙiƙa Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: “Kullum da safe waɗansu Mala’iku biyu suna sakkowa, sai ɗayansu ya ce: “Ya Allah ka mayarwa da mai bayarwa abinda ya bayar, ɗayan kuma sai ya ce: “Ya Allah kawo asara ga mai hanawa (Marowaci) (Bukahri 1442, Muslim 1010). 

FALALAR SADAKAR MAI ƘARAMIN ƘARFI 

An karɓo daga Abu Huraira (Radiyallahu Anhu) ya ce: “Haƙiƙa Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) yace: “Sadakar dirhami ɗaya ta rigayi sadaka dirhami dubu ɗari” Sai wani mutum ya ce: Kamar yaya Manzon Allah? Sai ya ce: 

“Mutum ne yana da dukiya mai yawan gaske, sai ya tsakuro dubu ɗari ya bayar sadaka, sai kuma wani dirhami biyu ne kaɗai da shi. Sai ya yi sadaka da dirhami ɗaya” (Nasa’I Ibn Khuzaimah,) (Sahihul Targib 875) 

FALALAR CIYARWA SHAYARWA DA TUFATARWA 

An karɓo daga Abdullahi ɗan Amr ɗan As (Radiyallahu Anhu) cewa: Wani mutum ya tanbayi Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) cewa: Wane musulunci ne mafi alkahairi? Sai ya ce: “Ka ciyar da abinci, ka yi sallama ga wanda ka sani da wanda baka sani ba” (Bukhari 12, Muslim39). 

Domin karanta Neman Aure Bisa Koyarwar Musulunci Danna nan

An karɓo daga Abu Sa’id Alhkudiri (Radiyallahu Anhu) ya ce: Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) yace: “Dukkan mutumin da ya ciyar da mumini mayunwanci, Allah zai ciyar da shi ‘ya’ yan itacen Aljanna, kuma duk mumini da ya shayar da mumini da yake cikin ƙishirwa Allah zai shayar da shi rufaffen ruwa garai-garai, kuma duk muminin da ya tufatar da mumini matsiraici, Allah zai tufatar da shi kayan ado ranar alƙiyama.” (Abu Dawud, Tirmizi, Hadisi ne mai rauni Da’iful jami’i: 2249).

NAFILOLIN AIKIN HAJJI 

Kamar yadda aka sani, aikin Hajji rukuni ne na musulunci ga wanda ya ke da iko. 

Malamai sun yi saɓani dangane da matsayin Umara shin farilla ce ko nafila? Malaman Mazahabar Hanafiya da Malikiyya suna ganin Umara ba wajibi ba ce , yayin, da Malaman Mazahabobin Shafi’ iyya da Hambaliyya da zahiriyya suna ganin Umar wajibi ce kamar aikin Hajji. 

Don karanta Ma’anar Aure danna koren rubutu

Kowane ɓangare suna da hujjojinsu da suka dogara da su a ayoyin Ƙur’ani da hadisai, waɗanda suna nan cikin littattafan fiƙhu1. Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: “Ku jeranta hajji da Umara saboda jeranta su yana kore zunubai da talauci kamar yadda ƙira yake kawar da tsatsar ƙarfe.”(Tirmizi 738, Nasa’I 2585.) 

Wannan hadisin yana nuna cewa yin Umara bayan aikin hajji akai-akai yana maganin talauci, yana kankare zunubai. 

FALALAR YIN UMARA A WATAN RAMADAN 

An karɓo daga Abdullahi Ibn Abbas (Radiyallahu Anhu) ya ce: “Yin umara a watan Ramadan dai-dai da ladan aikin hajji ne, ko kuma dai-dai da ladan aikin hajji tare da ni yake”.(Bukhari 1764, Muslim !69). 

FALALAR SHAN RUWAN ZAMZAM 

An karɓo daga jabir (Radiyallahu Anhu) ya ce: Haƙiƙa Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce:”Duk buƙatar da aka sha ruwan zamzam saboda ita, Allah zai biya wannan buƙatar (Sahihin hadisi ne duba sahihul Jami’i 5502). 

Duba babin aikin Hajji a littattafan “Al-Muhalla na Ibn Hazm, Bidayatul Mujahid na Ibn Rushd da sauransu. hadisi ne duba sahihul Jami’i 5502).

Abdullahi Ibn Abbas (Radiyallahu Anhu) ya kasance idan zai sha ruwan zamzam yana karanta wannan addu’ar: Allahuma inni as’aluka ilman nafi’an wa rizƙan wasi’an, wa shifa’an min kulli da’in”. Hakim ne ya ruwaito.

Domin Karanta Cikekken Littafin Danna nan

labarin da ya wuceDalilan Wajabcin Azumin Ramadan
Labarin na GabaFalalar Ciyarwa Shayarwa Da Tufatarwa