Haƙiƙa ba mace kidahuma, kamar matar da duhun kai ya sa ta yin gaba da kishiyarta, domin kuwa ko ga ɗabi’ar zaman tare, babu dacewa mutum ya mayar da abokin zamansa abokin gabarsa.
Ballantana kuma idan an koma ga dalilai na Shari’a ai ƙazantar hakan ta isa.
Duhun kan matar da take yin gaba da kishiyarta, yana kai ta ga munana ladabi ga Allah da Manzonsa, sannan kuma ya sa ta cutar mijinta, da ma ita kanta.
Da farko, Allah (Subhanahu wata’ala) da ya isa da kowa da komai, shi ne ya hallata wa maza su auri fiye da mace ɗaya, idan suna da halin yin hakan inda ya ce:
Ma’ana “Ku auri abin da ya yi muku daɗi daga mata (da aka halatta muku) biyu-biyu da uku-uku da hudu-hudu”.
Don karanta Ma’anar Aure danna koren rubutu
To yanzu don Allah ‘yan uwa, ina ladabi ga Allah a tare da matar da take yin gaba da kishiyarta, alhali kuwa kamar yadda Allah ya hallata a zauna da ita, haka ya halatta a zauna da kishiyarta.
Sannan kuma Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: “ku auri mata irin haihuwa, waɗanda kuke son su, su ma kuma suke son ku. Haƙiƙa ranar alƙiyama zan yi alfahari a kan sauran al’umma da yawanku”.
Ya ‘yan uwa yanzu don Allah ba munana ladabi ba ne ga Annabi da kuma wannan Magana tasa? Idan ya zama ana gaba da wadda ta dalilinta za a samu ƙarin yawan al’ummar da Annabi tsira da amincin Allah su tabatta a gare shi zai yi alfahari da ita a ranar alƙiyama? Allah dai ya sauwaƙe, amin.
Har wa yau kuma, Imamul Bukhari ya rawaito hadisi da yake ɗauke da cewa, sahabin Annabi Abdullahi ɗan abbbas (Rdiyallahu An hu) ya ce: Mafi alherin wannan al’umma shi ne wanda ya fi yawan mata”. Ma’ana, mai mace biyu yafi mai ɗaya, mai uku yafi mai biyu, mai hudu kuma ya fi mai uku.
Domin karanta Neman Aure Bisa Koyarwar Musulunci Danna nan
To, tun da munji haka ne, ina ƙaunar da mace mai gaba da kishiyarta take yi wa mijinta ta tafi? Ko kuwa ba ta son sa da ci gaba ne, shi ya sa take gaba da wadda zamansa da ita zai ƙara masa matsayi da ɗaukaka a wajen Allah Ta’ala? Ƙari a kan haka kuma, Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: “A tsokar
ɗayanku akwai sadaka”. Ma’ana, saduwar miji da matarsa ibada ce mai lada; tamkar miji ya yi sadaka.
Anya ko ba baƙin ciki matar da take gaba da kishiyarta take yi wa mijinta ba, a game da ladan da zai samu in ya sadu da kishiyarta? To, in ba haka ba, mene ne nata na yin gaba da kishiyarta?
Ga shi shikuma Bukhari da Muslim sun rawaito hadisin da yake cewa,Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: “dayanku ba zai zama mai cikakken Imani ba, har sai ya so wa ɗan’uwansa irin abinda yake so wa kansa na alheri”.
A ta yaya ne, mace mai gaba da kishiyarta za ta zama ta so wa mijinta alherin zamansa da kishiyarta? Kuma ina ƙaunarta wa kishiyarta samun irin alherin da ita ma take samu daga wajen mijin nasu. Kai wannan kidahumanci da yawa yake!
Don karanta Ma’anar Aure danna koren rubutu
Ya ‘yan’uwa don Alah yanzu a nan riba mace mai gaba da kishiyarta ta ci ko kuwa faduwa ta yi? Yanzu wane duhun kai ne ya fi mutum ya yi abin da zai hana
imaninsa cika? Allah dai ya sauwaƙe, amin.
Bayan haka, an karɓo daga Abdullahi ɗan Umar daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: “Mumini da yake cuɗanya da mutane, kuma baya haƙuri da cutarwarsu”. Bukhari ne ya rawaito shi a littafinsa Adabul Mufrad. Haka kuma Tirmizi da Ibn Majah sun rawaito shi.
A nan kuwa duba da wannan Hadisi muna iya cewa, matar da ta kasa haƙurin zama da kishiya, har ta kai ga mayar da kishiyarta tamkar maƙiyi, haƙiƙa ta yi wa kanta asarar ɗimbin alherin da wanda ya cuɗanya da mutane ya kuma yi haƙuri da su yake samu. Allah dai ya tsare mu da duhun kai, amin.
Domin karanta Yadda Za Ki San Kanki Kafin Ki Yi Aure Danna nan
Sannan kuma bugu da ƙari sau da dama matar da gabarta da kishiyarta ta sa mijinta ya saki kishiyarta, tana yi wa kanta maraba ne da cutar ƙanjamau, domin sau tari mazajen da buƙatarsu ta sha’awa ta kere iya wadatuwa da mace ɗaya, suna halartar dandali-dandali da gidajen da matan banza suke taruwa ne, domin biyan buƙatarsu ta sha’awa.
Wanda ko galibi ta nan ne masu irin wannan halayyar suke samo cutar ƙanjamau, daga nan kuma matansu na aure da suke gida su samu daga wajensu. Allah ya kiyashe mu, amin.
Don haka ‘yan’uwa mata sai a yi hatara a kuma san da wa ya halatta a yi zaman gaba.
Ko ya hallata Miji ya yi hira, ko kuma ya shiga ɗakin wata daga cikin matansa ba ranar kwananta ba?
An karɓo hadisi daga Aisha (Radiyalahu An ha) ta ce, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance babu wata rana face sai ya zagaya mu gaba ɗaya, sai ya yi kusa da wacce ya shiga wajenta ya shafa jikinta ba tare da ya biya buƙatar sha’awa da ita ba, har ya isa ga wacce take da kwanan ranar sai ya kwana a wajenta”. Imam Ahmad da Abu Dawud ne suka rawaito.
Bayan haka, cikin bayanan da suka gabata mun ji cewa har zuma Manzo yake tsayawa sha in ya shiga wani ɗakin.
Ashe nan halal ne miji ya zanta da matarsa ba a ranar kwananta ba, kamar yadda ya halatta gare shi ya shiga ɗakinta ta ba shi wani abu ya ci, kuma ya sha.
Domin Karanta Cikekken Littafin Danna nan