Dangogin Waƙafi

0
521

Ana iya yin waƙafi a ɓangarori da dama da suka haɗa da:

Ɓangarorin yaɗa addini da ilmantarwa:

1. Gina masallatai da samar da abubuwan Jin daɗin masallata:

A cikin su waɗanda suka haɗa da rijiyoyi don samun ruwan alwala da sauransu. Ba shakka musulmai magabata sun yi ƙoƙari matuƙa ta yadda suka samar da masallatai daban-daban; tare da ƙawata su da fitilu, da cika su da Alƙur’ani da shimfiɗu, tare da ɗaukar nauyin ɗawainiyar kulawa da su, da biyan albashin masu yi musu hidima; ta hanyar karantarwa da ilmantarwa da kiran sallah da sauransu.

Kaɗan daga cikin misalan waɗannan sun haɗa da abin da masana tarihin Musulunci suka bayyana a litattafansu cewa; yawan masallatan da suke birnin Kurɗubah ta ƙasar Andalus a ƙarni nan a uku bayan Hijira (ƙarni na goma a shekarar Miladiyya) sun kai kimanin ɗari shida. Kowannen su an samar masa duk wani abu da ake buƙata don jin daɗin masu amfani da shi.

Kamar yadda sanannen abu ne cewa har zuwa wannan zamani namu, akwai ragowar irin masallatai daɗaɗɗu; irinsu masallacin Azhar da ke birnin Alkahira da Masjid al-Amawiy dake birnin Dimashk; da Masallacin Kairawan da a halin yanzu yake Tunisiya da sauran ire-irensu a sauran wurare daban-daban a faɗin duniya.

2. Gina makarantu da samar musu da kayan aiki:

Ba shakka tarihin Musulunci cike yake da labarai na waƙafi a ɓangarorin gina makarantu da samar da cikakkun kayan aiki a cikinsu; waɗanda suka haɗa da wuraren kwanan ɗalibai da wuraren hutawar su da lafiyarsu da sauran su. Kaɗan daga cikin misalan waɗannan sun haɗa da abin da aka samo a littattafan tarihi cewa yawan makarantu da aka yi waƙafin su a birnin Skilliya (ƙasar Italiya a wannan a zamani namu); a ƙarni na huɗu shekarar Hijiriyya, wanda yayi daidai da ƙarni na goma sha ɗaya na Miladiyya, sun kai kimanin makarantu ɗari uku; kowacce a cikinsu cike take da ɗalibai a fannoni daban-daban na matakan karatu daban-daban, da jin daɗin na kyautatawa.

Wannan nau’i na makarantu za a gan shi a ko ina a manyan biranen Musulunci irinsu; Makkah da Dimashƙ da Halab da birnin Ƙudus da Bagdad da Alƙahira da Istanbul da kuma sauran garuruwa.

3. Waƙafin ɗakunan karatu da na bincike:

A irin wannan nau’i na waƙafi za ka iske an samar da ɗakunan karatu an kuma cika su da littattafai na fannonin ilmi daban-daban; kamar yadda akan samar musu da ma’aikata ƙwararru da za su rinƙa kulawa da su da suka haɗa da kwararru a fannin fassara da rubutu da kwamiti na amintattu da dai sauransu.

Ɓangaren kula da jin daɗin al’umma

1. Wannan ya haɗa da gina asibitoci da wuraren shan magani:

Haka nan tarihin Musulunci cike yake da labarai na waƙafi a fannin kulawa da lafiya; ta hanyar gina asibitoci da kulawa da ma’aikatansu da samar da cikakkun kayan aiki da bayar da kyakkyawar kulawa ga marasa lafiya. Asibiti na farko da aka gina a tarihin Musulunci shi ne wanda aka gina a zamanin halifancin Walid ɗan Abdul-Malik wanda ya keɓance shi musamman don masu fama da larurar kuturta, aka kuma ɗauki likitoci ƙwararru, aka kuma ware musu albashi.

Bugu da ƙari kuma, hatta su kansu marasa lafiya aka yanka musu kuɗaɗen alawus na kula da su. Waɗansu daga cikin misalai na irin wannan nau’i na waƙafi sun haɗa da asibitin Mustashfa Al ‘adudiy dake birnin Bagdad; wanda aka gina ƙarni na huɗu bayan Hijira (ƙarni na goma sha ɗaya na Miladiyya); da Almustashfa Annuriy dake birnin Dimashk wanda Sultan Nuruddin ya gina a shekara ta 549 bayan Hijira da Almustashfah Almansuriy dake birnin Alƙahirah.

Kuma wani abin ban sha’awa a nan shi ne, tun tsawon wancan lokaci, an samu waɗanda suka yi waƙafi na waɗansu asibitoci na musammman kamar ciwon ido; da na ƙashi, da na fata da cututtukan taɓin kwakwalwa, da sauransu. Kamar yadda kuma aka gina asibitoci aka kuma yi waƙafi da su musamman ga waɗansu makarantu; don amfanin malamansu da ɗalibansu da kuma na talakawa da miskinai.

2. Gina Wurare Na Musamman Don Kulawa Da Gajiyayyu:

Ma’anar gajiyayyu da aka ambata a nan sun haɗa da marayu da ‘yan tsintuwa da nakasassu da makafi; kai har ma da tallakawa gidajen marasa ƙarfi wajen ɗaukar nauyin aurar da ‘ya’yansu da hidimomi masu dangantaka da waɗannan.

3. Samar Da Ruwan Sha Da wurare Kwana Ga Dukkan Masu Buƙata:

Ba shakka addinin Musulunci ya kwaɗaitar da mabiyansa wajen sadaukar da dukiya ta hanyar waƙafi a wannan bangare; haka nan musulmi sun yi namijin ƙoƙari matuƙa wajen aiwatar da wannan umarni; kamar yadda muka gani a baya na sayen rijiya da sayyidina Uthman ya yi, ya kuma sadaukar da ita ga ɗaukacin al ‘umma.

4. Taimakon Talakawa Da Masu Ƙaramin Ƙarfi:

Wannan ɓangare ya shafi sadaukar da amfanin wata dukiya ko kadara ga mabuƙata; kamar yadda sayyidina Umar Allah ya yarda da shi ya yi da gonarsa dake Khaibara, kamar yadda muka gani a baya; marasa lafiya ko talakawa ko matafiya ko ɗaliban ilmi da sauransu.

Domin karanta cikakken bayani a kan Nau’o’in Masu Amfana Da Waƙafi Ko Hubusi danna nan.

Domin karanta cikakken bayani a kan Tarbiyyar Addini danna koren rubutun nan.

Wannan baya nin an ciro shi ne daga Littafin Gudunmawar Waƙafi/Hubusi Da Tasirinsa Wajen Gina Tattalin Arzikin Al’umma; wanda Dr. Sunusi Iguda Ƙ/Nasarawa ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

labarin da ya wuceSadarwa A Waƙar Baka
Labarin na GabaManufofin Waƙafi