Dabarun Yaƙi.

0
1008

Mutum yana daga cikin ƙananan halittun Allah, kuma raunana, marasa buwayayyen ƙarfi,hatta a mahaliccinsa mutum ɗan-tsurut yake in an kwatanta shi da sauran halittu maƙwabtansa, kamar duwatsu da bishiyoyi da raƙuma da jakuna da shanu da sauran manyan dabboni, amma duk da haka sai Allah ya ba shi hankali da dabara, kuma da su ne yake cin galaba a kan manyan halittu waɗanda suka fi ƙarfinsa.

Yana yin haka ne ta hanyar haɗin kai (taron dangi ) da samar da kayan aiki (makamai da aloli) tare da bin matakin na sauƙaƙe wahalhalu. Wato mutum ba ya fitowa shi kaɗai da fararen tafukan hannunsa ya tunkari giwa ko dutse, in ya yi haka, sai a gama da shi! Kamar haka idan mutum ya tsaya shi kaɗai ba tare da waɗansu makari ba, ya fuskanci son zuciya da shaiɗan da rudin duniya, to lallai zai sha mamaki, domin kuwa ba zai kai labari ba. Lallai sai ya yi shiri kuma ya tanadi dabarun yaƙi. Babu shakka bin waɗannan dabaru yana taimakawa ƙwarai, idan a ka gamu da muwafaƙa daga Allah. Daburun su ne kamar haka:
• Harsashin gina al’umma (iyaye).
• Tarbiyyar addini.
• Yanayi mai tsafta.
• Nasiha tsakanin Musulmi.
• Dokoki.

Domin karanta cikakken bayani a kan Harsashin Gina Al’umma (Iyaye) danna nan.

Wannan bayani anciro shi ne daga littafin Ɗan Adam Kamar Yadda Allah Ya ke Son sa wanda M. Aminu Isma’il Sagagi ya wallafa shi Domin karanta cikakken littafi danna nan.

labarin da ya wuceHarsashin Gina Al’umma (Iyaye)
Labarin na GabaDUNIYA MAKARANTA!
Dr. Aminu Isma'il Sagagi
An haifi Dr. Sagagi a Unguwar Sagagi cikin birnin Kano a 1968 Ya yi PhD a IUA Khartoum 2012 Ya yi aikin koyarwa a Makarantar Munazzama Kura. Ya yi koyarwa a Makarantar koyon Sharia ta Malam Aminu Kano. Ya taba rike Mukamin Mai ba wa Gwamna Shawara a kan Ilimi 2009-2011 A yanzu Malami ne a Sashin Nazarin Addinin Musulinci a Jami'ar Bayero.