(1) Samuwar Amincewar Waɗanda za a Ɗaurawa Aure:
A shari’ance, aure ba ya zama zartacce, abin la’akari da shi, sai idan an sami yardar ma’aurata da kuma amincewarsu.
Dalili kuwa faɗar Allah Maɗaukakin sarki: “Ku auri abin da ya kwanta muku a rai daga matan (da suka halatta a gare ku), biyu-biyu ko uku-uku ko kuma hurhuɗu”.
Da kuma hadisin da aka karɓo daga Ukbatu ɗan Amir (Allah ya yarda da shi) ya ce, “Haƙiƙa Annabi ( Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ) ya ce: “Da wani mutum (da zai ɗaurawa aure ) ka yarda in aura maka wance? Sai ya ce: eh (na amince), sannan Annabi ya ce da matar: kin yarda in aura miki wane? Sai ta ce: eh (na yarda), Sai Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ɗaura musu aure”. ( Baihaƙi da Hakim da wasun su ne suka rawaito shi ).
Kuma Abdullahi ɗan Abbas ( Allah ya yarda da shi ) yace: “Haƙiƙa, wata budurwa ta zo wajen Annabi ( Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ) ta ce: Babanta ya ɗaura mata aure ( Da wani ) ba don sonta ba ( nan take) sai Annabi ( Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ) ya ba ta zaɓin idan ta amince da wanda aka aura mata, auren ya ɗauru, idan kuma ba ta son sa, to auren bai ɗauru ba”. ( Ahmad da Abu Dawud da wasun su ne suka rawaito shi).
Sannan an karɓo daga khansa’u ‘yar Khidan ( Allah ya yarda da ita ) Cewa: Mahaifita ya ɗaura mata aure da wani tana bazawara ba don son ta ba, sai ta je ta shaida wa Annabi ( Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ) sai ya ce : “Auren bai ɗauru ba”. ( Bukhari ne ya rawaito shi ).
(2) Waliyyin Matar da za a Aura:
Waliyyi shi ne mutumin da alhakin aurar da mace yake wuyansa, kamar uba, ko madadinsa, ko shugaban Musulmai.
Waliyyi ma sharadi ne daga sharuɗɗan da sai da su aure yake ɗauruwa a Musulunce.
Saboda haka, bai halatta mace ta aurar da mace ba, kamar yadda bai halatta mace ta yi gaban kanta ta aurar da kanta ga wani ba.
An karbo daga Abu Huraira ( Allah ya yarda da shi ) ya ce: “Manzon Allah ( tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ) ya ce : “Mace ba ta aurar da mace, haka kuma mace ba ta aurar da kanta”. ( Ibn Majah ne ya rawaito shi ).
Kuma an karbo daga Ikrima da Abdullahi ɗan Abbas (Allah ya yarda da su) sun ce: “Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: “Babu aure sai da waliyyi”.
Sannan kuma an karbo daga A’isha ( Allah ya yarda da ita ) ta ce: Manzon Allah (Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ) ya ce: “Duk matar da ta yi aure ba da izinin waliyyinta ba, auren ɓatacce ne,. Idan kuma wanda ya aure ta a kan hakan, har ya sadu da ita to, ya ba ta sadakinta, saboda saduwar da ya yi da ita. Idan kuwa mace da waliyyinta suka saɓa, to, shugaban musulmai shi ne waliyyin duk wacce ba ta da waliyyi”. ( Abu Dawuda da Ibn Majah ne suka rawaito shi).
(3) Shaidu:
Su kuwa shaidu su ne, adalan mutanen da suke halartar gurin ɗaurin aure, su kuma kasance a gurin a lokacin da za a ɗaura auren.
A Musulunce, mutane biyu su ne mafi ƙarancin shaidu game da ɗaurin aure. Saboda hadisin da aka karɓo daga Imran ɗan Husaini, da A’isha ( Allah ya yarda dasu ) cewa, Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: ” Babu aure sai da waliyyi da kuma shaidu biyu adalai”. ( Imam Ahmad ne ya rawaito shi ).
Amfanin Samar da Shaidu a Aure:
Yana daga cikin amfanin da samar da shaidu yake da shi:
1. Kawar da zargin zina, ko daduro tsakanin ma’aurata.
2. Hana a kira ‘ya’yan da mutum ya haifa ‘ya’yan zina (shegu).
(4) Sadaki:
Sadaki shi ne dukiyar aure, wacce mace take cancantarsa daga wajen miji ta dalilin aure. Saboda faɗar Allah Maɗaukaki:
“kubawa mata sadakinsu cikin daɗin rai, idan kuma suka sayar muku da wani abu daga cikinsa da sonsu (don kansu), to, ku ci shi (halak malak ) rai kwance”.
Da kuma faɗar Allah maɗaukaki:” To, waɗanda ku ka ji daɗi da su daga cikinsu (mata) ku ba su sadakinsu (cikakke) tilas”.
Sannan kuma Allah cikin hikimarsa ya yi bayinsa bai yi su bai ɗaya ba, don haka ma, da ya wajabta musu bayar da sadaki, sai bai iyakance musu shi ba. Saboda ya dace da mai hali da kuma mai ƙaramin ƙarfi. Kowanne gwargwadon halinsa.
Don haka, a Musulunce ya halatta mutumin da yake da hali ya dunƙule wasu maƙudan kuɗi ya bayar a matsayin sadakin matar da zai aura. Allah Maɗaukaki ya ce : ” Idan ku ka yi nufin musanya wata mace a maimakon wata (da kuka saka) alhali kuwa da kun ba wa dayarsu ( ta farkon ) dukiya mai ɗimbin yawa (a matsayin sadakinta ), to , kada ku karbi komai daga cikinsa, shin kwa karbe shi don zalunci da saɓo mabayyani”.
Sai dai kuma mafi falalar sadaki shi ne wanda bayaninsa ya zo kamar haka:
An karɓo daga Ukbatu ɗan Amir (Allah ya yarda da shi) ya ce: “Manzon Allah (Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) “Ya aura wa wani mutum mace a kan sadakin zobe na ƙarfe”. (Hakim ne yarawaito shi).
Bayan haka kuma, shi sadaki haƙƙi ne na matar da aka aura, kamar dai yadda bayani ya gabata. Saboda haka, bai halatta ba ga waninta ya ci wani abu daga cikinsa, sai dai inda izininta.
To bayan kammalar bayanin waɗannan abubuwa da muka ji, ana so a lokacin da za a gudanar da ɗaurin aure a kwaikwayi Annabi ( Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ) a rigayi ɗaurin auren da gabatar da wannan addu’ar kamar haka:
An karbo daga Abdullahi ɗan Mas’ud ( Allah yayarda dashi ) Yace: Manzon Allah (Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ) ya koya mana yin ” Huɗubar Haja ” a lokacin ɗauren aure. Wato:
“Innal hamdulillahi ta’ala, nahmadhu wanastagiynuhu, wanastagfiruhu, wa na’u’zu billahi min shuruwri anfusina wa min sayyi’a’ti a’a’malina, man yahdihil-llahu fala mudilla-lahu, waman yudlil fala hadiyaya lahu, wa’ashadu an lailahaillallahu wahdahu la shariyka lahu, wa’ashadu anna muhammadan abduhuwarasuluhu”.
“Ya ayyuhal lazina a’manuttaƙuwllaha haƙƙa tuƙatuhi wala tamutunna illa wa antum muslimun (Al-i-mran, aya ta (102)
Ya ayyuhannasu-ttaƙuw rabbakumullazhiy kalaƙakum min nafsin wahida wakalaƙa minha zaujaha wabassa minhuma rajalan kasiran wa nisa’a’wattaƙuwllahal lazhiy tasa’a’luna bihi wal’arhama innallaha kana alaikum raƙiyba” (An nisa’i aya (1)
“Ya ayyuhal-lazhina ‘a’manuttaƙuw-llaha wa ƙulu ƙaulan sadhidhan yuslih lakum a’a’malakum wa yagfir lakum zhunubakum waman yuɗi’illaha wa rasuluhu faƙad faza fauzan a’zhima (Al Ahzab aya,
Abu Dawud, da Nisa’i da wasunsu ne suka rawaito shi.
Sannan kuma ya halatta bayan gama ɗaura aure, ranar a kai amarya gidan miji, a buga dundufa domin sanar da aure da kuma faranta ran ango. Amma bai halatta ayi dauraba.
Ranar Haɗuwar Ango Da Amarya:
A Musulunce ana so ranar da ango ya fara haɗuwa da amaryarsa ko kuma ranar da aka kawo wa ango matarsa gidansa, ya yi ƙoƙarin yin waɗannan abubuwa masu zuwa kamar haka:
(1) Ango ya jagoranci matarsa su yi sallah raka’a biyu- nafila don miƙa godiyarsa ga Allah da ya cika musu burinsu kamar yadda Ibn Abi Shaiba ya rawaito.
(2) Ya ɗora hannunsa a kan goshin matarsa, wato ya karanta ya riƙe, sannan kuma ya karanta wannan addu’a kamar haka:” Ya Allah ina roƙon ka alherin wannan mata da alherin da ka halicceta a kansa, kuma ina neman tsarin ka daga sharrinta da sharrin abin da ka halicce ta a kansa”. ( Bukhari a cikin littafinsa da Abu Dawuda da Ibn Majah da wasunsu ne suka rawaito shi ).
(3) Gabatarwa da amarya wani ɗan abin kusa da baka, kamar yadda Annabi (Tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ) ya yi wa matarsa A’isha (Allah ya yarda da ita ).
(4) Goge baki kafin kwantawa da amarya, domin kawar da wani hamami, ko wari da ka iya tashi daga cikin baki. Kamar yadda aka samu Muslim da Abu Awana sun rawaito Annabi (Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ) ya yi haka.
(5) Yin addu’ar saduwa da mace, kafin fara saduwa da ita. Addu’ar kuwa ita ce: “Ya Allah ka nesan ta ni daga shaiɗan ka kuma nesan ta shidan daga abin da ka azurta ni da shi”.
Annabi (Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ) ya ce: Idan Allah ya hukunta wa miji da matarsa samun ɗa a saduwar da suka karanta wannan addu’ar, to, shaiɗan ba zai cutar da ɗan da suka samu ba har abada”. (Bukhari da Muslim da wasunsu ne suka rawaito shi ).
(6) Yin walima da abin da Allah ya hore, bayan tarewa da saduwa da amarya. Saboda aiwatarwar Annabi da kuma umarnin da ya yi na ayi walima.
Sannan kuma idan za a kira jama’a walima, to a yi kokarin ganin an tara waɗanda suke mabuƙata, saboda Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ) yana cewa: “Mafi sharrin abinci walima, wanda ake kiran (ko gayyatar) mawadata a ƙyale mabuƙata “. ( wato a ki gayyatarsu ). ( Malik da Bukhari da Muslim da wasunsu ne suka rawaito shi ).
Daga lokacin da Allah ya hukunta wa Musulmi aurar wata mace, ko kuma ya hukunta wa Musulma auren wani Musulmi, to ya zamar musu lallai su san cewa, a musulunce akwai wasu nauye-nauye da suke tattare da rayuwar da zasu fuskanta ta zaman aure, wadanda suka sha bamban dana irin rayuwar da suka faro a baya ta zaman kaɗaici.
Domin karanta cikakken bayani a kan Nauye- Nauyen Rayuwar Aure danna koren rubutun nan.
Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Nagartacciyar Rayuwar Aure wanda Abubakar Abbas ya wallafa shi domin karanta cikakken littafin danna koren rubutun nan.