Category: ILIMIN TARIHI

  • Auren Annabi SAW Da Nana Aisha

    Auren Annabi SAW Da Nana Aisha

    Bayan an ɗaura auren Sayyada Saudatu da wata ɗaya sai aka ɗaura auren Nana Aisha ‘yar abokinsa Sayyadina Abubakar As-Sadik a lokacin shekarunta bakwai (7), amma Annabi Muhammad (Sallallahu alaihi wasallam) bai taɓa auren mace budurwa ba sai ita, daga Imam Bukhari a cikin Manaƙibul Ansar lamba ta (3,894), musannadi Ahmad (10/25.827), da dai sauransu.

    Falalar ta da darajar ta

    1. Zagin Nana Aisha kafiri ci ne kai tsaye, saboda Allah ya hana zagin ta kamar yadda suratul Nur daga kan aya ta 10-20 suka nuna.

    2. Haka kuma ita kaɗai ce wacce annabi yake wanka tare da ita, sannan kuma idan suna tare da annabi wahayi yana sauka.

    3. Ita ce wacce ta taɓa ganin mala’ika Jibrilu a fili.

    4. Nana Aisha an haife ta tsarkakkiya daga mahaifin ta tsarkakke.

    5. Ita ce wacce aka karɓi ran annabi yana hannu ta.

    6. A ɗakin Nana Aisha aka rufe annabi (sallallahu alaihi wasallam) da sayyadina Umar da sayyadina Abubakar.

    7. Mai gudun duniya ce, saboda akwai wata rana wata mace ta zo gidan ta tana bara sai kawai ta ɗauki gurasar ta ba ta baki ɗaya.

    8. Ta ruwaito hadisai guda dubu biyu da goma (2,010), wanda imamul Bukhari da Muslim sun haɗu akan hadisai guda ɗari da saba`in da huɗu (174), sannan kuma Bukhari ya ruwaito hadisai hamsin da huɗu(54) nata, wanda Muslim bai ruwaito su ba, haka kuma Muslim ya ruwaito hadisai sittin da takwas (68) wanda Bukhari bai ruwaito ba.

    9. Nana Aisha ta san ilimin fiƙihu da ilimin adab (waƙa) da ansabu na larabawa.

    Sannan kuma Nana Aisha ta rasu a shekara ta hamsin da da bakwai ko da takwas ko da tara, amma kuma ta rasu ne a ranar talata da daddare a ranar goma sha bakwai (17) ga watan Ramadan, haka kuma a lokacin da ta rasu tana da shekara hamsin da bakwai (57) a duniya, an binne ta a baƙi`ul garƙadi, sannan kuma sayyadina Abu-hurarira shi ne wanda ya yi ma ta sallah, saboda a lokacin wanda yake kula da garin makka ya yi tafiya shi ne Marwana ɗan Hakim.

    Domin karanta Sunayen Annabi SAW danna nan

    Edita; Rumasa’u M. Kallamu

  • Auren Sayyadi Abdullahi Da Sayyada Aminatu

    Auren Sayyadi Abdullahi Da Sayyada Aminatu

    Abdullahi ɗan Abdulmunaf shi ne mafi soyuwa a gurin Mahaifinsa, ya auri Aminatu ‘yar Wahabu ‘yar Abdulmanaf ‘yar Zuhra ‘yar Kilabu, lokacin yana ɗan shekara goma Sha-takwas (18) a duniya.

    A lokacin da Abdullahi ya auri Aminatu ita ce mafi fifiko a cikin matan zamanin a cikin ƙabila Ƙuraishawa da dangantaka mai kyau, yayin da Abdullahi ya shige ta, sai Allah (Subhanahu wata’ala) ya ba ta rabo na manzon Allah (Sallallahu alaihi wasallam), da wata biyu, sai mahaifinsa bai jima a duniya ba, ya yi wafati aka rufe shi a garin Madinah a gurin ‘yan uwansa Banu-Aɗiyyu bin Najar. A wannan lokacin ya kasance ya tafi kasuwanci zuwa Sham (Siriya), sai Ajalinsa riske shi a garin Madinah a kan hanyarsa ta dawowa gida.

    Yayin da lokacin haihuwar Aminatu ya yi, sai ta haifi annabi Muhammad (Sallallahu alaihi wasallam), an yi bushara da haihuwar wannan babban abin halitta, wanda ya yi dai-dai da ranar litinin, tara ga watan rabi’ul- auwal (Nurul yaƙin shafi na 8) ko kuma goma sha biyu ga watan rabbiyul-Auwal wanda bai yi dai-dai da ashirin ga watan Afrilu ba, shekara ta ɗari da saba’in da ɗaya (571) miladiyya, wanda ya yi dai-dai da shekarar farko ta giwaye.

    Daga ƙarshe, aka sanya masa suna Muhammad, wanda ya ba Labarawa mamaki sosai, saboda a lokacin babu wani mutum mai irin sunansa a zamanin, Saboda Allah (Subhanahu wata’ala) ya nuna matsayinsa ga halittunsa, da dai sauransu.

    Sannan a lamba ta huɗu (4), Yace; “Ummul-Aimana ta raine shi, to a nan ƙa’ida ta raino ga wacce ta ke so ɗanta ya zamo mai hazaƙa, to dole a kanta ta kiyaye irin abincin da za ta ci sannan ta dinga cin halal, sannan ta dinga kula da ɗanta shigarsa da fitarsa haɗi da mu’amala ta gari, Saboda ɗabi’a tana kwaikwayen ɗabi’a ne.

    Danna nan don karanta  Yadda Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasallam) Yake Shan Ruwa

    Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu

  • Auren Annabi SAW Da Nana Khadija

    Auren Annabi SAW Da Nana Khadija

    1. Bayan da wowar su da wata biyu daga tafiyarsu ta biyu zuwa Sham (ita ce Siriya a yanzu) ya auri shugaba Khadija (ita ce wadda ta nemi auransa da kanta).

    2. Shekarunta sun kasance arba’in (40) na daga rayuwarta, shi kuma (annabi) shekarunsa ashirin da biyar (25) na daga rayuwarsa.

    3. Ta kasance kafin ta aure shi (annabi) ta auri Abi-Halata, haƙiƙa ya mutu yana da ɗa guda ɗaya (1), sunan ɗan Halata.

    4. Haƙiƙa ta zauna tare da annabi, shekara ashirin da biyar (25), bai auri wata macen ba bayanta, har sai da ta rasu.

    Sharhi;

    Yayin da ya shiga garin Makkah, sai shugaba Khadija ta ga ya dawo mata da riba mai yawan gaske, sai ta yi farin ciki da ganin haka, sai ta aika masa tana neman izinin auransa idan zai amince, daman ita shugaba Khadija ta samu labarin sa, sai ta yi yunƙuri ta aure shi, amma ba ta samu ikon yi masa magana ba, sai can ta yi wani tunani, tace eh, to, tunda ina ɗaukar mutane kasuwanci, sannan kuma shi mutum ne mai sauƙin kai, mai zai sa ba zan ɗauke shi aikin ba, idan ya so daga baya sai na sanar da shi abin yake cikin zuciyata.

    Hakan kuwa aka yi, saboda albarkar da ke tattare da annabin ne da kuma irin gaskiyarsa da riƙon amanarsa. Waɗannan abubuwa dai sun faranta wa Khadijah rai ƙwarai da gaske da kuma ƙaunar annabi.

    Sai ko ta ɗauke shi aiki, bayan ya yi shirin tafiya kasuwanci, sai ta nemi ɗan aikinta mai suna Maisara, ta sanar da shi cewa, tana so za ta haɗa su kasuwanci da wannan babban mutum, amma abin da nake so da kai kawai shi ne, ka lura duk abin da yake yi na ɗabi’unsa haɗi da mu’amalarsa baki ɗaya.

    Sannan aka ɗora kayan kasuwanci akan dabbobi, sai suka kama hanya suka tafi, har suka tafi suka dawo, sai ta haɗawa annabi (Sallallahu alaihi wasallam) liyafa mai kyau, ta samar masa da waje mai kyau, ta ajiye masa kaya, sai ta kira Maisara take tambayarsa game da halayensa, sai Maisara yace, a gaskiya tun da muke tafiya kasuwanci, ban taɓa ganin mutum irin wannan ba ga tausayi, ga haƙuri, ga riƙon amana ga gaskiya, ga sanyin hali, ga kunya, da dai sauransu sai ta ji ya kamata ta sanar da shi abin da yake cikin ran ta.

    Saboda Hausawa sun ce: “A bari ya huce shi ke kawo rabon wani” sai kuwa ta fara tunanin yadda za ta sanar da annabi (Sallallahu alaihi wasallam), saboda ta san annabi Muhammad (Sallallahu alaihi wasallam) Balarabe ne, Sannan kuma ka san Larabawa farare ne su, kuma annabi Yusuf (Alaihis-salam) wanda muka ji labarinsa haɗi da abubuwan da suka faru a tsakaninsa da matan wannan zamanin duk da haka shi fa rabin kyau ɗin manzon Allah (Sallallahu alaihi wasallam) aka ba shi, amma ga abin da yaka faru da shi a wancan zamanin.

    Sai shugaba Khadija ta ga fuskarsa ta fi farar audiga, ta zarce madara irin ta ruga, Sannan da girman da kyawun tsaga, fuskarsa tana walwali, ta fi walƙiya haskakawa, ga haƙoransa fes ko tar sun fi wata haskakawa, goshinsa ya yi lub-lub baƙi sitil ga sansti, idan ya yi murmushi haske ne ke fitowa daga bakinsa saboda kyawunsa da kuma girmansa a wajen Allah (Subhanahu wata`ala).

    Sannan gashin kansa kamar gashin gada, ga idanunsa gada-gada zancensa akwai da fa’ida daɗin ƙamshin sa wa zai kwada, kowa na son sa cikin mutane, Sannan ga lallausan lafazi wanda ke ratsa zuciyar mutane ko ƙarfe ne a cikin zukatan mutane sai ya narke, saboda jin wannan lallausar hamshaƙiyar muryarsa.

    Bugu da ƙari zuciyarsa tar ce ko fes kuma ga haƙuri da hankali a gunsa gami da nutsuwa tamkar a ce mutane su yi murɗiya, saurin fushi ko faɗa ko ha’inci babu guda a gunsa gwanin gaskiya, sai shugaba Khadija ta ji ta gani, sannan ta tsuduma a cikin kogin madarar ƙaunarsa, sai ta samu Baffanta Amru ɗan Asdu ta ba shi labarin duk abin da yake tafe da ita, sannan ya samu Baffan annabi (Sallallahu alaihi wasallam) daga ƙarshe sai annabi ya amince zai aure ta.

    Haka kuma a wata faɗar an ce lokacin da annabi ya dawo daga kasuwanci, sai Maisara ya sanar da ita cewa sun dawo, sai sayyada Khadija ta saurari shigowar annabi, bayan ya shigo cikin gidan ta ga ya dawo mata da riba mai albarka, ashe lokacin da yake yi ma ta bayanin yadda kasuwancin nasu ya kasance, ita ko tsayawa ta yi tana kallon sa yadda yake yi ma ta jawabi cikin nutsuwa da yadda yake magana haɗi da sunkuyar da kan sa ƙasa tare da lallausar muryarsa mai ɗankaran daɗi, wadda dole mutum ya saurara, idan kuma ya yi shiru sai kwarjinin sa ya mamaye zuciyar mutum, sai ko sayyada Khadija ta shiga cikin wani hali na faɗawa cikin kogin zumuɗin ƙaunar sa (sallallahu alaihi wasallam), amma kuma sai ta kasa faɗa masa.

    Daga ƙarshe sai sayyadina Hamza da Abdul-Muɗallib suka tafi gidan su Nana Khadija aka nemo waliyyin ta (a lokacin ma mahaifinta ya rasu), sai Abdulmuɗallib ya sanar da shi (waliyyin na ta) abin yake tafe da su, sannan sai ya tashi ya yi huɗuba yake cewa “ duk wanda aka haɗa shi annabi akan ma’auni, to sai ɗan mu ya rinjaye shi, sannan kuma ba shi da dukiya a hannun sa, ita ko dukiya inuwa ce yanzu za ka iya samun ta zuwa anjima kuma a rasa ta”.

    Sai aka amince aka ɗaura musu aure da annabi (Sallallahu alaihi wasallam), sai aka yi shagalin aure, can sai ga wata tsohuwar mace nan da tumaki arba’in ashe Halimatus-Sadiya ce ta kawo su ta ce a yi shagalin bikin ɗan ta, saboda haka malamai suka ce babu wata mace wacce ta kai Nana Khadija zaɓin miji.

    Saboda haka a lokacin da annabi ya auri Nana Khadija sai ta share masa baƙin cikin da yake cikin zuciyarsa na tunanin rasuwar mahaifiyar sa da Baffan sa, sannan kuma ita ce wacce ta auri annabi tun kafin ya zama annabi.

    Haka kuma Shugaba Khadijah ta kasance kafin ta auri annabi (Sallallahu alaihi wasallam) ta auri wasu mazajen guda daga cikinsu akwai Abu-Halata shi ne wanda Allah (Subhanahu wata’ala) ya ba su ikon samun rabo na da guda miji guda ɗaya sunansa Halata. Sannan kuma ta zauna tare da annabi (Sallallahu alaihi wasallam) shekara shekara ashirn da biyar (25) saboda haka idan muka haɗa da shekarunsa sa aure shi ya kama shekarun Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) Hamsi (50) kafin shugaba Khadija ta yi Wafati ita kuma shekarun sittin da biyar (65) ko hamsin da uku (53) ko hamsin (50):

    Saboda haka Shugaba Khadija ta yi Wafati a shekara ta goma bayan annabta, amma annabi (Sallallahu alaihi wasallam) bai taɓa auren wata mace ba, har sai da ta yi wafati sannan ta haifa masa ‘ya’ya mata guda huɗu (4), wanda Babbarsu ita ce Zainab, sai Ruƙayya, sai Ummul-khursum sai Nana Faɗima wanda annabi Muhammad (Sallallahu alaihi wasallam) yasa mata Fatima, Saboda sunan Mahaifiyar Mahaifinsa ne Abddullahi ɗan Abdul-Muɗallib.

    Sannan dukkansu sun rayu kuma sun yi aure wacce sayyadina Usman Bin Affan ya auri guda biyu (2), daga cikinsu akwai sayyada Ruƙayya, bayan ta rasu sai ya auri sayyada Ummul-khursum, sai sirikin annabi (Sallallahu alaihi wasallam), na biyu shi ne Abul-as ɗan Rabi’a wanda ya auri sayyada Zainab wacce ta haifi ‘ya’ya daga cikin su akwai wacce ake kira da Umaima, wacce wani lokaci annabi Muhammad (Sallallahu alaihi wasallam) yake fitowa da ita yake riƙe ta yana Sallah da ita, sai sirikin annabi (Sallallahu alaihi wasallam) na uku (3) shi ne sayyadina Aliyu ɗan Abu-ɗalib (Karramallahu Wajjahahu) wanda ya auri sayyada Fatima , sannan kuma sayyada Nana Fatima tana da sunaye da yawa kamar su; Zakiyya, Batula, Ma’asuma, Alawiyya, da dai sauransu.

    Saboda haka menene dalilin da yasa Khadija ta zauna Annabi Muhammad (Sallallahu alaihi wasallam) shekara ashirin da biyar (25), kuma annabi (Sallallahu alaihi wasallam) bai taɓa auren wata macen ba har sai da ta rasu? Maganar gaskiya dalilan suna da yawan gaske, amma dai sayyada Khadija mace mai yawan ibada da haƙuri da juriya, sannan kuma ta iya zamantakewar auratayya haɗi da sanin kalaman da za su sanyayawa annabi zuciya.

    Bayan annabi Muhammad (Sallallahu alaihi wasallam) ya fito daga shinge (wata kariya ce da ya shiga, a lokacin mutanen Najrana suka Zo wajen annabi (Sallallahu alaihi wasallam) su ashirin (20) ko kusa da ashirin sai annabi (Sallallahu alaihi wasallam) ya karanta musu Alƙur’ani, suka yi Imani da shi) kafin Hijira daga Makkah zuwa Madinah da shekaru uku (3) a shekara ta hamsin).

    Sai Sayyada Khadija ta rasu ‘yar Khuwailid matar annabi (Sallallahu alaihi wasallam), ya kasance yana yawan tunawa da ita saboda Imam Bukhari (3,818), Babi na (20) yace,; “Annabi ya auri sayyada Khadija yana daga fifikonta daga Hadisin da aka ruwaito daga Nana A’isha tace: ‘’ban taɓa kishi da wata mace ba daga cikin matan annabi (Sallallahu alaihi wasallam), sai sayyada Khadija, saboda irin abubuwan da na gani da irin son da annabi (Sallallahu alaihi wasallam) yake yi mata.

    Sai dai da na ga annabi (Sallallahu alaihi wasallam) ya cika yawan ambaton ta har ma (bayan ta rasu) yana yanka akuya (fata) sai ya ba ƙawayenta da ‘yan uwanta (Sayyada Khadija), sannan annabi (Sallallahu alaihi wasallam) ya kasance wani lokaci yana cewa, kamar bai taɓa ganin wata ‘ya mace a wannan duniyar kamar sayyada Khadija ba, yace: ita (sayyada Khadija) ta kasance kaza da kaza haka kuma a tare da ni da ita akwai ‘ya’ya (Nurul Yaƙin shafi na 53).

    Danna nan don karanta Sunayen Annabi Muhammad (S.A.W)

    Edita; Rumasa’u M. kallamu

  • Tarihin Marigayi Dakta Murtala Kudan

    Tarihin Marigayi Dakta Murtala Kudan

    An haifi Dr. Murtala Shehu a garin Kudan a ranar 01/01/1960, ya yi karatun allo, sannan kuma ya yi karatu a makarantar firamare wacce take Kudan, haka kuma ya yi karatun gaba da firamare, kazalika kuma ya yi karatu a jami’ar Ahmadu Bello ɓangaran ilimin lafiya (wato CHO) a 1982. Sunan mahaifinsa shi ne Alhaji Shehu Turaki, mahaifiyar sa ita ce Hajiya Khadija mai Gauda.

    Sannan kuma ya yi aure ya haifi ‘ya’ya maza da mata kamar haka;

    1. Usman

    2. Abduljalali

    3. Ahmad

    4. Abdullahi

    5. Sani

    6. Isah

    7. Yahaya

    8. Abdulhadi

    9. Mubarak

    10. Hauwa

    11. Amina

    12. Bilkisu

    13. Shafa’atu

    14. Suwaiba

    15. Maimuna

    16. Khadija

    17. Salima

    18. Halima

    19. Na’ima

    20. Asiya

    21. Fatima

    22. Nusaiba

    Sannan kuma ya buɗe asibiti a garin Kudan a shekara ta 1982 mai suna “Nakowa nursing and maternity home Kudan” (yau kimanin shekara 39 ke nan) wanda dubbunan mutane suke amfani da shi (asibitin).

    Domin karanta yadda ilimi zai zama hasken rayuwarka danna nan

    Edita; Rumasa’u M. Kallamu

  • Tarihin Mawaƙi Ashir San Kudan

    Tarihin Mawaƙi Ashir San Kudan

    An haifi Ashiru Hamisu a garin Kudan a gidan Tattibu, ɗa ne ga Malam Adamu wanda aka fi sani da Malam Bala, sunan mahaifiyar sa ita ce Maryam Yusha’u wacce aka fi sani da suna Dogora an haife ta a ƙofar Arewa gidan Malam Tanko, ta rasu a shekara ta 2019. Ashiru an fi sanin sa da suna Ashir San, wanda yake amfani da sunan yayan sa, wato Sani, wanda shi ne babban yayan sa.

    Ashir San ya yi karatun allo a hannun Malam Abdullahi, wanda shi ne ƙanin mahaifiyar sa, tun yana karatun allo ya fara tunanin yadda zai rubuta waƙa, saboda yawan jin wani shiri da yake yi a Kano a Freedom Radio, wato shirin Taskira sai ya samu takarda ya fara rubuta waƙa, amma da ajami (rubutun harafan larabci) sai mutane suke yi masa dariya, saboda su ba su taɓa ganin inda aka rubuta waƙa da ajami a lokacin su ba.

    Bayan ya dawo gida daga makarantar allo, sai ya shiga makarantar zamani (boko) a inda har yanzu yana fafatawa. Sannan kuma Allah ya yi masa baiwar waƙa har muryar Naziru sarkin waƙa yanayi, wanda ya fara koyo masa waƙa shi ne Shu`aibu army na ƙofar Arewa Kudan.

    A fannin waƙa har sai da ta kai an kulle shi a police station har sai ya yi kwana uku a can, saboda wata waƙa da ya yi mai suna Kutara-kutara ɓarayi, daga ƙarshe sai uban gidan sa wato Salisu Ten-ten ya fito da shi, tun lokacin da aka kama shi sai ya ƙara samun magoya baya sosai, yana fitowa sai ya yi wata waƙa mai suna kainuwa dashen Allah, domin nuna godiyar sa ga mutanan sa suka ba shi gudunmawar su a lokacin da aka kulle shi, a ƙarshe kuma ya yi waƙoƙi da dama ga kaɗan daga cikin waƙoƙinsa;

    1. Duniya .

    2. Ita gaskiya.

    3. Nusaiba.

    4. Ashir San Salisu M. Rana.

    5. Yayyafin kuɗi.

    6. Kainuwa dashen Allah.

    7. Ku tara ɓarayi.

    8. Sarkin dole.

    9. Tinjim.

    10. Mazurai.

    11. Sarkin Zazzau.

    12. Fatima.

    13. Baƙar masarauta.

    (Mun samu wannan bayani ne daga bakin Ashir San wanda ya turo min ta waya ta a ranar Talata 13/06/2020 a misalin ƙarfe 5;03 na yamma).

    Danna nan don karanta ƙa’idoji sha shida na samun nasara a rayuwa

    Edita; Rumasa’u M. Kallamu

  • Tarihin Mawaƙi Labaran Adam Kudan

    Tarihin Mawaƙi Labaran Adam Kudan

    An haifi Labaran Adamu Shu’aibu a ƙofar Arewa Gidan Malam Tanko Kudan, a Ƙaramar Hukumar Kudan jihar Kaduna, ya fara karatun allo a wajen Alaramma Aliyu Labaran Ƙofar Arewa Kudan, sai kuma ya wuce jihar Kano wajen Alaramma Hamisu wanda yake  Ƙaramar Hukumar Nassarawa Tudun Murtala a wannan makarantar ne ya samu damar sauke Alƙur`ani mai girma, sai kuma ya koma gida ya fara karatun littattafai a wajen malam Magaji na-umma wanda yake ƙofar Arewa, ya yi aure yana da ‘ya mace mai suna Nazifa, amma kuma Allah ya yi wa matarsa  ta farko rasuwa bayan ta haifa masa waccan ɗiyar.

    Bayan waɗansu lokuta ne sai kuma ya dawo jihar Kano ya kama harkar kasuwanci a ƙaramar hukumar Kumbotso jihar Kano. Sai kuma ya ci gaba da karatun addini a wajen marigayi Malam Adamu Azare limamin Juma’a na Panshekara da kuma Alaramma Misbahu Tsaure. Sannan kuma ya yi karatun boko a Yakubu firamare school wacce take jihar Kaduna a shekara 2001-2007, ya yi karatu a Annur Institute for Islamic education Shahuci a shekara ta 2011, yana yin waƙar bege da waƙar siyasa da dama ga kaɗan daga cikin su;

    1. Gari mai albarka (bege)

    2. Nana Aminatu (bege)

    3. Hajiya Mariya (waƙa ga mahaifiyar Ɗangote)

    4. Farin gani Kumbotso (waƙar siyasa ga Sadau)

    5. Isah Ashiru  (waƙar siyasa ga Rt. Hon. Isah Ashiru Kudan)

    6. Mudassir (waƙar siyasa ga Ɗanmajalisa Mudassir) da dai sauran su.

    (Mun samu wannan bayani ne daga Labaran Adamu wanda ya rubuto min a ranar Laraba 24/06/2020 da misalin ƙarfe 11;30 na safe).

    Domin karanta tarihin Dakta Alhaji Gambo Kudan danna nan

    Edita; Rumasa’u M. Kallamu

  • Tarihin Marigayi Nuhu Baushe Kudan

    Tarihin Marigayi Nuhu Baushe Kudan

    An haife shi a garin Kudan, sunan mahaifinsa shi ne malam Bala, mahaifiyar sa kuma Hassana, ya shahara wajen iya harbi, wanda waɗansu mutane suka ce tun da suke, ba su taɓa ganin ya auna ko ya saita wani abu ba.

    Amma kuma ya ƙasa bugo abin, wanda hatta ma maganin bindiga an sha kawo su wajen sa, amma da ya saita, sai kawai ka ji bindigar ta tashi, kamar yadda muka tattauna da ‘ya’yansa (Suleman da Shitu mai aski) suka ce ba a taɓa kawo masa maganin bindiga ya harba ta ƙi tashi ba a iya tsawon rayuwar sa.

    Saboda haka ne ma yasa ake yi masa laƙabi da Nuhu mai bindiga, duk da yake an yi wasu a can baya, amma kuma su da kwari da baka suke yi kamar wata mace wacce ake iya kira da suna Madidi mace mai kamar maza, wadda ta kashe ɓarawo a daji ita kaɗai, ga sarkin Kudan Sambo, ga Mika na sari, ga Garba na Ode da sauran su.

    Bugu da ƙari kuma,  ya iya sana’ar wanzanci da ƙira da mafarauci da allura da ɗori da ba da magungunan gargajiya da gyaran keke da kuma harbi. Saboda a harkar faruta mafi yawanci shi kaɗai yake fita daji, ya tafi ya yi farautarsa a cikin dare ya dawo da safe, haka kuma wani lokacin ma yakan yi kwanaki uku ko sama da haka a daji bai ya dawo gida ba, sai dai kawai abin da ya farauto ya aiko da shi gari a siyar.

    Shahararsa 

    Ya shahara wajen iya sarrafa bindiga ta yadda yake so kuma a lokacin da yake so, misali idan  yana ɗaki a kwance a kan gadonsa, sai ya hango wata tsuntsuwa a kan wata bishiya, to zai iya auna ta daga nan inda yake zaune ya kuma harbo ta. Haka kuma akwai wani lokaci da ya tafi barikin sojoji na Fatakwal, wanda yake a Ohode ya dawo gida da wata adda, wanda wannan addar duk ƙafar da aka sara da ita ,sai dai kawai mutum ya ga ƙarfan ta gutsire ko ya noƙe ko ya lauye.

    Sannan kuma ya tafi Nassarawa wajen wani gari wanda ake kira da suna Toto ya yi kwana da kwanaki a can, ya kuma tafi jihar Sokoto wajen garin Moriki, ya tafi jihar Taraba wajen garin Zink, waɗannan su ne kaɗan daga cikin dajujjukan da  ya halarta daga cikin ƙasar nan banda su irin Katsina da Jigawa da dai sauran su.

    Bugu da ƙari kuma, akwai wata rana ya tafi daji akan ɗan wani gajeren mashin ɗin sa, bayan ya tafi dajin sai ya samu wani waje ya ajiye shi, can sai wani mutum ya lallaɓo ya taho zai ɗauke masa mashin ɗin nasa, ai ko yana zuwa kusa da inda mashin ɗin yake, sai kawai ya ga mashin ɗin ya koma kamar  Gada, sai ko ya tsaya ya ciro bakar sa wai zai harbe shi.

    Can sai ga Nuhu Baushe nan ya taho ya dafa mashin ɗin sa ya hau ya kara gaba, kawai abin nan  ya ba shi mamaki, kamar yadda duk wanda yake garin Kudan ko ƙaramar hukumar Kudan, ya san wane ne Lado, wanda shi Lado ɗa ne ga Nuhu Baushe, sannan kuma shi Lado idan mutane sun kai guda ɗari ko sama da haka, to ba su isa su hana shi ya wuce ba ko da ko sun kewaye shi baki ɗayansu.

    A lokacin da yake ganiyarsa, da zarar ya yi wani yunƙuri, sai dai kawai a ga ya wuce, kamar yadda an sha samun waɗansu zuga a garin Kudan, sun taho domin su yi masa lahani, amma kuma da zarar ya yi wani yunƙurin, sai kawai a ga ya fice.

    Saboda haka idan mutum ya yi nazari sosai, zai ga abin mamaki sosai akan sha’anin, domin kuwa kowane mutum a wannan zamanin zai iya shaidawa cewa masana na ɓangaran lafiya ne kaɗai suke yin allura ko kuma wanda ya yi ilimin zamani (boko) mai zurfi su ne kaɗai ne suke yi allura, amma  kuma shi  sai ga shi almajiri ne, wanda ya yi karatun allo, amma kuma sai ga shi yana yi wa mutane allura, wanda har ma ni kai na mai wannan rubutun na shaida ya yi min allura.

    Haka kuma akwai mutane da yawa waɗanda suka koyi allura, saboda yawan zama da suke yi da shi misali kamar ɗansa Nuhu mai aski a kuka, wanda ya shaida mana cewa dukkanin ‘ya’yan sa da shi kan sa, idan ba shi da lafiya, to da kansa yake yin allura, amma kuma almajiri ne.

    (Mun samu wannan jawaban ne ta hannun ‘ya’yan sa wato Suleman da Shittu a ranar lahadi 16/03/1442 Hijira=01/11/2020 da misalin ƙarfe goma na dare a shagon Shitu mai aski wanda yake Kuka Kudan).

    Danna nan don karanta tarihin hakimin Kudan

    Edita; Rumasa’u M. kallamu

  • Tarihin Dakta Alhaji Gambo Kudan

    Tarihin Dakta Alhaji Gambo Kudan

    An haifi  Dr. Alh Gambo a garin Kudan a ƙofar gabas a ranar 01/01/1954, sunan  mahaifinsa shi ne Khalid, ya yi karatun Allo, sannan kuma ya yi karatun zamani a makarantar firamare ta garin Kudan a 1960-1967, sai ya tafi makarantar gaba da fimare, wacce take Maƙarfi a 1967-1973, sai ya wuce makarantar ilimin lafiya, wacce take jihar Katsina (School of Nursing) a 1976-1980.

    Bugu da ƙari kuma, ya fara aiki ne a asibitin Ikara (General Hospital Ikara) daga 1980-1994,ya yi kuma aiki a asibitin maƙarfi 1994-2015, wanda a wannan asibitin na Maƙarfi, ya yi ritaya na aiki kamar yadda dokar ƙasa ta tsara, wanda mutum ba zai haura shekara 35 ba, yana aikin gwamti ba, wanda ya yi ritaya ne yana da matsayin chief nursing officer.

    Sannan kuma ya buɗe asibitin sa a garin Kudan, wanda yake kan hanyar zuwa Doka daga Kudan, a shekara ta 1985 mai suna Rahama Nursing Home har zuwa yau (shekarar asibitin  36 ke nan daga wannan shekarar ta 2021).

    Sannan kuma, ya samu lambobin yabo da dama, amma ga kaɗan daga ciki;

    Arewa Trusted Youth initiative Forum of Nigeria 2016.

    Association of General Private Nursing practitioners 06/11/2015.

    (Mun samu wannan bayanin ne daga bakin sa,wanda ya umarci ma’aikacin sa wato Dr. Mu’azu ya rubuto akan takarda, ya ba Mubarak Idris a kawo min)

    Domin karanta shinkafa mai ƙwai danna nan

    Edita; Rumasa’u M. Kallamu

  • Tarihin Sha’iri Aliyu Sani (na annabi) Kudan

    Tarihin Sha’iri Aliyu Sani (na annabi) Kudan

    An haifi Aliyu Sani a garin Kudan kuka wanda aka fi sani da suna “na annabi”  a ranar talata 12/4/1982, ya taso a cikin garin Kudan, ya yi karatun firamare da sakandire duk a garin Kudan, sannan kuma ya yi karatun allo a Zaria, bayan ya yi sauka, sai ya wuce makarantar koyar sana’o’i  wacce take birnin gwari  a Dogon dawa a cikin  jihar Kaduna, wacce take koyar da ilimin noma da kiwon dabbobi (Agric Training School). A yanzu kuma yana aiki a hukumar Kastelea ta jihar Kaduna.

    Dalilin da ya sa ya fara bege shi ne, wata rana a makarantar allo yana bacci, sai ya yi mafarki an tara masa mutane da yawa sai aka ba shi amsakuwwa (lasafika) yana rera waƙa, amma kuma ba zai iya tuna irin waƙar da yake rerawa ba, bayan ya farka daga baccin, sai ya roki Allah ya cika masa burin sa, aiko Allah ya amsa muradin sa, saboda ya rera bege da yawa daga cikin su akwai ;

    1.Na riƙe Mustafa annabi Ɗaha.

    2.Lale-lale mauludi.

    3.Ni dai gaskiya  ina ƙaunar manzo.

    4.Mai daraja da muƙami.

    5.Almukhtari.

    6.Almadani.

    7.Ba zan bari ba.

    8.Oyo-oyo maulidi ya zo.

    9.Mu muna son manzonmu.

    10. Maulidin annabi sai mun yi.

    11.Marhaba ɗan Amina shugaba.

    12. Ya Muhammadu shugaba na.

    13. Rasulu bege a gunka soyayya ce.

    14. Azzahara’u ‘yar ma’aiki.

    15. Halin rayuwa.

    16. Mu yi nazari.

    17. Mai ilimi.

    A ƙarshe kuma, ya yi aure yana da mata guda ɗaya da ‘ya’ya guda huɗu.

    (Mun samu wannan bayanin ne daga Aliyu Sani na annabi Kudan, wanda ya turo min ta waya ta  a ranar Alhamis 17/06/2020 da misalin ƙarfe 6;33 na dare).

    Danna nan don karanta tarihin marigayiya Hajiya Gude

    Edita; Rumasa’u M. kallamu

  • Tarihin Salman Khan Salim

    Tarihin Salman Khan Salim

    An haifi Abdurrashid Salim, wato Salman Khan a ranar 27 ga watan Disamba ta shekara 1965, a garin  Mumbai, sannan kuma ɗa ne ga fitaccen marubucin nan wato Salim Khan, wanda ya yi shura sosai  a fina-fina na shekarun baya, kamar Sholay (1975), Deewaar (1975), da Don (1978).

    Haka kuma,sunan mahaifiyarsa  furodusa fim Sushila Charak (wacce  aka fi sani da Salma Khan), kuma sau da yawa yana ba da labarinta a cikin hirarrakinsa.

    Salman Khan shi ne babba a cikin ‘ya’yan da mahaifinsa ya haifa guda biyar, daga cikinsu akwai  Sohail Khan da Arbaaz Khan, waɗanda su ma ‘yan wasa ne kuma mashirya fina-finan Indiya (Producer), sai kuma ‘yan uwansa mata guda biyu, wato Alvira Agnihotri Khan, wacce ta kasance mai shirya fina-finai kuma mai tsara kayan sa wa a cikin fina-finan Indiya, da kuma Arpita Khan Sharma, mai zanen cikin gida a cikin fina-finan Indiya.

    Salman Khan ya fara aikin wasan kwaikwayo ne ta hanyar yin rawa a cikin fim ɗin “Biwi Ho To Aisi” (1988). Har ila yau, ya samu  babban matsayi a cikin  ofishin romantic hit Maine Pyar Kiya (1989). Daga nan ne ya zama mai son kallon fina-finan Indiya.

    Salman Khan ɗan wasan Indiya ne, mai shirya fina-finai, kuma mai watsa shirye-shiryen talabijin, wanda fitattun ayyukansa da kuma fitattun jarumai gami da farin jini a wajen  jama’a, suka ba shi matsayin zama megastar a Bollywood.

    A cikin shekarun da suka wuce, ya zama wani yanki mai ban sha’awa na al’adun gargajiya a Indiya. Salman Khan, wanda ya fara a matsayin abin koyi kuma jarumi a ƙarshen shekarun 1980, ya fito a fina-finai sama da 100.

    Har ila yau, Salman Khan yana alfahari da sana’arsa, wanda  ya shafe kusan shekaru arba’in a cikinta. Ya yi shura da jarumai kamar su Shah Rukh Khan da Aamir Khan, Salman Khan yana ɗaya daga cikin jaruman maza uku da suka samu nasara a harkar fina-finai ta Bollywood tun daga shekarar 1990. Sannan kuma magoya bayansa, suna mutuƙar ƙauna gami da alfahari da shi, har sai suka sanya masu suna da  “Bhai” (Hindi: “Brother”) ko Bhaijaan (adireshin girmamawa da nuna ƙauna ga “ɗan uwa” a harshen Urdu).

    Bugu da ƙari kuma, Salman Khan ya yi shura a cikin fina-finai guda goma sha biyu, waɗanda suka shahara a ƙasar Indiya (ko a duniya baki ɗaya). Kamar su; Maine Pyar Kiya, Andaz Apna Apna, Hum Aapke Hain Koun..!, Hum Saath-Saath Hain, da Prem Ratan Dhan Payo.

    Khan ya yi aiki a matsayin abin koyi ga  kayayyakin talla irin su Limca (abin sha mai laushi), kafin ya sauko da rawar fim ɗinsa na farko, a cikin Biwi Ho To Aisi (“Matar ya kamata ta kasance kamar wannan”), a cikin 1988. Matsayinsa ya fara shahara ne tun daga  1989, wanda a cikin Fim ɗin soyayya nan “Maine Pyar Kiya” (“I have Loved”), wanda ya yi nasara a soyayyarsa, ya samu  kyautar Filmfare a matsayin mafi kyawun fitowar maza.

    Sunansa a cikin fim ɗin, Prem (“Love”), ya zama wani abu mai ban sha’awa a gare shi, kuma ya buga haruffa da wannan sunan a cikin fina-finai na gaba. Waƙoƙin Maine Pyar Kiya, irin su “Kabootar Ja Ja Ja” (“Fly Away, Pigeon!”), “Dil Deewana” (“Crazy Heart”), da “Mere Rang Mein Rangne Wali” (“Wanda Yake) Coloured in My Colours”), su ma sun kasance manyan ginshiƙai tare da masu sauraro kuma ana ci gaba da lissafa su a matsayin wasu fitattun waƙoƙin soyayya daga fim din Khan.

    Duk da yabon da ya samu na rawar da ya taka a fim ɗin “Maine Pyar Kiya”, aikin Khan ya ci gaba da riƙe kambunsa har zuwa fitowar fim ɗin “Hum Aapke Hain Koun” a 1994! (HAHK; “Wane ni a gare ku?”). Acikin fim ɗin ya fito ne a matsayin  Prem Nath, wanda ya kasance yaro mai fara’a, rashin laifi, iya  soyayya ga Nisha Choudhury, wanda hakan ya sa ya mamaye zukatan miliyoyin mutane da sauri.

    Har ila yau, kimiyyar sinadarai na Khan da Dixit ta kasance cikakkiyar abin farin ciki ga jama’a, kuma fim ɗin ya zama babban matsayi a wannan shekarar. A cewar mai bin diddigin kasuwancin fim Box Office India, HAHK ya zama fim ɗin Hindi da ya fi samun kuɗi a kowane lokaci, inda ya karya tarihin shekaru 19 da Bollywood classic Sholay (1975; “Embers”) ta yi.

    Ana la’akari da shi ɗaya daga cikin abubuwan da aka tsara na Bollywood da ingantaccen wasan kwaikwayo na iyali. HAHK ya riƙe rikodin akwatin ofishin har zuwa 2001, lokacin da Gadar: Ek Prem Katha (“Tawaye: Labarin Soyayya”) ya sauke shi, wanda jarumi Sunny Deol ya fito. Khan ya yi amfani da nasarar HAHK don ɗaukar sabbin ayyuka iri-iri daban-daban,don ganin ya riƙe kambunsa.

    Bugu da ƙari kuma, daga kan 1994-2010: Salman Khan  ya fito a cikin wasan barkwanci kamar Andaz Apna Apna (1994; “Kowa yana da nasa salon”) da babu shiga (2005); rawar da ya taka a fim ɗin  “Karan Arjun” (1995); da kuma soyayya, irin su fim ɗin “Kuch Kuch Hota Hai” (1998; “Wani abu ya faru”), wanda hakan ya ba shi damar lashe kyautar Filmfare Award, don jarumta da ya nuna a cikin fim ɗin, sai kuma fim ɗin  “Hum Dil De Chuke Sanam” (1999; ” madaidaiciyar zuciya”), Hum Saath-Saath Hain (1999; “We Stand United”), da Tere Naam (2003; “A cikin Sunan ku”).

    A shekarar 1999 fina-finan Khan guda uku ne suka shiga cikin fina-finan da suka fi samun kuɗi a Bollywood a waccan shekarun su ne; Hum Saath-Saath Hain, Biwi No. 1 (“Mace No. 1”), da Hum Dil De Chuke Sanam.

    Har ila yau, aikin Salman Khan ya samu karɓuwa sosai a shekarar 2009 ta fim ɗin Wanted, wanda har sai da ya kafa tarihi a duniyar Bollywood. A cikin 2010 Khan ya samu rawar tauraruwar Chulbul (“Robin Hood”) Pandey, ɗan sanda mafi girma fiye da rayuwa, a cikin blockbuster Dabangg (“Fearless”). Fim ɗin ya ƙayatar sosai gami da nishaɗantarwa,fim ɗin ya ɗauki hankulan masu kallo. A wannan lokacin, shahararsa ta sake bayyana a idon duniya sosai fiye da baya.

    A shekara ta 2012 jarumin ya sake mayar da matsayinsa na Chulbul Pandey a cikin Dabangg 2, wanda kuma ya kasance blockbuster. A shekarar 2019 ya dawo fagen kasuwanci tare da Dabangg 3. Fina-finan Tiger guda biyu na farko na Khan—Ek Tha Tiger (2012; “There Once Was a Tiger”) da Tiger Zinda Hai (2017; “Tiger Is Alive”)—wanda Khan ya taka Avinash Singh Rathore, jami’in leƙen asirin Indiya, sun yi nasara sosai.

    Don karanta yadda za a gabatar da aiki mafi muhuimmanci danna nan

    Tiger Zinda Hai ya karya tarihin daga cikin fina-finan Hindi da suka fi samun kuɗin shiga a kowane lokaci, inda ya ci gaba da lashe fim ɗin da ya fi ɗaukar hankali a Filmfare Awards. An saita ikon amfani da Tiger a cikin duniyar ɗan leƙen asiri , wanda kamfanin samarwa Yash Raj Films ya ƙirƙira.

    Salman ya kammala karatunsa a St. Stanislaus High School da ke Bandra, Mumbai, kamar yadda ƙaninsa Arbaaz da Sohail suka yi. Tun da farko, ya yi karatu a The Scindia School, Gwalior na wasu shekaru tare da ƙaninsa Arbaaz. Ya halarci Kwalejin Elphinstone kuma ya fita bayan shekara ta biyu.

    Abubuwa 10 masu ban sha’awa game da Salman Khan

    1. Jaruman da ya fi so su ne Sylvester Stallone & Hema Malini.

    2. Yana son tafiya Landan.

    3. Yana da tarin motoci kuma yana sha’awar tuƙin BMW, Mercedes-Benz da Land Cruiser.

    4. Salman yana son abincin ƙasar China kuma lambun China da ke Mumbai an ce shi ne abincin da ya fi so.

    5. Yawanci ya fi son saka  jeans kuma yana sanye da abin hannu na dutse turquoise a ciki da waje.

    6. Jarumin ya fi sha’awar tara sabulai iri-iri a banɗakinsa na gida, musamman sabulun da ke ɗauke da ‘ya’yan itatuwa da kayan marmari.

    7. Yana gudanar da wata ƙungiya mai suna “Being Human”.

    8. Jarumi ne mai son ganin ya nishaɗantar da mutane.

    9. Zai iya zama ƙwararren ɗan wasan linƙaya. Ya kasance zakaran linƙaya a makaranta har ma an sa shi a matsayin wanda yake wakiltar Indiya, don taron linƙaya.

    10. Baya ga wasan kwaikwayo, ya kuma gwada sauran  basirarsa a Bollywood: rubutu na Baaghi, kamar su ; A Rebel for Love, Chandra Mukhi and Veer. Sannan kuma mai gabatarwa a cikin Chillar Party, Jarumi kuma Dr Cabbie; Singer in Hello Brother, Chal Mere Bhai, Yuvaraj.

    Lambobin girmamawa da Salman Khan ya samu

    Salman Khan, ya samu lambobin girmamawa da yawa a cikin sana’arsa, ga wasu daga cikin nan;

    A. Filmfare Award

    1.  Salman Khan ya lashe jarumi  mafi kowa ƙwazo a ɓangaran maza a fim ɗin “Maine Pyar Kiya” ta 1990.

    2. Salman Khan ya lashe jarumi  mafi himma a fim ɗin “Kuch Kuch Hota Hai” ta 1999.

    B. Nomination for Filmfare Award

    1. Salman Khan  ya lashe jarumi mafi kowa ƙwazo a fim ɗin “Mene Pyar Kya” ta 1990.

    2. Salman Khan ya lashe jarumi mafi kowa ƙwazo a fim ɗin “Karan Arjun” ta 1996.

    3. Salman Khan ya lashe jarumi mafi kowa ƙwazo a fim ɗin “Jeet” ta  1997.

    4. Salman Khan ya lashe jarumi mafi kowa ƙwazo a fim ɗin ” Pyar Kya To Darna kya” ta 1999.

    5. Salman Khan ya lashe jarumi mafi kowa ƙwazo a fim ɗin “Hum Dil De chuke Sanam” ta 2000.

    6. Salman Khan ya lashe jarumin barkwanci  mafi kowa ƙwazo a fim ɗin ” Bwi No. 1″ ta  2000.

    7. Salman Khan ya lashe jarumi mafi kowa ƙwazo a fim ɗin “Tere Naam”  ta  2004.

    8. Salman Khan  ya lashe jarumin mafi kowa ƙwazo a fim ɗin ” Baghban” ta 2004.

    9. Salman Khan   ya lashe jarumin barkwanci mafi kowa ƙwazo a fim ɗin “No Entery” ta  2006.

    10. Salman Khan  ya lashe jarumin barkwanci mafi kowa ƙwazo a fim ɗin “Dabangg” ta 2011.

    C. Zee Cine Award

    1. Salman Khan an zaɓe shi a matsayin jarumi  mafi kowa ƙwazo a ɓangaren maza,wanda ya samu kyautar “Zee Cine Award”  a fim ɗin “Tere Naam” ta 2004.

    2. Salman Khan   an zaɓe shi a matsayin jarumi mafi kowa ƙwazo a ɓangaren maza, wanda ya samu kyautar “Zee Cine Award”  a fim ɗin  “Mujhse Shaadi Karogi” ta 2005.

    3. Salman Khan an zaɓe shi a matsayin jarumi mafi ƙwazo a ɓangaren maza, wanda ya samu kyautar “Zee Cine Award”  a fim ɗin “Entry” ta 2006.

    4. Salman Khan an zaɓe shi a matsayin jarumi mafi ƙwazo a ɓangaren maza, wanda ya samu kyautar “Zee Cine Award” a fim ɗin ” Dabangg” ta  2011.

    D. Star Screen Award

    1. Salman Khan ya lashe kyautar “Stardust Award”, a matsayin jarumi mafi ƙwarzon shekara na ɓangaren maza a fim ɗin “Dabangg” ta 2011.

    E. Nomination

    1. Salman Khan an zaɓe shi a matsayin wanda ya lashe kyautar “Star Screen Award” ɓangaren jaruma na fim ɗin “Tere Naam”  ta 2004.

    2. Salman Khan an zaɓe shi a matsayin wanda ya samu kyautar “Star Screen Award”  a fim ɗin “Pride and Honour”  ta  2005.

    F. Bollywood Movie Award

    1. Salman Khan ya lashe kyautar mai taken ” Most Sensational Actor”, a fim ɗin “Chori Chori Chupke Chupke”  ta 2002.

    G. International Indian Film Academy Award

    1. Salman Khan ya lashe kyautar IIFA a matsayin “Habitat Humanity Ambassadorship”  ta 2010.

    H. Stardust Award

    1. Salman Khan ya lashe kyautar “Stardust Award” a matsayin gwarzon shekara na ɓangaren maza a fim ɗin “Dabangg” ta  2011.

    I. Big Star Entertainment Award

    1. Salman Khan ya lashe kyautar “Most Entertaining Film Actor Award” a fim ɗin “Dabangg” ta 2010.

    J. Indian Television Award

    1. Salman Khan ya lashe kyautar “Best Anchor”, a fim ɗin “Ka Dum” ta 2008 (Zagaye na farko).

    2. Salman Khan ya lashe kyautar “Best Anchor” a fim ɗin “Ka Dum” ta  2008 (zagaye na biyu).

    Danna nan don karanta waƙar bikin ƙaddamar da manhajar WikiHausa

    Edita; Rumasa’u M. kallamu