Matakan Bunƙasa Ƙudurar Ɗan’adam

0
1812

Bayan salati da sallama ga Manzon tsira Annabi Muhammadu (SAW), tsira da aminci su tabbata a gare shi da Alayensa da Sahabbansa da waɗanda suka bi sahunsu baki ɗaya.

Bayan haka; wannan bayani an yi shi ne taƙaice a kan hanyoyin da za su taimaka wa ɗan Adam wajen bunƙasa ƙudurarsa da mutumtakarsa (personality), waɗanda aka kasa gida uku, sai kuma ɗan bayani a kan manufofin da ya kamata mutum Musulmi ya ɗaura don cimma nasara a rayuwarsa.

Ina fata za a gafarce ni a kan kurakuraina kuma a yi min gyara, tare da kyautata min zato, abin da nai daidai kuwa, a yi min addu’a.

MATAKI NA FARKO
KA SAN ZATIN KANKA (KNOW YOUR PERSONALITY)

Hanyoyin da za ka bi domin sanin zatin kanka suna da yawa, kuma masu sauƙi ne kwarai ga waɗansu guda takwas:

Matakan Bunkasa Ƙudurar Ɗan'dam
Matakan Bunkasa Ƙudurar Ɗan’dam
1- ka fahimci abin da ka ginu a kansa.

Ina nufin ka san abin da Allah Ta’ala ya halicce ka da shi, domin sanin wannan zai taimaka maka wajen sanin kanka da kyau.

Idan kuwa ka san kanka, to ka san za ka iya amfanar kanka ta ɓangarori daban daban. Ɗan’adam kuwa Allah Ya halicce shi ne da abubuwa guda biyu masu zuwa:

A- Gangar jiki: Wanda ya kamata ka san dame aka halicci ita kanta gangar jikin taka. To kamar yadda kowa ya sani dai farkon halitta Babanmu Annabi Adam (AS) Allah Ta’ala ya halicce shi ne da yumɓu (laka/taɓo).

Tare da haka kuma, Allah ya sanya ɗan Adam shi ne mafi kyawon halittunsa, idan kasan haka, sai ka ga ashe kai ma kana da muhimmanci, don haka sai ka ɗau kanka da muhimmanci ka ba shi haƙƙinsa da ya dace. Allah Ta’ala yana cewa:

(الذي أحسن كل شيء خلقه وبدا خلق الإنسان من طين. ثم جعل نسله من سلالة من ماء مهين.)

Shi ne wanda ya kyautata halittar komai, kuma ya fara halittar ɗan Adam daga yumɓu. Sannan ya sanya tsatsonsa daga ɗigon maniyyi na ruwa wofintacce” (Surat Sajdah: 6-7).

Akwai ayoyi waɗanda ba su da iyaka a kan halittar ɗan Adam wanda yin tunani kansu zai taimake ka wajen sanin muhimmancinka a rayuwa da muhimmancin samar da kai, wanda ba a banza kake ba. Allah Ta’ala ya ce:

(وفي أنفسكم أفلا تبصرون)

kuma a kan kawunanku, shin ba kwa zam masu lura ba?” (Surat Zariyat: 21)

Idan ka yi dubi a kan kanka, za ka ga ababe daban-daban da Allah Ta’ala ya karrama ka da su, kamar abubuwan da suka shafi jiki, kana da ido, alhali ga wani can makaho ne, kana da hannu, wani bai da shi, kana da ƙafa, wani gurgu ne, kana da kunne wani kurma ne…. to ashe Allah yai maka baiwa mai yawa waɗanda ba a banza suke ba.

B- Ruhi (rai): abin da ya shafi rai kuwa shi ne mafi muhimmanci ga jikin ɗan Adam domin ran ɗan Adam daga wani ruhi na Allah Ta’ala yake.

Ashe wannan kawai, ya isa ka san irin ƙarfin dake tare da kai na ƙudura da irada da girma da muhimmanci… Allah Ta’ala ya ce:

(ثم سواه ونفخ فيه من روحه وجعل لكم السمع والأبصار والأفئدة قليلا ما تشكرون)

“sannan ya daidaita shi Ya busa masa rai daga ruhinSa, Ya sanya muku ji da gannai da hankula, kaɗan ne ke iya godewa” (Surat Sajdah: 8)

A wani wajen kuwa Allah Ta’ala cewa ya yi:

(فإذا سويته ونفخت فيه من روحي فقعوا له ساجدين)

idan na daidaita shi, na busa masa daga ruhina, sai ku faɗi kuna masu yi masa sujada” (Sauratul Hijr: 29)

Idan ka dubi abin da ya shafi wannan kuwa za ka ga irin baiwar da Allah ya yi maka, kamar hankali, wani mahaukaci ne… Da wannan za ka fahimci cewa Allah ya halicci Ɗan’adam daga abubuwa guda biyu, su ne: Gangar jiki da kuma Ruhi waɗanda dukkansu suna da matuƙar muhimmanci gare ka.

To don me ba za ka ɗauke su da muhimmanci, ka ba su haƙƙoƙinsu ba?

2- ka san sirrukanka: wannan kuwa wani abu ne wanda ya shafe ka tsakaninka da kanka da kuma Ubangijinka, masanin komai.

Kowane ɗan Adam kuwa yana da wani sirri wanda zai iya zama mai kyau ne, ko marar kyau, kamar misali yafiya da rashin riko.

Ka ga Allah ne kawai ya san abin da ke cikin zukata, haka kuma, kamar misalin hassada da munafunci, ka ga mutum idan yana da iren waɗannan halaye, Allah kaɗai ya sani.

(يعلم خائنة الأعين وما تخفي الصدور)

Shi ya san mayaudarin ido da abin da zukata ke ɓoyewa

Sai kuma wasu sirrukanda zaka iya fada ma na kusa da kai kamar iyaye da aminanka.

3- ka fahimci ɓangaren da Allah ya ajiye ka: Ina nufin ɓangaren ababen da suka shafi rayuwa, domin kowa da inda Allah ya ajiye shi, wani mai kuɗi wani talaka wani ɗan kasuwa wani likita wani mahauci wani almajirin ilmi wani malami da dai sauransu.

Ba ana nufin idan kai talaka ne, ka yi ta zama a talaka ba, arziƙi dai na Allah ne, amma sai ka bi hanyoyin da suka dace domin samun sauƙi, idan kuwa mai kuɗi kake, to ta ina ya kamata ka sarrafa su?

4- Ka fahimci irin damar da kake da ita: amfani da dama kowace iri ce kada ka bar ta ta wuce a banza, wannan damar kuwa ta kunshi LOKACI da KARFI da KUDURA da DUKIYA da sauransu.

Za ka yi mamaki kwarai, yayin da ka tantance lokacinka na kullum wanda kake da awa ishirin da hudu a kullum rana, yayin da za ka ga kana da lokaci mai yawa yana shuɗewa a wofi. Ka tuna da faɗar Manzon Allah (SAW) da yake cewa:

(لا تزال قدما عبد يوم القيامة حتي يسأل عن أربع: عن عمره فيم أفناه وعن ماله فيم اكتسبه وعن شبابه فيم أفناه وعن جسده فيم أبلاه)

“Ƙafar ɗayanku ba za ta gushe ba ranar Ƙiyama, har sai an tambaye shi a kan abubuwa huɗu: a kan shekarunsa cikin me ya ƙarar da su, a kan dukiyarsa, ta ina ya tara ta, a kan samartakarsa, kan me ya ƙarar da ita, haka kuma a kan jikinsa a kan me ya tsofintar da shi?” (Tirmizi)

Ka sani cewa damar da kake da ita za a tambaye ka a kanta gaba ɗaya, don haka sai ka ɗauki mataki.

5- ka fahimci irin al’adunka da ɗabi’unka na kwarai, don inganta su, domin za ka samu da yawan mutane waɗanda suna da ala’adu na kwarai, amma saboda rashin zurfafa tunani ba su damu da su ba; ballantan su ɗauke su da muhimmanci. Kamar misalin kyauta, tausayi son juna da sauransu. Manzon Allah (SAW) yana cewa:

“أحب الأعمال إلي الله تعالي أدومها وإن قل

“Mafi kyawon aikin da Allah Ta’ala ya fi so shi ne wanda aka dauwama kansa komin ƙanƙantarsa

6- ka fahimci irin ɗabi’unka da al’adunka maras kyau, don nisantarsu da kuɓuta daga tarkonsu.

Domin ire-iren waɗannan su ne sukan ja mutum zuwa ga halaka da kauce tafarkin Allah Ta’ala.

Ire-iren waɗannan al’adu kuwa sun haɗa da ƙarya, zambo, habaici, girman kai, jiji da kai, ganin ƙyashi, da sauransu. Manzon Allah (SAW) yana cewa:

“ولا يزال العبد يكذب حتي يكتب عند الله كذابا”

kuma bawa ba zai gushe ba, yana ƙarya har sai an rubuta shi a matsayin maƙaryaci a wajen Allah

Saboda haka idan ka san kana da iren waɗannan al’adu, sai ka yi ƙoƙarin nisantar su sannu-sannu.

7-karanta littafan dake magana a kan ɗabi’un ɗan Adam: babu dai wani littafin da ya yi bayani a kan haka a bayan kasa irin Alƙur’ani mai girma, domin shi saukarwa ne daga Masanin dukkan komai, kuma tunda Allah ne ya ƙirƙiri halittar ɗan Adam ya zama shi ne ya fi cancanta ya bada bayani cikakke game da shi, ko Hausawa ma sukan ce “Halin ɗan  Adam sai Allah” wato Allah kaɗai ya san halin ɗan Adam.

Kaɗan daga cikin ayoyin da suka yi magana a kan halin ɗan Adam kuwa su ne:

(إن الإنسان خلق هلوعا. إذا مسه الشر جزوعا. وإذا مسه الخير منوعا. إلا المصلين)

“Haƙiƙa an halicci mutum da tsananin kwaɗayi, mai tsananin raki, idan sharri ya shafe shi, kuma mai tsananin rowa idan alheri ya shafe shi. Sai dai masu yin sallah. waɗanda suke dauwama a kan sallarsu”. (Surat Al’ma’arij:19-23)

Sanin wannan zai taimaka maka wajen sanin irin ɗabi’ar ɗan Adam ta ƙwarai da marar kyau, sai ka duba ka ga, kai kuma a wane ɓangare kake? Za ka iya amfani da sauran littafan psychology da finafinan bidiyo da sauransu.

8- Tambaya: domin samun ƙarin bayani da ƙaruwa da experience na wasu, za ka iya yin tambaya a kan ɗabi’un ɗan Adam ko ɗabi’unka kai kanka.

Wasu da yawa ko an ce su yi tunani, tunanin nasu bai iya kai su ga fahimtar wasu ababen, saboda haka tambaya ita ce mafi sauki. Allah Ta’ala ya ce:

(فاسألوا أهل الذكر إن كنتم لا تعلمون)

ku tambayi masana ilmi idan kun kasance ba ku sani ba

Da farko waɗanda ya dace ka fara tambaya su ne iyaye, domin su ne suka fi kowa kusa da kai musamman Mahaifiya, kuma sun san ababen dake yi maka tasiri da sauransu.

Haka kuma, za ka iya tambayar aminanka, kamar yadda za ka iya tambayar malaman addini da na tarbiyya (Education) da na Psychology.

Za ka tambaye su ne a kan hoton kanka gaba ɗaya, domin an ce “Mumini madubin dan uwansa ne”

Idan har ka gama bin waɗannan matakai guda takwas, waɗanda su ne za su ba ka hoton kanka gaba ɗaya, to, daga nan ne za ka tantance inda kafi ƙarfi da inda kake da rauni, sai kuma ka ɗauki matakin da ya dace don bunƙasa ƙudurarka.

Ga wani jadawali nan wanda zai taimake ka wajen tacewa:

Jadawalin tace ɗabi’una:

Abubuwanda ka fi ƙarfi a kansu/ Abubuwan da kake da rauni a kansu.

1- Sallah ba ta wuce ni
2- Ina da tausayi, ina taimako
3- Ina sanya kayan mutunci idan zan fita

1-Ban damu da yin sallah ba wani lokaci
2- Ba ni da wani abin da nake ɗauka da muhimmanci
3-Nakan sa kayan da ba su dace ba idan zan fita.

Damar da kake da ita hukunci ko mataki

1- Ina da kudura/irada
2-Ina da lokaci
3-Ina da kuɗi /dukiya
4-……
5-……. Ana nufin ɗaukar mataki a kan abin da ka fi ƙarfi ko rauni a kansa ta hanyar ragi ko ƙari.

(حاسبوا أنفسكم قبل أن تحاسبوا)

ku yi wa kanku hisabi tun gabanin a yi muku

Tambayoyi masu muhimmanci:

1- Ta yaya zan yi amfani da ɓangarorin da na fi Ƙarfi a kansu, da damar da nake da ita domin bunƙasa kaina?

a- Tsari da lazimtar tsarin.

b- Lazimtar ababen da nake da su masu kyau da ƙoƙarin ƙara wasu.

c- Addu’a don tabbata a kansu.

2- Ta wace hanya zan kuɓuta daga ɓangarorin da nake da rauni
a kan su domin gusar da abubuwan dake rusa mani tsari?

a- Kyamatar su a zuciya da addu’a.
b- Tuba.

(قُلْ يَا عِبَادِيَ الَّذِينَ أَسْرَفُوا عَلَى أَنْفُسِهِمْ لَا تَقْنَطُوا مِنْ رَحْمَةِ اللَّهِ إِنَّ اللَّهَ يَغْفِرُ الذُّنُوبَ جَمِيعًا إِنَّهُ هُوَ الْغَفُورُ الرَّحِيمُ) (سورة الزمر: 53)

ka ce ya ku bayina waɗanda suka yi ɓarna a kan rayukansu, kada ku yanke ƙauna daga rahamar Allah, haƙiƙa Allah yana gafarta dukkan zunubai, kuma lallai Shi ne Mai gafara Mai tausayi.

c- Maye gurbin mummunan aiki da kyakkyawa.
d- Nisantar abokan wofi.

MATAKI NA BIYU
IYAKANCE MANUFOFI

Akwai da yawa waɗanda kan kwana su tashi kullum, suna cikin dogon buri ko manufa, kuma suna ɗaukar matakai tuƙuru don cimma wannan burin, amma haka za su ƙare rayuwarsu ba su ci nasara wajen cimma ko ɗaya daga cikin wadannan manufofin nasu ba.

IYAKANCE MUNUFUFI
IYAKANCE MUNUFUFI

Dalili kuwa shi ne, suna yin kuskure tun farko wajen gina wannan manufa, haka kuma da yawa na karkace hanyar isa zuwa gare ta.

Za ka ga wani burinsa kullum shi dai ya zama mai kudi, amma bai ɗauki hanyoyin da za su zama sababi zuwa ga hakan ba, shin zai bi ta hanyar kasuwanci ne, ko noma ko kuwa aiki?

Wani ko za ka ji yana cewa shi malami yake so ya zama, amma bai iyakance wane irin malami yake son zama ba, na boko ko na addini?

Idan na boko yake so, to a wane ɓangare?

Haka idan na addini ne shi ma a wane ɓangaren?

Malamin fiqhu ko hadisi? In na fiqhu ne wane ɓangaren?

Fiqhun ibada ko na mu’amala ko kuwa usulul fiqh. Haka dai ya kamata ka iyakance manufofinka wanda za ka iya ɗaura masu jadawali kamar haka:

Jadawalin iyakance manufofi:

Manufofin da suka shafi ibada, iyali, aiki, Hutu

Jadawalin tace dabi'una:
Jadawalin iyakance manufofi:

1- Lazimtar sallah cikin lokaci
2- Azumin Litinin da Alhamis

1- Zaɓar mata ko mijin da ya dace da ni.
2- Ba su haƙƙoƙinsu.
3- Ciyar da su daga halal

1- Aikin halal
2- Kasuwanci na halal
3- Kiyaye dokokin Musulunci a ma’aikata

1- 30 minutes daga safe zuwa azahar.
2- 30 minutes bayan azahar
3- 30 minutes da yamma
4- Barcin awa shida.

Alaƙoƙin Abubuwan da ka fi ƙwarewa a kansu. wasu 
1- Zamantakewa
2- Girmama na gaba
3- Taimako

Bayan ka gama iyakance kowace manufa cikin jadawalin da ya gabata, sai ka ɗauki kowace manufa ka sanya mata jadawali na daban, mai zaman kansa da matakan isa zuwa gare ta.

Jadawalin matakan manufa:

Manufa: lazimtar sallah cikin lokaci, kwanan wata Gudanarwa
Mataki na ɗaya: yin alwallah da an kira sallah …………… …………..
Na biyu: tafiya masallaci kafin a tayar da sallah …………… ……………
Na uku: yin sallah cikin jam’i …………… ……………
…………. …………… ……………

Kana iya ɗaura wannan jadawalin daidai da sati ɗaya sannan ƙarshen kowane sati sai ka duba kaga irin ci gaban da ka samu.

MATAKI NA UKU
TSARA LOKACI

Kafin mu yi bayanin yadda za ka tsara lokacinka, ya kamata mu fara sanin muhimmancin lokaci.

TSARA LOKACI
TSARA LOKACI

Akwai ayoyi da yawa a cikin Alƙur’ani mai girma dake magana a kan lokaci da muhimmancinsa kamar ayoyin dake magana kan rana da wata da amfaninsu a rayuwa, da waɗanda ke magana a kan dare da yini, da ma masu magana a kan zamani gaba ɗaya. Allah Ta’ala yana cewa:

(قل أرأيتم إن جعل الله عليكم الليل سرمدا إلي يوم القيامة من إله غير الله ياتيكم بضياء أفلا تسمعون. قل أرأيتم إن جعل الله عليكم النهار سرمدا إلي يوم القيامة من إله غير الله يأتيكم بليل تسكنون فيه أفلا تبصرون. ومن رحمته جعل لكم الليل والنهار لتسكنوا فيه ولتبتغوا من فضله ولعلكم تشكرون)

“ka ce, “shin kun gani, idan Allah Ya sanya dare tutur a kanku, har zuwa ranar ƙiyama, wane abin bautawa wanin Allah zai zo muku da haske? Shin, ba ku ji ne?” “ka ce, “shin, kun gani, idan Allah ya sanya yini a kanku tutur zuwa ranar ƙiyama, wane abin bautawa, wanin Allah, zai zo muku da dare, wanda kuna natsuwa a cikinsa, shin fa, ba ku gani ne?” “kuma daga rahamarSa Ya sanya muku dare da yini domin ku natsu a cikinsa, kuma domin ku nema daga falalarSa, kuma ko da za ku gode“. (Surat Kasas: 71-73)

Idan ka lura da kyau a waɗannan ayoyi za ka ga suna bayani a kan yadda Allah Ta’ala ya tsara mana lokutanmu da kuma abin da za mu yi a ko wane lokaci, kamar neman falalarSa cikin lokacin yini wanda shi ne neman abinci da kuma hutu da dare da sauransu.

Wanda wannan kuma ba zai hana mu kiyaye dokokin Ubangiji ba, na ɓangaren ibada, kamar yadda Allah Madaukaki Ya ce:

(رجال لا تلهيهم تجارة ولا بيع عن ذكر الله وإقام الصلاة وإيتاء الزكاة يخافون يوما تتقلب فيه القلوب والأبصار)

wasu mazaje ne, waɗanda wani kasuwanci ko cinikayya ba su shagaltar da su daga ambaton Allah da tsaida sallah da bayar da zakka, suna tsoron wani yini wanda zukata da gannai ke jujjuyawa” (Surat Nur: 38)

Wannan kaɗai ya ishe ka ka gane muhimmancin lokaci, ka dau matakin da ya dace wajen (utilizing) na shi. Domin shuɗewa yake, kuma in ya tafi ba zai dawowa har abada, kada ka bari nadama ta zo maka ranar da ba ta da wani amfani. Allah Madaukaki Ya ce:

(حتي إذا جاء أحدهم الموت قال رب ارجعون. لعلي أعمل صالحا فيما تركت كلا إنها كلمة هو قاءلها ومن وراءه برزخ إلي يوم يبعثون)

“har sai mutuwa ta zo ma ɗayansu, sai ya ce, “Ya Ubangiji a mayar da ni (duniya). Lallai ni zan aikata aikin ƙwarai” ina! wannan wata magana ce kawai da shi yake fadi, ga kuma barzahu can tana jiran shi har zuwa ranar da za a tayar da su” (Surat Mu’minun: 99-100)

Don haka, kada ka bari ka zamto cikin waɗanda zukatansu ke cikin gafala.
Yanzu sai ka bi ni sannu a hankali domin ganin yadda za ka tsara lokacinka.

Ka rubuta rabe-raben lokutanka. Misali:

– Shekara
– Kana da wata goma sha biyu a shekara
– A duk wata kana da sati huɗu
– Kwana bakwai a sati
– Awa ishirin da hudu a rana
– Kana da awa takwas daga asuba zuwa azahar 5:00am to 1:00pm
– Ana samun awa uku daga azahar zuwa la’asar 1:00pm to 4:00pm
– Harma akwai awa uku daga la’asar zuwa magariba 4:00pm to 7:00pm
– Sannan da awa biyu daga magariba zuwa isha’i 7:00pm to 9:00pm
– kuma ma da awa takwas daga Isha’i zuwa Asuba 9:00pm to 5:00am

Idan ka kirga wadannan awoyi za su ba ka awa ashirin da huɗunka na rana guda: 8+3+3+2+8=24.

Daga nan sai ka ɗauki kowane lokaci ka tsara masa abubuwan da za ka yi a cikinsa. Misali Sallah dai dole ne in lazimce ta a kullum, to, bari in fara fitar mata da lokacinta:
Jadawalin lokutan sallah:

rana Asuba Azahar La’asar Magariba Isha’i
Awa 24 Minti 30 15 10 10 15

Idan ka hada wadannan lokuta daka warewa Sallah zaka ga duka awa ɗaya da minti ishirinne kawai.

To, sai ka ɗebe awa ɗaya da minti ashirin cikin awa ashirin da huɗunka na rana. Za ka ga kana da sauran awa ashirin da biyu da minti arba’in.

Su kuma sai ka rarraba su ga ayyukanka na yau da kullum. Kamar wanka, wanki, dafa abinci, zuwa makaranta, wajen aiki, hira, ziyara, chatting, hutu, barci da sauransu.

Yi ƙoƙari ka tsara ayyukan dake da kama da juna da yan’uwansu:

Jadawalin ayyukan yau da kullum:

Asabar Ibada Abinci Motsa jiki Barci Mota jarida darasi hira chatting … …. Jumillar lokaci

Lahadi ……. …….. ……….. ………. ……..
Litinin
Talata
Laraba
Alhamis
Juma’a

Jadawalin ayyukan sati:

Daga ranar Asabar ….. zuwa Juma’a …..
Manufofin da nake son cimmawa cikin satin:
1-……
2-……
3-……

Ayyukan Asabar

… Lahadi
….. Litinin
…… Talata
…… Laraba
……..ALHAMIS

Abubuwan da zan Ɗaura sati hukunci akan satin da ya gabata.
Mai zuwa
…..
…..
…..

Bayan wannan sai ka lura da kyau ka ga ina lokacinka ya fi tafiya a wofi? Wanda za ka iya tsamo su ɗaya bayan ɗaya ta hanyar jadawalin dake zuwa.

Jadawalin tace abubuwa:

Abubuwanda ke bijirowa masu muhimmanci tare da buƙatar gaggawa. (waɗannan abubuwa su ne masu ƙwanƙwasa, amma suna da wahalar gina gaba, idan ba a yi taka tsantsan ba) sai ka duba ka ga nawa cikin ɗari suke ci maka na lokaci?

Abubuwa masu muhimmanci, amma ba su bukatar gaggawa. (waɗannan kuwa su ne masu gina zati) sai ka tsara masu lokaci.

Abubuwa marasa muhimmanci amma suna da fizgar jama’a. (wadannan kuwa su ne mayaudaran abubuwa. Kamar misalin kallon ƙwallo world cup ds) sai ka yi tunani a kansu.

Abubuwa marasa muhimmanci kuma ba su bukatar gaggawa. (wadannan kuwa su ne ruɗani da ɓata. Kamar lazimtar fcbk, net maras amfani, finafinai maras ma’ana, hira, ds) sai ka nisance su.

Ta wannan jadawali ne za ka tsamo inda lokacinka ya fi shuɗewa. Haka dai za ka dinga ɗaura jadawaloli daga na ɗan lokaci zuwa na lokaci mai ɗan tsawo zuwa lokaci mai nisa don cimma burinka da kuma gina ƙudurorinka.

MANUFOFIN DA YA KAMATA MUSULMI YA GINU A KANSU:

1- Ibada: domin itace dalilin zuwan ka duniya gaba ɗaya. Allah bai halicci Mutum da Al’jani ba sai don su bauta masa. Wannan bautar kuwa tana da manufa, wadda ita ce, cin nasara da jin daɗin rayuwa duniya da lahira.

Kamar yadda muka yi bayani can baya cewa, Allah Ta’ala ya halicci ɗan Adam daga abubuwa guda biyu, su ne: gangar jiki da kuma ruhi.

To, kowanen su yana buƙatar abincin da za ka bunƙasa shi da shi wanda bunƙasa waɗannan biyun shi ne, bunƙasa ƙudurarka da mutumtakarka da rayuwarka gaba ɗaya. Shi kuwa Ruhi ana ciyar da shi ne da ibada.

Wanda ya rayu cikin bautar Allah Ta’ala, to, Allah zai rayar da shi rayuwa mai tsarki wato yardadda.

Kuma da ambaton Allah zukata ke natsuwa. Haka kuma wanda ya kauda kai daga ambaton Allah, to, lallai yana da wata rayuwa mai tsananin ƙunci. Sai ka tsara wa ibadarka lokuta kamar yadda ya gabata.

2- Aiki don samun abin rayuwa: wannan kuwa dole ne ga dukkan mai hankali domin ya ɗauki nauyin kansa da na iyalinsa kai harma da na yanuwa.

A nan abin lura shi ne, wane irin aiki ne ya dace da ni? Na halal ne ko na haram? Aikin gwamnati ne ko Noma ko Aikin hannu (sana’a) ko kasuwanci?

Koma dai wane irin aiki ne, sai ka lura da faɗar Allah Madaukakin Sarki:

(وقل اعملوا فسيري الله عملكم ورسوله والمؤمنون وستردون إلي عالم الغيب والشهادة فينبؤكم بما كنتم تعملون)

“kuma ku yi aiki, da sannu Allah zai ga aikinku da ManzonSa da kuma Muminai, kuma za a mayar da ku zuwa ga Masanin gaibu da shahada ya ba ku labarin abin da kuka kasance kuna aikatawa“(Surat Tauba: 105)

3- Zuriya ko Iyali: yanzu fa ka kai matsayin da za ka iya haɗa iyali naka na kanka, wanda hakan shi ne sunnar da Allah Ta’ala ya sanya wa rayuwarka.

Haɗa iyalin shi ne cikar Mutumtakarka ga idon kowa. Haka kuma idan ka yi watsi da wannan manufar to, ka sani cewa ka yi watsi da ƙudurarka kenan, kuma ka rusa rayuwarka.

Ba ka ga Allah ya sanya wannan sunnar har ga AnnabawanSa ba?! Allah Ta’ala ya ce:

(ولقد أرسلنا رسلا من قبلك وجعلنا لهم أزواجا وذرية…)

kuma haƙiƙa Mun aika Annabawa gabaninka, kuma Muka sanya maSu mata da zuriya” (Surat Ra’ad: 38)

To sai ka tsara yadda za ka tsara iyalinka, tun daga neman aurenka, har zuwa ga samun zuriya, ka keɓance musu haƙƙoƙinsu, da manufar da za ka gina su a kanta.

4- Jama’ar dake kewaye da kai: domin su ma suna da haƙƙoƙi a kanka, kamar yadda nassoshi suka nuna, Hadisi ya zo daga Abi Ayyub bin Salamah bin Mukhlid ya ce:

Manzon Allah (SAW) ya ce: “wanda ya kasance cikin biyan buƙatar mutane, to, Allah zai kasance cikin biyan bukatunsa” (Bukhari da Muslim cikin Mukhtasar sahih Muslim: 2:243)

Idan ka lura da wannan hadisin za ka ga muhimmancin jama’a, sai ka ɗaura jadawalin da za ka bi don biyan haƙƙoƙinsu.

5- Gangar jikinka: kamar yadda muka yi bayani can baya cewa an gina mutum ne daga abubuwa biyu, Ruhi da Gangar jiki, kuma muka bayyana cewa, kowanen su yana buƙatar abincin da za ka bunƙasa shi da shi, to, jikinka ma na buƙatar abin da za ka gina shi da shi don samun cikakken ƙoshin lafiya.

Sai ka yi wa abincinka tsari, kuma ka rika excersice motsa jiki domin yana da matukar muhimmanci wajen gina lafiyayyen jiki, masu ilmi suna cewa: “Cikakken hankali yana ga lafiyayyen jiki”. Kamar yadda Manzon tsira ya riga ya yi bayani cewa:

“Kuma jikinka na da haƙƙi a kanka“. Ashe wannan na da matuƙar muhimmanci.

Waɗannan su ne filaye guda biyar waɗanda nake ganin rayuwar ɗan Adam na kai komo cikinsu, kuma idan har ka ɗaura su gaban idonka, ka lura da kyau za ka ga cewa, idan har ka kiyaye su, to, su ne ke bunƙasa ƙudurarka da mutumtakarka gaba ɗaya.

Yanzu ga waɗansu ‘yan sharuɗɗa nan da za su taimake ka wajen kafa manufa:

SHARUƊƊAN KAFA MANUFA:

– Iyakance manufa.

– Daidaituwar ta da ɗabi’arka.

– Karɓuwar ta ga damar da kake da ita.

– Karbuwar ta da yanayi, zamani, lokaci, da kuma jama’ar da kake cikinsu.

– Dacewarta da matakan dake kaiwa zuwa gare ta.

ABUBUWAN DAKE TAIMAKAWA GA CIMMA MANUFA:

– Bin sababi, wato hanyoyin dake kaiwa gare ta.
– Haƙuri.
– Bin tsari.
– Juriya.

– Kokari da dagewa, domin “Wanda ya yawaita kasala, duniya za ta yi masa talala” (Kabir Kaita), haka kuma ka sani cewa “da dagewa ake neman buri, amma ana cimmasa ne da kaddara” (Kabir Kaita).

– Bin shawarar masu tajruba.
– Addu’a da mika al’amari zuwa ga Allah.
– Amfani da hankali, tunani, lura, da sauransu.

Ina fata wannan ‘yar taƙaitacciyar muzakkira za ta taimake ka  dan uwa Musulmi wajen gina kanka da al’ummarka. Subhanakallahumma, wabi hamdika, ash’hadu anla’Ilaha illa anta, astaghfiruka wa atubu ilaika.

Dan’uwanka a Musulunci:
Domin karanta mahangar siyasa a addin musulunci  danna koren rubutun nan

 

labarin da ya wuceMahangar Siyasa A Musulunce
Labarin na GabaYadda Ake Ayyukan Gida Domin Taimakon Juna