Cikakken Bayani A Kan Buɗa-baki

0
577

Buɗa Baki – Ana buɗa-baki da zarar rana ta faɗi, Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalaml) ya yi umarni wajen gaggauta yin buɗa-baki; kamar yadda ya zo cikin hadisin Sahal Bn Sa’ad (Radiyallahu Anhu) cewa; Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasalam Ya ce; “Mutane ba za su gushe cikin alheri ba, matuƙar suna gaggauta buɗa-baki”. (Bukhari 4/173).

An karɓo hadisi daga Abu Huraira Radiyallahu Anhu cewa, Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce; “Addini ba zai gushe ba yana mai galaba, matuƙar mutane na gaggauta buɗa-baki; domin Yahudawa da Nasara suna jinkirtawa”. (Abu Dawud 2355).
Har ila yau, wani hadisi daga Abu Darda’i (Radiyallahu Anhu) ya ce; “Abubuwa uku suna cikin ɗabi’un annabawa: gaggauta buɗa-baki; jinkirta sahur da ɗora hannun dama a kan na hagu lokacin sallah”. (Sahihul Jami’u 3034).

Game da abin da mutum zai fara buɗa-baki da shi kuwa, an karɓo Hadisi daga Anas (Radiyallahu Anhu) cewa; “Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya kasance yana buɗa-baki da ɗanyen dabino kafin ya yi sallah; idan kuma bai samu ba sai ya yi da busasshe, idan kuma bai samu ba, sai ya kurɓi makwarkwatai na ruwa”. (Abu Dawud 2/306, Tirmizi 3/70).

Hadisi ya tabbata daga Abu Huraira (Radiyallahu Anhu) cewa, Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya ce; “Addu’o’i uku karɓaɓɓu ne: addu’ar mai azumi, da wanda aka zalunta, da matafiyi”. (Sahihul Jami’u 3027).

A wani hadisi daban ruwayar Tirmizi; Ibn Majah da Ibnu Hibban cikin hadisin Abu Huraira (Radiyallahu Anhu), Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) cewa ya yi; “Mutum uku ba a dawo da addu’arsu: mai azumi yayin da yake buɗa-baki, da shugaba adali, da addu’ar wanda aka zalunta”.

An karɓo hadisi daga Abdullahi Ibn Amru Ibn Aas (Radiyallahu Anhu) cewa; Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Waasalam) ya ce; “Haƙiƙa mai azumi yayin buɗa-bakinsa yana da addu’ar da ba a ƙin karɓa”. (Ibnu Majah 1/557, Hakim 1/239).

Mafificiyar addu’a yayin shan ruwa ita ce, addu’ar da aka rawaito daga bakin Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) mafi tsarki.

Wannan addu’a ita ce:

“Zhahabaz Zama’u Wabtallatil Uruk Wathabatal Ajru Insha Allah”.

Ma’ana: “Ƙishirwa ta tafi, jijiyoyi sun jiƙu; kuma lada ya tabbata insha Allah”. Sannan babu laifi mutum ya yi wata addu’a ta shi ta neman wasu buƙatunsa.

Domin karanta cikakken bayani a kan Halayen Da Ya Kamata Mai Azumi Ya Siffantu Da Su danna nan.

Domin karanta cikakken bayani a kan Falalar Nafilolin Azumi danna nan.

Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Guziri Ga Mai Azumin Ramadana (Bisa Koyarwar Alƙur’ani Da Sunnah); wanda Ibrahim Baba (Ibrahim Garba Nayaya (Baban Fauzan) ya wallafa shi; Domin karanta cikakken Littafin danna nan.

labarin da ya wuceFalalar Yin Umara A Watan Ramadan
Labarin na GabaCikakken Bayani A Kan Sahur