Haƙiƙa Sayyidina Husaini (Radiyallahu Anhu) yana da maɗaukakiyar daraja da alfarma a zukatan dukkan musulmi na ƙwarai musamman ma malamai.
Wannan ya sa bakinsu ya zo ɗaya wurin bayyana darajojinsu da falalarsa da nuna alhini da takaicin yadda ƙarshen rayuwarsa ta kasance. Wannan yana tabbatar da ƙaryar masu cewa wai Ahlussunna suna ƙin Ahlulbaiti ko kuma wai suna murna ga abinda ya faru ga Husaini da sauransu na zaluntarsu da aka yi wannan sharri ne ƙage ne.
Amma a lokaci guda Ahlussunna basa goyon bayan bidi’o’i da fitintinu da ake yi duk shekara idan ranar ashura ta zo har zuwa kwana arba’in, da sunan nuna juyayi da ta’aziyyar Husaini (Radiyallahu Anhu) da ‘yan tawagarsa, saboda babu wani daga cikin shugabannin Ahlul Baitin ko malamai na ƙwarai da suka aikata hakan. Su kuwa sun fi kowa son Ahlul Baiti da goyon bayansu (Radiyallahu Anhuma) da damuwa da halin da suke ciki.
Maganganun malamai suna da yawa dangane da falalar Husaini (Radiyallahu Anhu) da kuma matsayinsu a kan kashe shi da aka yi a ranar ashura a shekara ta 61 daga hijra, saboda haka zan kawo kaɗan daga cikinsu domin su wakilci sauran.
1- Ibn Abdulbarri Abu Amr Yusuf (A.H.S368 Y.M.S 495H)
Ibn Abdulbarri Ibn Abdulbarri haɗaɗɗen malami ne mai tsoron Allah da faɗin gaskiya, masanin hadisi, a cikin littafinsa na tarihin sahabbai mai suna “Al-Isti’ ab yana cewa:
“Husaini ya kasance mutum ne mai daraja, da tsananin riƙo da addini, da yawan azumi da salla da aikin hajji. Ya yi aikin hajji sau ashirin da biyar a ƙasa, an kashe shi ranar Juma’a goma ga watan Muharram shekara ta 61 daga hijira”.
2- Ibnul Arabi Al-Maliki (A.H.S. 468 Y.M.S543)
Shaihin malami Alƙali Abubakar Ibnul Arabi Almaliki bayan ya yi bayanin abinda ya faru a taƙaice na shahadar Husaini (Radiyallahu Anhu) sai ya ce:
“Ina ma dai a ce mai girma ɗan mai girma, sharifi ɗan sharifiya Alhusaini ya yi zamansa a gidansa, cikin iyalansa, yaƙi sauraran duk wanda ya zo da maganar ya nemi halifanci, koda kuwa irinsu lbn Abbas ne da Ibn Umar, ina ma dai a ce ya tuna abinda kakansa ya faɗa a kan wansa Hassan(ɗan nan nawa shugaba ne Allah zai sasanta rundunoni biyu manya masu yaƙar juna saboda shi).
Da ya tuna da ɗan uwansa ya rasa halifancin nan alhali yana da goyon bayan dukkanin rundononi kuma duk wasu manya a lokacin Suna tare da shi, sai ya ga to shi yaya za a yi ya samu wannan halifanci ta hanyar goyon bayan tarkacen mutanen Kufa. Ga kuma manyan sahabbai sun hana shi, Suna janye jikinsu daga neman halifancin da yake?
Kai ni dai na rasa ta cewa sai dai kawai na miƙa wuya ga hukuncin Allah, da kuma alhinin rasuwar jikan Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) ba don manyan sahabbai sun san cewa Allah bai ƙaddara halifanci ga iyalan Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) ba, kuma bai kamata a shiga cikin fitina ba, ai da ba zasu taɓa ƙyale shi ba.
3. Shaihul Islam Ibn Taimiyya (A.H.S 660 Y.M.S 728)
A iya ɗan ƙaramin sani na, a cikin dukkan malamai da suka yi Magana akan abinda ya faru ga Hussaini (Radiyallahu Anhu) da kuma matsayinsu game da Yazidu da mahaifinsa Mu’awiyya, da kuma shi’anci, babu wanda ya fi shan zagi da tsinuwa da tsana har ma da Kafirtawa a wurin ‘yan Shi’a Kamar Ahmad Ibn Abdulhalim Ibn Abdussalam Ibn Taimiyya.
Ibn Taimiyya ya wallafa wani babban littafi mai mujalladi tara mai suna “Minhajussunnatin Nabawiyya fi naƙdhi kalamis shi’a wal kadariyya” kan bayanin ɓacin aƙidun shi’a, a ciki yayi bayanai kan wannan mas’ala.
Kuma matsayin da ya ɗauka, ba wani abu da ya keɓanta da shi ba, a’a akwai malamai da suka gabace shi da kuma waɗanda suka zo bayansa da suke akan wannan matsayi, amma shi suka fi jin haushi, har ma da yi masa ƙazafin ƙin Ahlul Baiti da ma Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam), saboda kawai tsanain kiyayya, da kwarewa a cikin karya da karya da kage.
Wani babban malami wanda ya yi fice kan tattara littatafai da fatawowin Ibn Taimiyya, musamman waɗanda suke a rubutun hannu da buga su, mai suna Muhammad Ibn Ƙasim Rahimahullah, ya tattara maganganun da lbn Taimiyya yayi akan Ahlul Baiti, da sahabbai da matsayin Ahlusunna da ‘yan shi’a akansu, kasancewar masu zargin Ibn Taimiyya da ƙin Annabi (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) da iyalansa suna yawan ƙin maganganunsu daga wannan littafi.
Amma fa a gaskiyar Magana, basa kula da amanar ilimi a wajen ciro maganganun nasa, saboda suna yanko iya wurin da ya dace da son ransu sai kawai Su gina hukunci a kai, su yanke duk wurin da suka san asirinsu zai tonu in sun kawo shi.
Domin bayanin gaskiyar lamari kan matsayin Ibn Taimiyya akan wannan mas’ala da ma waɗansu mas’alolin zan kawo gaba ɗayan babin da malamin ya kawo a cikin littafin, sannan kuma in kawo bayanin matsayin wasu daga cikin fitattun almajiransa, domin in tabbatarwa da mai karatu cewa Ibn Taimiyya cikakken masoyin Manzon Allah ne (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) da iyalansa.
Amma kifin wannan ga abinda yake faɗa a cikin “fatawa” ɗinsa da manyan baƙaƙe: “Tsinuwar Allah da ta Mala’iku da ta mutane gaba ɗaya ta tabbata akan wanda ya kashe Hussaini, ko ya taimaka aka kashe shi. Kada Allah ya karɓi ibadunsa na farilla da na nafila.
“Ƙaunar Ahlul Baiti, tilas ne wajibi ne a kanmu, shi ne ya sa kullum muke yi musu salati a cikin sallolinmu Tsinuwar Allah da ta mala iku da mutane baki ɗaya ta tabbata a kan maƙiya Ahlul Baiti.
To mai karatu mu je zuwa da fatan ba za ka Ƙosa ba. Shaihul Islam Ibn Taimiyya ya ce:
Domin karanta cikakken bayani a kan Manufar Makokin Husaini Da ‘Yan Shi’A Sukeyi danna nan.
Domin karanta cikakken bayani a kan Azumin Annabi Dawud (Alaihis salam) domin nan.
Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Gaskiyar Magana A kan Ashura wanda Shehu Mansur Dala ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.
Edita@rumasau-kallamu