Bayani Akan Gyambon Baki {Canker Sore}

0
94

Canker sore: ita ce gyambon baki, ƙurji ne yake fitowa a baki, mafi yawa yana somawa ne da ɗan ƙaramin kurji mai zafin gaske,wanda yakan iya fitowa a kowanne ɓangare na baki.

Alamomin Canker Sore Sun Haɗa Da:
  • Farin ƙurji a baki
  • Ciwo mai tsanani
  • Wani lokocin yana zama ja
  • Yana zuwa da zazzabi
Mutum Zai Iya Ɗaukan Canker Sore Lokocin Mu’amala Ko Kiss?

Mafi yawan canker sore ba ta yaɗuwa ta hanyar mu’amala ko kiss sai dai kaɗan daga cikin su, kuma haka nan yana warkewa da kansa ko ba a sha magani ba cikin kwana uku zuwa huɗu.

Domin karanta Dalilan Da Suke Sanya Mace Rashin Ɗaukar Ciki Danna nan

Me Yake Kawo Matsalar Canker Sore?
  • Ƙarancin sinadaran Vitamin B12, zinc da folate a jiki yakan iya kawo matsalar canker score.
  • Jin rauni a baki lokocin goge baki yakan iya kawo wannan matsalar.
  • Allergy: Idan garkuwar jiki ta ƙyamaci wata ƙwayar bakteria ko abinci yakan iya kawo wannan matsalar.
  • Mata suna fuskantar wannan matsalar lokocin al’ada ta dalilin rikicewar sinadaran hormones.
  • Yawan damuwa (stress) yakan iya kawo wannan matsalar.
  • Ƙwayar cutar bakteria wanda aka fi sani da H-pyloria yana kawo wannan matsalar.
Haka Kuma Wasu Cututtaka Kamar:
  • Chrons disease
  • Irritable bowel syndrome
  • Ulcerative colitis
  • HIV da sauaran su sukan iya kawo wannan matsalar.
Yadda Za a Magance Wannan Matsalar A Lokacin Da Ya Fito:
  • A sa gishiri/manda chokali guda cikin ruwa kofi ɗaya mai zafi a kurkure baki da shi safe da yamma.
  • Ko kuma a sa bakin soda chokali guda cikin ruwa kofi ɗaya mai zafi a kurkure baki da shi a ƙalla sau uku a rana.
  • Bayan haka a samu zuma mai kyau a shafa a  wajen a kalla sau huɗu a rana (zuma na ɗauke da sinadaran kashe ƙwayar cutar bakteria da kuma sinadaran rage kuburi da raɗaɗi).
  • Idan ba a samu zuma mai kyau ba za a iya amfani da man kwakwa shi ma sau uku zuwa huɗu za a shafa a wajen.
  • Za a iya haɗawa da ƙwayar vitamin B complex a ƙalla sau ɗaya zuwa biyu a rana.

Daganan idan babu alamar sauƙi cikin kwanaki biyu zuwa 3 a garzaya zuwa asibiti a tsananta bincike a gano me ya kawo matsalar.

Kada a yi amfani da lemon tsami ana gogawa wajen domin yana tsananta ciwon maimakon warkar wa.

Domin karanta bayani akan Ciwon Kai Na Gado Wato [Migraine] Danna nan 

labarin da ya wuceCiwan Kai Na Gado Wato [Migraine]
Labarin na GabaKa San Dalilin Shanyewar ƙafa Bayan Allura A Ɗuwawo Da Yadda Za A Magance