Kafin na yi nisa cikin wannan littafin, yana da kyau na fara kawo kaɗan daga cikin amfanin sanin kai ga kowanne mutum da yake da mafarkin rayuwa mai kyau.
❖ Sai Ka San Kanka Za Ka Ci Gaba
Babu wanda ya zo duniya da sani, kowa a gidan duniya ya san duk abin da ya sani. Haka nan babu wani da yake samun ci gaba sai ya ci gaba da neman sani, duk wanda ya tsaya da neman sani daga nan rayuwarsa take ƙarewa.
Za ka yi mamaki idan na ce da kai ‘ƴan gargajiyar da muke gani a yanzu masu ilimi ne a zamaninsu, sun ƙi yarda su karɓi ilimin sabon zamanin da suke ciki ne ya sa ake musu kallon ‘ƴan gargajiya. Haka duk wanda ya ƙi ci gaba da neman ilimi zai zama a zamanin gaba.
Mene ne alaƙar ci gaba da sanin kai? Sai ka san kai wane ne da matakan da ka taka na ilimi kafin ka san inda za ka ɗaura. Wanda ya san bai iya turanci ba misali, ba zai yi karambanin karanta littafin turanci mai wahala ba, in kuwa zai karanta da wuya ya tsinci wani abu. Inda iliminka ya tsaya daga nan za ka ɗaura in ka san kanka, in ba ka san kanka ba kuwa za ka iya kamawa daga ko ina sai abu ya yi nisa ka ga ashe akwai wani giɓi a baya da ka baro.
Sanin kai wane ne zai haska maka wuraren da kake da rauni, da wuraren da
Allah ya maka baiwa, hakan zai taimake ka ka mayar da hankali wajen inganta baiwarka sama da ƙorafi a kan gazawarka. Wanda ya mayar da hankali kan inda baiwarsa take shi ne rayuwarsa take ci gaba ba wanda yake ta faɗi-tashi da rauninsa ba.
Hakan kuwa ba lallai ya zo da mamaki ba saboda ƙa’idar ita ce: duk abin da aka mayar da hankali kansa shi ne yake ƙara girma da haɓaka.
❖ Za Ka Dena Haɗa Kanka Da Wasu
Muna rayuwa a wani zamani da bayanai suka yawaita, abubuwan da muke karantawa, kallo da saurare ba ƙaramin tasiri suke mana ba a rayuwa, don haka muke shafe shekaru ma su tsawo a rayuwarmu muna kamanta kanmu da wasu, muna ganin cewa mu ma ya kamata mu yi rayuwa irin yadda suke yi, har ma mukan shiga damuwa a dalilin hakan.
Wanda ya san kansa ba zai tsaya damuwa da kwatanta rayuwarsa da ta kowa ba, ya san me yake so, ya san ina zai je, ya san kuma hanyar da zai kama domin isa wurin, to yaushe zai tsaya tunanin wane ba haka yake rayuwa ba? Sanin kaina ya taimaka min sosai wurin rayuwa irin wacce ta dace da ni, zan ga mutane suna yin abubuwa, amma saboda abubuwan ba su shalle ni ba, ba na fatan na zama su, ina so ni dai kawai na fi yadda na ke a jiya.
❖ Za Ka So Kanka
Son kai yana daga cikin abubuwa mafiya wahala a wannan zamanin, mutum ya ji yana ƙaunar kansa a yadda yake ba tare da jin haushin gazawarsa ba. Yana daga cikin dalilin da ya sa malaman tarbiyya suke ba wa iyaye shawarar su dinga nuna wa yaransu ƙauna, yaba musu in sun yi abin kirki, yaba musu a cikin mutane in sun yi bajinta, ba su ƙwarin gwiwa, rashin gwale su ko disga su, neman shawararsu da ba su dama su yi wasu
abubuwan da kansu (Dr. Aisha Hamdan: Nurturing Eeman in children).
Wanda ba ya son kansa ba zai taɓa tsinana komai ba, zai cika kansa da tunanin gazawarsa da rauninsa dan haka sai wannan ya zama masa matsala. Wanda ya san kansa ya san wuraren da Allah ya fifita shi a kan sauran mutane dan haka zai gode masa kuma zai cigaba da aiki tuƙuru a wannan fannin. Haka nan kuma zai san wuraren da yake da rauni, don haka zai dinga taka-tsantsan a wannan ɓangaren.
❖ Za Ka San Abokanka
Zaɓar aboki wani ɓangare ne mai wahala a rayuwa musamman ga mutane shiru-shiru irina, ba mu da saurin ƙulla abota. Amma duk da haka duk lokacin da muka san kanmu muna samun sauƙi wurin zaɓen aboki. Aboki wani jigo ne na rayuwa, ana tasirantuwa da shi matuƙa, dan haka ake so mutum ya yi taka-tsantsan wurin zaɓar abokai.
Misali, a sanin da na yi wa kaina tunani ya fi aikina yawa, zan daɗe ina tunanin abu har sai na gano ba zai yiwu ba sai na watsar tun kafin na fara, da na ƙulla abota da Mallam
Bahaushe wanda shi kuma yana aikin yana tunanin a lokaci guda, sai ya zama na tasirantu da shi na koyi haɗa dukka biyun ni ma daga gare shi.
Wataƙila da ba mu ƙulla abota ba da wannan littafin ma yana nan zaune cikin tunanina har yanzu. Sanin kanka da sanin manufarka zai sauƙaƙa maka wannan ɓangaren na
rayuwarka, za ka yi abota da wacce ta ku ta zo ɗaya, za ka yi haɗaka da wanda za ku ƙarfafi raunin juna, za kuma ka ci gaba da mutunci da sauran mutane, domin ƙa’idar dama ita ce “ba a ce sai kowa ya zama abokinka ba, amma za ka iya yin mutunci da kowa”.
❖ Za Ka Koyi Yi Wa Mutane Uzuri
Wanda ya san kansa yana saurin sanin cewa mutane kowa da yanayin halittarsa, yadda yake ba haka kowa yake ba, kuma yana lura ya gane ya mutane suke, hakan yana taimakonsa wajen yi musu uzuri.
Kafin na samu haske kan ni wanene wannan yana daga cikin ɓangaren da ya fi wahalar da ni, sai in kasa gane me yasa mutane suke abu iri kaza, ko meyasa suke son su ga ina yin abu iri kaza, ko meyasa su ba sa lura da kaza da kaza.
Wannan Ilimin yana daga cikin abubuwan da suka ɗaga darajar Ma’aiki mai tsira da aminci kan sauran shuwagabannin duniya. In kana bibiyar tarihinsa za ka ga yana bambance sahabbansa ko wurin sanya su aiki yana mai la’akari da yadda suke. In ana buƙatar zafi ba ya neman sayyadina Abubakar, sayyadina Umar yake nema, haka nan in ana buƙatar wata maslaha ko wani abu na sauƙin kai, ba ya neman sayyadina Umar sai dai ya nemi sayyadina Abubakar. A rubuce-rubucena na “Iya ruwa…” na kawo
makamancin wannan misalin.
❖ Za Ka Ɗauki Alhakin Rayuwarka
Sanin kai yana ragewa mutum yawan ƙorafi da ɗaurawa wasu lefin matsalarsa. Wanda ya san kansa zai gwammaci ya mayar da hankali kan abin da zai amfani rayuwarsa sama da ba wa kansa hanzari ba gaira ba dalili. Kai ne ya kamata ka zama a kujerar mai tuƙi a motar rayuwarka ba a kujerar mai zaman banza ba (Sean Covey: 7 habits of highly effective teens).
❖ Rayuwarka Za Ta Yi Sauƙi
In ka san kanka komai zai zo maka da sauƙi. Misalin wanda ya san kansa kamar misalin me yin bulaguro ne, ya san inda za shi, ya san a ina zai samu mota, ya san wacce hanya za a bi. Idan ka san kanka komai za ka san irin na ka, tun daga kan abinci, tufafi, abun hawa, wasa, kai hatta kallo da zuwa wuraren nishaɗi, za ka je ko aikata abin da bai ci karo da kai waye ba ne, balle ka samu ƙunci.
Za ka rage damuwa da kallon da mutane za su maka don kai ka san abin da ba su sani
ba game da kanka (kamar yadda na yi tsokaci a baya, akwai lokacin da dole sai ka saje da su don maslaha).
Kana buƙatar wani cikin waɗannan abubuwan a rayuwarka? In amsarka e ce to mu je zuwa, in kuwa ta zamto a a, ina mai ba ka haƙuri wannan littafin ba na ka ba ne.
Wanan bayanin an ciro shi ne daga littafi mai taken Ka San Kanka wanda AHMAD SANI ya wallafa.
Danna nan don karanta Ka Ɗauka Ka Sani
Edita@rumasau-kallamu










