Amfanin Ƙaho Ajikin Dan’adam

0
32

Ƙaho, abu ne mai asali da tarihi a Musulunci, domin kuwa, tun kafin yin hijira daga Makka zuwa Madina da kamar shekara guda a lokacin da aka yi Isra’I da Mi’iraji da Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) Mala’iku masu yawa sun nusar da Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam)

Da yin amfani da ƙaho da kuma ba shi muhimmancin gaske. Don haka, Manzo (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya yi ƙaho; kuma ya biya wanda ya yi masa ƙahon lada. 

Matsayin Ƙaho:

Ƙaho abu ne da yake da babban  matsayi da gagarumar falala, wanda har hakan ya sa Manzo (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: “Ƙaho ne mafi alherin abin da mutane suke yin magani da shi”. 

Domin karanta Falalar Tafiya Masallaci Danna nan

Ranakun da Ake Yin Ƙaho a Cikin Wata: 

Ga mai son ya ci cikakkiyar gajiyar yi ƙaho, to, ya yi shi a ranar sha bakwai (17) ko sha tara (19), ko kuma ranar ashirin da ɗaya (21) ga watan shekarar Hijira. Manzo (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: “Wanda ya yi ƙaho a ɗaya daga cikin waɗannann ranakun; da izinin Allah ƙahon zai zama maganin duk wata cuta”. 

Ranakun da Ake Yin Ƙaho Cikin Sati: 

Ga mai son ya yi ƙaho a ranakun da suka dace daga cikin ranakun mako, to ya yi a ɗaya daga cikin waɗannan ranaku uku masu zuwa: Ranar Litinin da Talata ko kuna Alhamis.

Ranakun da ba a Yin Ƙaho a Cikinsu a Sati: 

An karɓo Hadisi daga Abdullahi ɗan Umar, Allah ya yarda da su, ya ce: “Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: “Ku nisanci yin ƙaho a ranar Laraba, da Juma’a, da Asabar da kuma ranar Lahadi…”. 

Fiyayyen Lokacin da Ake Yin Ƙaho a Cikinsa:

Yin ƙaho da safe kafin Karin kumallo shi ne fiyayyen lokacin da ake yin ƙaho a cikinsa.

Guraren da Ake Yin Ƙaho

Ana yin ƙaho a sassa daban-daban na jiki, kamar yadda aka rawaito cewa, Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya yi ƙaho a ƙafa da kafaɗu da gyaffan wuya ko mahaɗar wuya da baya, kuma ya yi ƙaho a ka.

Kuma ana iya gudanar da ƙaho a wasu guraren daban daga waɗanda aka ambata a sama, gwargwadon buƙata. 

Domin karanta cikakken bayani a kan Tsayuwar Watan Ramadan danna nan.

Amfanin ƙaho
  • Ƙara hankali.
  • Ƙara kaifin hadda.
  • Maganin cututtukan jiki.
  • Rage yawaitar jini don daidaita gudanarsa.
  • Rage maiƙon cikin jini.
  • Maganta matsanancin ciwon kai.
  • Rage yawan majinar jiki.
  • Ƙara wa sinadaran yaƙar cututtukan jiki ƙarfi.
  • Raba jiki da guba.
Domin Dauko Cikekken Littafin Danna nan 
labarin da ya wuceMuhimman Abubuwan Da Suke Inganta Lafiya
Labarin na GabaAbubuwan Da Suke A Farkon Aure
wikiHausa
wikiHausa kundin ilimi (insakulofidiya) ce da ke ilimantar da jama'a yara da manya da maza da mata wajen samun ilimi a saukake, cikin harshen Hausa.