Tabbas saduwar aure a tsakanin namiji da mace tana da matuƙar muhimmanci a zamantakewar aure. Duk da kasancewar ba ita kaɗai ba ce ta ke samar da morewar zaman aure. Saduwa ita ce a kan gaba.
Wannan yana nufin cewa ko da mace tana da ladabi da biyayya, iya magana, iya girki, iya kwarkwasa, iya kwalliya, tsabta da sauran abubuwan ƙayatarwa na zaman aure, to, dukkan su ba su kai muhimmancin saduwa ba a wurin mijinta.
Haka nan kuma, koda namiji yana da ƙoƙarin samar wa matarsa da abinci da abin sha, sutura, wurin zama, kiwon lafiya, tsare mutunci, tausayawa, kyautatawa da sauran abubuwan ƙayatarwa na zaman aure, to, dukkansu ba su kai muhimmancin saduwa ba a wurin matarsa. Bisa wannan dalilin ne maza su ke jajircewa wajen ganin cewa sun gamsar da matansu ta fuskar jima’i.
ABIN DA AKE NUFI DA GAMSAR DA JUNA WAJEN SADUWAR AURE (SEXUAL SATISFACTION)
Masana a fannin lafiya (medical health), da na addinin Musulunci (Islamic clerics), da na halayyar ɗan-adam (psychologists) sun kai sun komo ga me da ma’anar gamsar da juna a wurin saduwar aure. Amma duk bayanansu sun tattara ne a kan cewa ma’anarsa ita ce, “A samu natsuwar da za ta gusar da duk wata sha’awa bayan an gama saduwar, sai kuma wani lokaci idan buƙatar hakan ta taso”.
Da wannan ne wasu da yawa daga cikin mazajenmu su ke ɗaukar cewa mutum ba zai iya gamsar da iyalinsa ba sai:
- Idan yana da al’aura mai kauri, ko tsawo, ko kuma duka biyun.
- Idan yana daɗewa wajen saduwa.
Hakan ne ya bai wa wasu kamfanoni masu sarrafa magungunan Bature, da kuma masu maganin gargajiya damar samar da magunguna iri-iri waɗanda aka ce suna bai wa namiji ƙarfin gamsar da iyalinsa yadda ya kamata. Abin ya yi yawa sosai, ta yadda masu waɗannan magunguna suka cika chemists, da kasuwanni, tituna, da tashoshin mota suna cin karensu babu babbaka.
RABE-RABEN MAGUNGUNAN BATURE NA ƘARA KARFIN NAMIJI
Magungunan sun kasu kamar haka:
- Kwayoyi (drugs): waɗannan su ne magungunan da ake sha da baki, kuma suna da yawa. Sun haɗa da Viagra, VigRX Nitric Oxide , TestRX, GenF20 Plus, Semenax, ProSolution Plus, VigRX Plus, Extenze, da sauransu.
- Mayuka (creams): waɗannan su ne magungunan da ake shafawa. Su ma suna da yawa, kamar Maxman Delay Sex Cream, Viamax Maximum Gel, TITAN Gel, Doc Johnson Power Plus Delay Cream, Man1 Oil Penile Health Cream, Lavenda Massage Oil, da sauransu.
- Allura (injection): waɗannan su ne magungunan da ake yin allura da su. Su ma suna da yawa, kamar Papaverine, Prostaglandin E1 (PGE1), Phentolamine, Alprostadil, Trimix, da sauransu.
- Tiyata (surgery): wannan ita ce aikin yanka mazakuta da ake yi a ɗakin tiyata domin a ƙara mata tsawo ko kauri (penile augmentation surgery) ta hanyar sanya wata roba mai kama da jijiyoyin mazakuta (medical grade silicone). An fi yinta a ƙasashen Turawa, kuma tana da tsada sosai.
- Jike-jiken magungunan gargajiya (herbal concoctions): wannan shi ne ya fi yawa a cikin al’umarmu. Su ma akwai na sha akwai kuma na shafawa. Masu ilmin kimiyya ba su cika yarda da tsabtar waɗannan magungunan ba, haka kuma ba su yarda da sahihancin ƙa’idar amfani da su ba (dosage).
TASIRIN MAGUNGUNAN ƘARA ƘARFIN NAMIJI
Masu amfani da waɗannan magunguna suna ganin tasirinsu. Hakan ba ya rasa nasaba da abubuwan da ake haɗa su da shi, kamar ginkgo biloba, ginseng, DHEA, horny goat weed, fenugreek, maca da sauransu. Wasu chemicals ne wasu kuma ana tatso su ne daga tsirrai, sa’annan suna sanya ƙaruwar zubar sinadarai (hormones) a cikin jiki ne. Amma a gaskiya sakamakon binciken kimiyya da yawa ya tabbatar da cewa daɗewa ana amfani da su yana haifar da illa ga lafiyar mutum. Bayan wannan kuma, idan jikin mutum ya saba da su, to, zai yi wahala ya iya saduwa da matarsa in baiyi amfani da su ba. Assha! Kaga kenan matsala ta auku.
SIRRIN GAMSAR DA MACE WAJEN SADUWAR AURE
Alqur’ani mai girma ya gama mana komai, domin ya sanar da mu yadda za a gamsar da mata wurin saduwa:
“نِسَاؤُكُمْ حَرْثٌ لَكُمْ فَأْتُوا حَرْثَكُمْ أَنَّىٰ شِئْتُمْ ۖ وَقَدِّمُوا لِأَنْفُسِكُمْ ۚ وَاتَّقُوا اللَّهَ وَاعْلَمُوا أَنَّكُمْ مُلَاقُوهُ ۗ وَبَشِّرِ الْمُؤْمِنِينَ“
“Matanku gonakinku ne, ku shiga gonakinku ta yadda ku ke bunata, kuma ku yi wasanni da su (a lokacin da za ku sadu da su)”, Baqarah: 223.
Kenan idan mutum ya yi wasanin motsa sha’awa sosai kafin ya fara saduwa da iyalinsa, to, insha-Allahu zai gamsar da ita. Wasu suna yin kuskuren fahimtar cewa daɗewa ana saduwa shi ne kwazo da burgewa. A likitance wannan ba gaskiya ba ne, domin ana so ne saduwa ta zama daga minti 3 zuwa 17. Idan ta kai minti 20, to, tayi yawa domin zata iya sanya ni’imar matar ta ɗauke, daga nan sai ta fara jin zafi, kila ma a yi mata rauni. Amma a lura ba wai ina nufin dole kada a wuce abinda na faɗa ba ne, domin wani yana iya yin minti 60 ma ba tare da matar ta tsawwala ba.
MENE NE ABIN YI?
- Matsalar ƙanƙancewar gaba gaskiya ce. Idan mutum yana da ita, to, ya kamata ya tuntuɓi likita, domin a ɗora shi a kan maganin da ya dace, maimakon saye da kuma amfani da magunguna barkatai, waɗanda idan illarsu ta taso, bai san yadda zai magance ta ba.
- Idan ba ya zama dole ba, kada ka saba ma madam da daɗewa ana saduwa, domin idan ka daina daɗewa daga baya, to, akwai matsala fa.
- Ka ƙarfafa wasanni kafin ka fara, kamar yadda Alƙur’ani ya yi umarni.
WalLahu A’lam
Domin karanta yadda ake gyara soyayya ko Yadda Za Ki Ja Hankalin Mijinki ko yadda ake wa maigida lokacin al’ada