Addu’ar Da Ake Yi Ga Mamaci A Cikin Sallar Jana’iza

0
855

Addu’a Ga Mamaci – “Allaahummagfir lahu warhamhu, wa aafihi; wa afu anhu wa akrim nuzulahu wawassi’i mudkhalahu, wagsilhu bil maa’i wassalji wal baradi; wa naƙƙihi minal khaɗaayaa kamaa naƙƙaitas saubal abyadha minad danasi; wa abdilhu daaran khairan min daarihi wa ahlan khairan min ahlihi wa zaujal khairan min azabil ƙabri wa azabin naari”.

Addu’a Ga Mamaci – {Ya Allah! Ka yi masa gafara, ka ji ƙansa, ka amintar da shi daga bala’i, ka yi masa rangwame; kuma ka girmama liyafarsa, ka yalwata mashigarsa (ƙabarinsa); kuma ka wanke laifuffukansa kamar yadda kake tsaftace farar tufa daga dauɗa, kuma ka musanya masa gidan da ya fi gidansa alheri; da mata da ta fi matarsa alheri, kuma ka shigar da shi Aljannah , ka tsirar da shi daga azabar kabari da azabar Wuta}.

Allaahummagfir li hayyinaa wa mayyitinaa wa shaahidinaa, wa gaa’ibinaa, wa sagiirinaa wa kabiirinaa, wa zakarinaa wa unsanaa. Allaahumma man ahyaytahu minnaa fa’ahyihi alal Islaami waman tawaffaitahu minnaa fatawaffahu alal imani, Allaahumma laa tahrimnaa ajrahu walaa tadhillanaa ba’adahu”.

{Ya Allah! Ka gafarta wa rayayyunmu da matattunmu, da waɗanda suke halarce tare da waɗanda ba sa nan; da yaranmu da manyanmu, da mazajenmu da matayenmu. Ya Allah! Wanda ka rayar da shi daga cikinmu, to ka rayar da shi a cikin Musulunci; wanda kuma ka ɗauki ransa, to ka ɗauki ransa a kan imani. Ya Allah! Kada ka haramta mana ladan (haƙurin rashinsa), kada kuma ka ɓatar da mu bayansa}.

Allaahumma inna fulaana bin fulaanin fii zimmatika, wahabli jiwaarika, faƙihi min fitnatil ƙabri wa azabin naari, wa anta ahlul wafaa’i wal haƙƙi fagfir lahu warhamhu innaka antal gafuurur rahiimu”.

{Ya Allah! Haƙiƙa wane ɗan wane yana cikin alƙawarinka (na kiyayewa) da amanarka; don haka ka tserar da shi daga fitinar ƙabari da azabar wuta. Kai ne ma’abocin cika alƙawari da gaskiya; ka gafarta masa, ka ji ƙansa. Haƙiƙa kai, kai ne mai yawan gafara, mai yawan jin ƙai}.

Allaahumma abduka wabnu amatika taaja ilaa rahmatika, wa anta ganiyyun an azabihi, in kaana muhsinan fazid fii hasanaatihi wa in kaana musii’an fatajaawaz anhu”.

{Ya Allah! Bawanka kuma ɗan baiwarka ya buƙatu ga rahamarka, kuma Mawadaci ne ga barin azabarsa. Idan mai kyautata aiki ne, ka yi ƙari a cikin kyawawan ayyukansa; idan kuma mai mummunan aiki ne, ka yafe masa}.

Domin karanta cikakken bayani a kan Addu’a A Yayin Da Ake Rufe Idanun Mamaci danna nan.

Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Addu’ar Samun Lafiya Ga Cututtuka danna nan.

Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Garkuwar Musulmi Ta Addu’o’i Daga Alƙur’ani Da Sunna; wanda Sheikh Sa’id Ibn Ali Ibn Wahf Al-Kahdani ya wallafa shi; Domin karanta cikakken Littafin Danna nan.

labarin da ya wuceAddu’a A Yayin Da Ake Rufe Idanun Mamaci
Labarin na GabaYadda Ake Addu’ar Ta’aziyya
wikiHausa
wikiHausa kundin ilimi (insakulofidiya) ce da ke ilimantar da jama'a yara da manya da maza da mata wajen samun ilimi a saukake, cikin harshen Hausa.