Abubuwan Da Suka Shafi Idi

0
6

Da farko dai ana son mutanen da za su je Idi su zamto sun tsabtace jikinsu sannan su sanya sababbin tufafi ko kuma mafi kyau daga cikin kaya, sannan su tafi a ƙasa (ba a kan abin hawa ba). Domin sayyidina Aliyu (R.A) yace: “Yana daga cikin sunnah tafiya idi a ƙasa”. Tirmizi

Game da mata kuma an halarta musu zuwa idi saboda Hadisin Ummu adiyya (R.A) tace: Manzon Allah SAW ya kasance yana umurtar mu da zuwa Idi mu da bayinmu da masu haila a cikin mu domin mu halarci wannan alheri da kuma addu’ar Musulmai, amma masu haila an umurce su da su nisanci wurin da ake yin sallah. Bukhari da Muslim.

Saboda haka ya halatta mata su je idi, amma fa su ji tsoron Allah domin neman dacewa.
sannan ana buƙatar mai zuwa idi ya rinƙa yin kabarbari da hailala tare da Hamdala Kamar haka:

ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, LA ILAHA ILLALLAHU, ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR WA LILLAHIL HAMDU.

Ba a son ana tafiya Idi ana Surutu. An tambayi Anas Bn Malik (R.A) yaya kuke aikatawa lokacin Manzon Allah (SAW)? Sai yace: “Mai ambaton Allah ba a hana shi; sannan mai kabbara na kabbara ba mai hana shi”. Bukhari.

Bayan haka, ana son idan an idar da Sallah mutum ya saurari Huɗuba (ba wai daga idar da sallah mutum ya tafi gida ba). Sannan kuma ana so a cigaba da wannan zikiri da kabarbari har tsawon kwana Uku (3) saboda faɗin Manzon Allah SAW: “Kwanaki uku na sallah kwanaki ne na ci, da sha, da kuma ambaton Allah (SWT)” Wanda ya je filin Idi ba zai yi nafila ba saboda faɗin Abdullahi Ɗan Umar yace Manzon Allah SAW da Sayyidina Abubakar, da Sayyidina Umar suna yin sallar Idi kafin Huɗuba. Bukhari da Muslim.

Sannan kuma ya tabbata a Hadisi Manzon Allah SAW yana yin Sallar Idi raka’a biyu (2). Sannan ba ya yin wata sallah kafin ko bayan Sallar idi. A nan za mu fahimci cewa; ba a sallar Nafila kafin idi ko kuma bayanta.

HANI GA YANKE FARCE KO CIRE GASHI GA WANDA ZAI Yl LAYYA

Ana son wanda zai yi layya kada ya gyara gashinsa da kuma yanke farcensa yayin da watan sallah (Dhul-Hajj) ya kama domin an samu Hadisi daga Manzon Allah SAW yace: “Idan kuka ga watan sallah ya kama (Dhul-Hajj) sannan ɗayanku zai yi layya to kada ya cire gashin kansa” Wannan Umurni ne shi ma yana daga cikin nau’in ibada.

Domin karanta Abin Da Ya Shafi Yanka danna nan

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceAbin Da Ya Shafi Yanka
Labarin na GabaMai Jin Harshe Ɗaya
Faruq Adamu
Sunana Faruq Adamu. Mu'assasin Gidauniyar Less-Privileged and Almajiri Initiative. Gidauniya Mai Rajin Taimakawa Mabukata, Dakuma Inganta Tare da Zamanantar da Tsarin Ilimi Na Almajirci a Nijeriya.