Abubuwan Da Ke Sa Kishiyoyi Shiri Da Zaman Lafiya

0
19

Haƙuri da kau da kai game da kura-kuren kishiya; shi ne mafi girman abubuwan da suke wanzar da zaman lafiya a tsakanin kishiyoyi.

Ga abin da Allah (Subhanahu wata’ala) ya ce: a game da muhimmancin haƙuri. Ma’ana “kayi haƙuri kan duk sha’anin da ya same ka, haƙiƙa yin hakan na daga cikin muhimman al’amura” 

Watsi da tsegungumi tare da nisantar munanan zace-zace marasa dalilai game dakishiya, shi ma yana daga cikin abubuwan da suke inganta zamantakewar kishiyoyi, kuma dimantar kulawarmu da hakan shi zai ba mu damar aiki da tarbiyyar da addininmu ya ɗora mu a kai ta kyautata wa junanmu zato. 

Don karanta Ma’anar Aure danna koren rubutu

Allah Ta’ala yace: 

Ma’ana “Ina ma dai lokacin da kuka ji (mummunan zaton da aka yi wa Aisha) muminai maza da muminai mata sun zatar wa kawunansu alheri, kuma su ce wannan ai ƙage ne bayyananne”. 

Kuma an karɓo hadisi daga Abu Huraira Allah ya yarda da shi ya ce, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: “Na hana ku mummunan zato, haƙiƙa, mummunan zato shi ne mafi ƙaryar zance”. 

Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi. 

Kyautata wa kishiya da kuma mai da komai ba komai ba , dalili ne ƙwaƙƙwara da yake tabbatar da zaman lafiya tsakanin kishiyoyi. 

Don karanta Ma’anar Aure danna koren rubutu

Imamul Bukhari da Muslim sun rawaici hadisi da aka karɓo daga Aisha Allah ya yarda da ita ta ce: “yayin da sauda ‘yar Zam’a (matar Annabi) ta manyanta sai ta bai wa Aisha ranar kwananta, sai Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya zama yana raba wa Aisha kwanan Sauda. (ƙari a kan nata kwanan). Wannan kyakkyawan misali ne da yake sanar da matanmu yadda ya kamata su zauna da kishiyoyinsu. 

Domin karanta Neman Aure Bisa Koyarwar Musulunci Danna nan

labarin da ya wuceDuhun Kan Mace Mai Gaba Da Kishiya
Labarin na GabaShin Ko Ya Halatta A Je Wajen Boka Ko Ɗantsubbu (Mai Duba) Domin Sihirce Kishiya?