Abubuwan Da Ba Su Inganta Ba Game Da Ashura

0
29

Bayan faruwar wannan abin takaici na kashe Husaini (R.A) a ranar 10 ga Muharram shekara ta 61 labarai da hikayoyi masu ban mamaki da ake danganta su ga Husaini da Yazid da Banu Umayya da ranar Ashura da ƙasar Karbala da kusan duk wani abu da yake da alaƙa da wannan abu. 

Sai waɗannan labarai da jin su ba sai an faɗawa mai imani da ilmi ba cewa waɗansu masu son zuciya da fitina ne suka ƙirƙiro su, domin cimma buƙatunsu, kuma sun ci gaba da ƙirƙirarsu da yaɗa su har zuwa yau. Sannan kuma ga ibadu na bidi’a jingim da aka raba da watan da ranar waɗanda Allah Ta’ala da Manzonsa da Ahlul baiti, ba su yarda da su ba. 

Wannan abu ya faru a ɓangarorin Sunna da Shi’a baki ɗaya, kuma malamai musamman daga ɓangaren Sunna sun yi bayanai kan rashin ingancin da bidi’ancin waɗannan labarai da ibadu. Ga kaɗan daga cikin su: 

Domin karanta Neman Aure Bisa Koyarwar Musulunci Danna nan

1- Rana ta kisfe a wannan yini har sai da aka rinƙa ganin taurari da rana gagal. 2- Sama ta yi jawur, ba a taɓa ganin ta yi ja ba sai a ranar. 

3- An yi ruwan jini daga sama. 

4- Duk dutsen da aka ɗaga sai anga jini a kai. 

5- Garuka sun yi tayin kukan jini lokacin da ake wucewa da kan Husaini (R.A). 6- Ƙasa ta yi duhu tsawon kwana uku. 

7- Tarurukan warsu da za’afaran sun rinƙa ƙona duk wanda ya shafa su. rinƙa ƙona naman raƙuman da aka kama daga jama’a. 

8- Hussaini bai ji ciwo ba. Saboda ya ji ɗaci kamar guna. 

9- Taurari sun yi ta yin karo da junansu. 

10- An yi wa ƴaƴa da matan Husaini zigidir, an ɗora su a kan raƙuma, an kewaya da su cikin gari, ana yi musu átire, wai don su sami sutura, sai tozo biyu ya ɓullo a kan rakuman, wai daga nan aka fara samun raƙuma masu tozo biyu. 11- Wai Yazidu ne ya ba da umarnin a kashe Husain.

12- Wai an kai masa kan Husainin ya caccaka kara a bakinsa. 13- Wai Husaini bai taɓa shan nono ba, harshen Annabi(S.A.W) ko yatsansa ya ke tsotsa. Kansa ya yi magana har ya karanta Kur’ani 

Don karanta Ma’anar Aure danna koren rubutu

14- Dukkanin halittu sun yi kukan mutuwarsa. 

15- Aljanu ma sun yi ta kururuwa. 

16- Dukkan annabawa sai da suka kai masa ziyara. 

17- Duk kukan da tattabaru suke yi, a kan Husaini suke kuma la’antar makasan sa suke yi. 

18- A da mujiya tsuntsuwar gida ce kuma da rana take harkokinta, amma tun daga ranar da aka kashe Husaini ta koma daji take yin azumi da rana da daddare kuma tana kuka tana la’antar makasan Hussaini 

Domin Karanta Cikekken Littafin Danna nan

ƘASAR KABARIN HUSAINI 

Ita kuwa wannan ƙasa, an faɗi falala da maganin da take yi wanda sun tsallake hankalin mai hankali da ilmin mai ilmi, ga kaɗan daga cikinsu: 

21 Sallar da aka yi a kan wannan ƙasa tana keta shamakai bakwai (Karbabiyya ce). 22 Duk wanda ya ci wannan ƙasa da niyyar neman waraka kamar ya ci naman imamai ne. 

23 Duk Istigifari ɗaya da aka yi da carbin da ya nesantar da saba’in, in kuma ya riƙe shi kawai to duk kwayar carbi ɗaya, za a rubuta masa lada bakwai na Istigifari. 

24 In aka goga ta a dadashin jariri sabuwar haihuwa(Tahniƙi) zai samu aminci da kariya. 

25- In aka sa ta a cikin kabari, musamman a yiwa mamaci matashi da ita, ba shi ba azabar kabari. 

26- Yawo da ita yana maganin tsautsayi da asara, da dukkan wani abin tsoro. 

27- Tana maganin kowane irin ciwo sai dai mutuwa. Sharaɗan yin amfani da ita su ne: 

  1. a) Imani da cewa ita ce take warkarwa ko amfanarwa. 
  2. b) Karanta addu’o’i (sun faɗe su a littafinsu). 
  3. c) Imani da son haƙiƙanin Husaini. 
  4. d) Ka da ya ci ƙasar don sha’awa kawai, a’a sai dai don neman biyan buƙata! e) Ka da ya ci don buƙatar kar ya mutu!

f ) Ka da ya ci sama da girman gurjiya. 

  1. g) A tabbatar daga haramin Karbalar aka ɗebo ƙasar, wato gaba ko zirfi saba’in daga kabarin, ko mil ɗaya ko huɗu ko goma , kai duk ma gewayen Kubbar da masallacin! 
  2. h) A kula da ita sosai, a ɓoye ta don ka da aljanu da masu zunubai su taɓa ta, ta lalace albarkarta ta washe. 

ZIYARTAR KABARIN HUSAINI DAKE KARBALA

A gaskiya abubuwan da ake faɗa game da wannan, ba na jin akwai wani jahilin musulmi da zai yarda da su, ballantana ya ɗauke su a matsayin addini amma kuma hakan ta faru! Allah ka shiryi bayinka tafarki madaidaici. Ga kaɗan daga cikin waɗannan maganganu: 

28- Ziyartar kabarin Hussaini daidai yake da aikin Hajji uku tare da Manzon Allah (S.A.W). 

29-Ziyartarsa daidai take da aikin Hajji sau ɗari. 

30- Wanda ya ziyarce shi, za a rubuta masa ladan Hajji dubu karɓaɓɓu, za a yafe masa dukkan zunubai. 

31- Ƙasar Karbala ta fi ƙasar Harami falala. 

32- Harami amintacce da shekara dubu ashirin da biyar kafin a halicci Makka! Sai da aka halicci Karbala. 

33-Ba don Karbala ba, da ba a halicci Ka’aba ba! 

34 Sallah raka’a ɗaya a Karbala daidai take da Hajji dubu, da Umra dubu da ƴanta bawa dubu da yake dubu tare da Annabi(Manzo). 

Domin Karanta Cikekken Littafin Danna nan

35- Zuwa Karbala ya fi tsayawa a Arafa, saboda duk taku ɗaya, ladan aikin Hajji za a bai wa mutum! To wannan abu in haka ne, wane ne zai je wani aikin Hajji ballantana Umra? Ka ga dai so ake a hana mutane zuwa aikin Hajjin. 36- Ziyartar kabarin Husaini ranar Ashura wai tana: 

  1. a) Sa wanda ake bi bashi ya sami abin biya. 
  2. b) Wanda ba ya haihuwa ya samu haihuwa. 
  3. c) Mutum zai san gaibu. 
  4. d) Maganin kowace cuta. 
  5. e) Warware manyan matsaloii masu rikitarwa.
  6. f) Warware matsaloli na yau da kullum. 

37- Yana daga ladaban ziyarar bayan karanta wata Mashahusiyar addu’a a yi tsinuwa ga magabata (sahabbai) da waɗanda suka biyo bayansu har zuwa ranar alƙiyama sau ɗari ba ɗaya a ce: “Alahummal anhum jamian! (Ina lillahi wa inna ilaihi rajiun). 

Wanda ya yi kuka ranar Ashura ko ranar da wata musiba ta sami Ahlul baiti, ko ya ji ko ya tuna ya yi kukan, komai ƙanƙantar hawayen da ya zubar, zai tashi matsayi ɗaya da imamai ranar ƙiyama! Kuma ba zai yi kuka ba ranar, kuma zuciyarsa ba za ta mutu ba, ka ji fa daga kuka ka sami matsayin Imamai a lahira! 

38- Wanda ya yi wa Hussaini waƙa ya sa mutum ɗaya zuwa hamsin kuka, koda kuwa kukan ƙarya ya yi to shi ɗan aljanna ne! 

39- Dangane kuwa da zanga-zanga da sanya baƙaƙen kaya da wasan kwaıkwayo da sauransu a Ashura malamansu, Muhammad Bakir Annasriy ya yi ƙoƙarin kawo falalar yin waɗannan ranar amma labarai kawai ya kawo ba aya ba hadisi babu maganar Imam ko ɗaya, shi yasa ba zan kawo labaran ba, sai dai mai son jin ƙwaƙwaf sai ya duba littafin shafi na 233 273. Majnunu Ali duba littafin shafi na 233 273. Majnunu Ali Muhammad!. 

Domin Karanta Cikekken Littafin Danna nan

labarin da ya wuceMatsayin Azumin Ashura A Wurin Ahlil Baiti (R.A)
Labarin na GabaHadisai Na Ƙarya Da Raunana A Kan Ashura