Abubuwa Da Ya Kamata Mace Ta Kiyaye Lokacin Al’ada

0
108
  • A kiyaye barin audiga (pad) ta dade a jiki,koda ba jinin  ta kiyaye amfani da da ruwan kankara ko ruwan sanyi lokacin al’ada sabida amfani da ruwan kankara yakan sa jini ya daskare a mahaifa bazai fita gabaki daya ba,bayan shekaru 5 zuwa 10 sai yakawo ciwon daji na mahaifa
  • Ta kiyaye saka shampoo a kanta lokacin al’ada sabida a wannan lokacin kofar gashi a bude take kuma shigan shampoo kofar gashi yana kawo ciwon kai mai tsanani.
  • Ba’aso mace tayi amfani da gurji (cucumber) lokocin al’ada sabida akwai sinadarai a jikinta wanda zai iya hana jinin yafita gabaki daya,wanda daga karshe zai kawo ciwon daji na mahaifa.
  • Koda wasa kada kiyarda a daki cikin ki,kuma ki kiyaye duk abinda zai daki cikinki sabida dukan ciki a wannan lokocin zaijiwa mahaifa rauni wanda daga karshe zai zama ciwon daji, kuma yana kawo aman jini lokoci guda.
  • A kiyaye amfani da  gishiri mai yawa amfani da gishiri (manda) dayawa yana kawo yawan zubar da jini kuma yakan sa ruwa ya taru a mahaifa.
  • A kiyaye amfani da ƙwaƙwa (coconut) lokacin al’ada sabida tana tsananta alamomin al’ada kamar ciwon ciki da sauran su.
  • A kiyaye amfani da barasa (giya) lokacin al’ada duk da bincike ya nuna tana rage radadi lokacin al’ada,to akwai matsaloli dayawa da zai iya kamuwa da su sosai kada ayarda abar pad a jikinki samada awa 3-4 lokacin al’ada.
  • A kiyaye amfani da tabar sigari,dukkan mu munsani tabar sigari tana da illa ga lafiyar jikinmu bayan haka bincike ya nuna amfani da tai lokacin al’ada tana saka alamomin suyi tsanani.

Abubuwa Wanda Ake Tunanin Za Su Iya Kawo Jinkirin Al’ada:

  •  Juna Biyu
  • Shayarwa
  • Shigan ƙwayar cuta
  • Magungunan tazarar haihuwa
  • kunburin kwan mace (ovarian cyst)
  • Rashin kwanciyar hankali (Stress)
  • Motsa jiki mai ta da hanakali.
  • Rashin samun lafiyaiyan abinci da isheshshen
  • Cututtuka kamar zazzabin typhoid.
  • Matsalar sinadaran hormones.
  • Magunguna irinsu maganin cancer.

Domin karanta Yadda Za Ki San Kanki Kafin Ki Yi Aure Danna nan

labarin da ya wuceMatsalar Zubar Yawun Bacci
Labarin na GabaAlamomin Cancer