Guraren Da Aljanu Sukafi Zama

0
23

A wajen zama mun bambanta, sai dai da yawan mu muna rushe musu wurin zamansu sannan mu gina namu, kuma muna sare musu wajen zamansu mu dasa namu.

Aljanu sun fi zama a cikin daji, saman dutse, saman ɗaki, cikin bola, cikin garken raƙuma, jikin shuri da dai sauransu. Da yawa akwai hatsari da mutum ya ga an share fili a daji ya tsugunna ya yi fitsari ko kashi.

Akasarin irin wajejen nan aljanu ne suka yi jinya suka warke suka tashi a wajen don haka sai a kiyaye. Akwai waɗanda suke mu’amalantar mu a cikin gida, waɗanda su suke zama a cikin gida kamar yadda muke zama, haka kuma wasu daga cikinsu a hanya muke gamuwa da su, su rako mu har gida. Shi yasa musulunci ya koyar da mu addu’ar da za mu yi in za mu shiga gida da in za mu fita. Ya kamata in za ka bar gida sai ka ce;

“Bismillahi tawakkaltu alallahi wala haula wala ƙuwwata illa billah, allahumma inni a’uzhu bika an adilla aw udilla, aw azilla aw uzalla, au azlima aw uzlama, aw ajhala aw yujhala alayya”

Sannan in za ka shiga gida sai ka ce;

“Bismillahi walajna, wa bismillahi kharajna wa’alal lahi rabbana tawakkalna”

Amfanin addu’ar nan shi ne ko da aljanu sun biyo ka gida idan ka karanata wannan addu’ar za su ga babu ƙofa a gidanka, ba wurin zama sai su koma. Idan kuma ka yi sakaci wurin karanta ta, to za ka ga ka shiga gida cikin damuwa, da ƙunan rai da tashin hankali da jin haushin mutanen gidan.

Daga lokacin shi kenan sun sami abinda suke so, ka yi ta faɗa da mutanen gida. Shi yasa musulunci ya koyar da mu hatta abinci in za ka ci ka ce bismillah, Allah ba zai ba su ikon su sa hannu su ci ba. In kuma ka gama cin abincin sai ka karanta wannan addu’ar;

“Allahumma barik lana fi hi wa ta’amna khairan minhu”

Idan ka yi wannan addu’ar Allah zai ba ka lada sannan kuma ya sa wa abincin da za ka ci albarka.

Hatta kaya idan za ka cire, musulunci ya koyar da mu addu’a da ya kamata ka yi don ka samu kariya daga sharrin aljanu da sheɗanu. Don haka in za ka cire kayanka ka ce “bismillah” Allah zai rufe idanun aljanu ba za su ga tsiraicinka ba.

Haka ɗakin da ya dade a rufe hatsari ne a shiga ba tare da an yi addu’a ba. Ko da shimfiɗa ce aka gyara ta domin a kwanta, musulunci ya koyar da mu ka karkadɗeta sau uku sannan ka yi addu’a ka kwanta. Kuma mu kiyaye zama a kofar ɗaki don wannan ma wurin zamansu ne.

Sai a kiyayi zubar da ruwan zafi a makwarara, saboda nan ma wajen zamansu ne. Kuma a kiyayi zama a cikin ɗaki mai duhu da kuma yin surutu a bayi da zama kai ba ɗankwali da jiki a bude. Sai mu raba kanmu da yawan kalle-kalle marasa amfani ko jin kade-kade.

Sannan uwar gida ki tattare kayanki da zarar magariba ta doso kai, ki killace yaranki, ki hana su zama ba riga, sannan a rufe kwanukan da aka ci abinci har dai za a bar su a waje. Wannan duk musulunci ya koyar da mu ne don kulawa da kanmu.

Domin karanta cikakken bayani akan Yadda Kalolin Aljanu Suke danna koren rubutun nan.

Domin karanta cikakken bayani akan Yadda Ake Addu’ar Samun Lafiya Ga Kowane Irin Ciwo danna koren rubutun nan.

Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu

labarin da ya wuceHanyar Ƙona Aljani A Jikin Mutum
Labarin na GabaYadda Ake Warkar Da Kambun Baka Ko Maita