Yadda Za Ki San Kanki Kafin Ki Yi Aure

1
884

Mata – Akan so kowacce mace a ce ta san kanta, budurwa ko matar aure ko kuma bazawara, wannan shi ne zai sa ki sami daraja a wajen mijinki.

Da yawan mata, sun kasu gida huɗu kuma kowacce da hanyar da take bi gurin ta ga ta samu daraja a wajen mijinta; wata hanyar mallaka za ta bi, wata kuma hanyar gyaran jiki; wata kuma hanyar biyayya da kyautatawa, wata kuma wajen kwanciya.

Ba laifi ba ne, in kin bi hanyoyi uku cikin huɗun nan; wajen ki ga kin samu daraja, kin zama ‘yar lele a wajen mijinki. Bin hanyar mallaka ita ce babbar illa ga mata; don kuwa ita ce ba ta lasting (ƙarko) don tana da iyaka, ba ta ɗorewa.

Da yawa iyayenmu mata; idan za su aurar da yaransu mata, sun fi damuwa da shirin kayan ɗaki ko kuma shirye-shiryen kayan anko da irin fitar da amarya za ta yi; har ya rage wata uku kafin biki za ki ga ana koya wa ƙawayen amarya irin rawar da za su yi, don su burge ango da abokansa.

Amma kaɗan ne cikin iyayenmu mata da suke bincikar amarya kama daga lafiyar jikinta da gyarensa; don ta burge mijinta in ta je gidansa.

Kaɗan ne cikin ‘yan matan da idan suna da matsala suke iya bayyana ta ga iyayensu; wasu yaran sukan ɓoye ta har suje gidan miji da ita.

Shi yasa da zarar mace ta yi aure sai ka ga kwana kaɗan namiji ya fara juya mata baya; ya fara hantarar ta, yana mata wulaƙanci, don kuwa ya rasa gamsuwar da yake son samu a wajen matarsa; don haka, iyaye ku kula sosai ku rinƙa jan ‘ya’yanku mata a jiki sosai, kuna sanin halin da suke ciki.

Wannan shi ne zai ba ku dama ba za su rinƙa boye muku sirrinsu ba. Sanin halin da suke ciki shi ne zai ba ku damar ɗaukar mataki kafin ku kai su gidan miji.

Mata na cewa, “Aure yaƙin mata” .

Ki zauna da ‘yarki budurwa ki tambaye ta duk abin da yake damun ta da abin da take ji a jikinta da abinda take gani a gabanta kafin ki kai ta gidan miji.

Kar ki kai ta gidan miji da cuta a jikinta, ya kasance shi kansa mijin ya tsani yarinyar ke kuma yana jin haushin ki.

Domin karanta cikakken bayani akan Yadda Za ki Gyara Kanki danna koren rubutu.

labarin da ya wuceYadda Za Ki Gyara Kanki
Labarin na GabaYadda Ake Addu’ar Bushewar Zuciya
wikiHausa
wikiHausa kundin ilimi (insakulofidiya) ce da ke ilimantar da jama'a yara da manya da maza da mata wajen samun ilimi a saukake, cikin harshen Hausa.