Siffofin Masu Bayar Da Tarbiyya

0
556

Masu hikima suna cewa: “In mutum ya ce zai ba ka riga, to ka dubi ta jikinsa. kuma “Wanda ba shi da abu ba zai iya bayar da shi ba.”

A kan haka ya wajaba a kan duk wani wanda nauyin tarbiyya ya hau kansa iyaye, malamai da shugabanni ya kasance mai tarbiyya ne shi a karan kansa.
Wani mutum ya tambayi malaminsa cewa ya koya masa yadda ake yin tarbiyyar ‘ya’ya, a lokacin ‘yarsa ta fari tana wata ɗaya da haihuwa, sai malamin ya ce da shi ai kuwa ka makara. Saboda ita tarbiyya tun kafin a yi aure ake fara yin ta, ba sai an haifi ɗan ba.
Malamai sun yi bayanin siffofin da ya wajaba mai ba da tarbiyya ya siffantu da su in dai yana son ya sami nasarar aikin tarbiyya kuma ya yi tasiri.

A Taƙaice Ga Waɗannan Siffofi:

1. Ya kasance mai haƙuri da juriya da naci, kada ya ɗauka cewa tarbiyya aiki ne na sha yanzu magani yanzu.
2. Ya yarda cewa haƙƙi ne wajibi a kansa. Ya rinƙa jin haka a ransa a kowane lokaci. wannan zai hana shi yin watsi da tarbiyyar iyalinsa.
3. Ya rinƙa sa ido da lura da bibiya, saboda tarbiyya kamar dashe ne, in ba a bibiyarsa da kula da shi sai yå bushe ya lalace ko dabbobi da ƙwari su kashe shi.
4. Yi dan Allah (Ikhlasi) kar mutum ya nemi wani lada ko yabo a kan tarbiyyar ‘ya’yansa da iyalınsa sai a wurin Allah kawai. Saboda haka ban da alfahari ban da fariya ban da goranta wa ‘ya’ya da iyali ban da raina ‘ya’yan wasu.
5. Tarbiyya tana buƙatar tausasawa da bin al’amura sannu-sannu daki-daki. tsanani da gallazawa kawai ba sa kawo gyara. dole sai ana cizawa ana hurawa.
Mai ba da tarbiyya shugaba ne, saboda haka ya kamata
ya siffantu da siffofi na shugabanci ya kasance jarumi
mai adalci mai kwarjini mai iya ɗaukar nauyin
waɗanda yake jagoranta mai kyauta sauƙin kai da
saussauci a inda ya dace mai tsanani a inda ya dace, da
dai sauran siffofi na jagora ko shugaba na gari.

Harkar tarbiyya ba abu ne da ake yin sa da ka ba, lallai
sai an yi karatun tarbiyyar saboda tana farowa, tun kafin
a auri uwar da har ta haife shi ya balaga, za a yi masa
tarbiyyar jiki da imani da halaye da ladabai da haƙƙoƙi da siyasa da
sha’awa. To in ba ilmi, ta yaya wannan aiki zai yiwu?
8. Wajibi ne mai tarbiyya ya kasance mai adalci. Ya
kasance yana ɗaukar matakai na gasakiya a komai ya
daidai ta tsakanin tsanani da sassauci da sakin hannu da rowa. ya kasance tsaka-tsaki a komai.
9. Wanda yake da tsananin rowa da kankamo da masifar
son abin duniya ba zai iya tarbiyya ba. Dole ya kasance
mai sakin hannu da sakin fuska. Kada ya ɗauka asarar
kuɗi yake yi in ya biya kuɗin makaranta ko ya sai
abinci da sauran bukatun ‘ya’yansa.
10. Ya kasance mai nuna ƙauna ta gaskiya ga ‘ya’yansa
maza da mata ‘ya’yan uwar gida da na amarya.
11. Dole ne mai tarbiyya ya kasance nitsattse mai hankali da tsari a rayuwarsä.
12. Wajibi ne mai tarbiyya ya kasance ya siffantu da
kyawawan halayen da yake umarni da a aikata su. yana
nisantar munanan ayyukan da yake hanawa. Kada ya
zama fitina ga waɗanda suke a ƙarkashinsa.
13. Ya kasance mai kyakkyawan fata da sakakkiyar zuciya.
Kada ya rinƙa camfa abubuwa ko saurin siƙewa da fidda
rai kan samun nasara.
14. Ya kasance mai jin ƙai da tausayi.
15. Ya kasance mai tsoron Allah (Taƙawa) wannan sharuɗɗa
muhimmancinsa ya gawurta.

Domin karanta cikakken bayani a kan Kura – Kuran Masu Ba Da Tarbiyya danna nan.

Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Tarbiyar ‘Ya’Ya Daga Neman Aure Zuwa Girmansu wanda Shehu Usman Abubakar (Shehu Mansur Dala) ya wallafa shi domin karanta cikakken littafin danna nan.

labarin da ya wuceHukunce-hukuncen Raino
Labarin na GabaKura-kuran Masu Bayar Da Tarbiyya.