Duhun Kan Mace Mai Gaba da Kisihiya.

0
515

Haƙiƙa ba mace kidahuma, kamar matar da duhun kai ya sa ta yin gaba da kishiyarta, domin kuwa ko ga ɗabi’ar zaman tare, babu dacewa mutum ya mayar da abokin zamansa abokin gabarsa. Ballantana kuma idan an koma ga dalilai na Shari’a, ai ƙazantar hakan ta isa.

Duhun kan matar da take yin gaba da kishiyarta, yana kai ta ga munana ladabi ga Allah da Manzonsa, sannan kuma ya sa ta cutar da mijinta, da ma ita kanta.
Da farko, Allah (Subhanahu wata’ala) da ya isa da kowa da komai, shi ne ya halatta wa maza su auri fiye da mace ɗaya, idan suna da halin yin hakan inda ya ce:
Ma’ana “Ku auri abin da ya yi muku daɗi daga mata (da aka halatta muku) biyu-biyu da uku-uku da hudu-hudu”.
To yanzu don Allah ‘yan uwa, ina ladabi ga Allah a tare da matar da take yin gaba da kishiyarta? Alhali kuwa kamar yadda Allah ya halatta a zauna da ita, haka ya halatta a zauna da kishiyarta.
Sannan kuma Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: “Ku auri mata irin haihuwa, waɗanda kuke son su, su ma kuma suke son ku. Haƙiƙa ranar alƙiyama zan yi alfahari a kan sauran al’umma da yawanku”.
Ya ‘yan uwa, yanzu don Allah ba munanan ladabi ba ne ga Annabi da kuma wannan magana tasa? Idan ya zama ana gaba da wadda ta dalilinta za a samu ƙarin yawan al’ummar da Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi zai yi alfahari da ita a ranar alƙiyama? Allah dai ya sauwaƙe, amin.
Har wa yau kuma, Imamul Bukhari ya rawaito hadisi da yake ɗauke da cewa, sahabin Annabi, Abdullahi ɗan Abbas (Radiyallahu Anhu) ya ce: “Mafi alherin wannan al’umma shi ne wanda ya fi yawan mata”. Ma’ana, mai mace biyu ya fi mai ɗaya, mai uku ya fi mai biyu, mai huɗu kuma ya fi mai uku.
To, tun da mun ji haka ne, ina ƙaunar da mace mai gaba da kishiyarta take yi wa mijinta ta tafi? Ko kuwa ba ta son sa da ci gaba ne, shi ya sa take gaba da wadda zamansa da ita zai ƙara masa matsayi da ɗaukaka a wajen Allah Ta’ala?
Bugu da ƙari a kan haka, Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: “A tsokar ɗayanku akwai sadaka”. Ma’ana, saduwar miji da matarsa ibada ce mai lada; tamkar miji ya yi sadaka.

Anya kuwa ba baƙin ciki matar da take gaba da kishiyarta take yi wa mijinta ba, a game da ladan da zai samu in ya sadu da kishiyarta?
To, in ba haka ba, mene ne nata na yin gaba da kishiyarta?

Ga shi kuma Bukhari da Muslim sun rawaito hadisin da yake cewa, Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: “Ɗayanku ba zai zama mai cikakken Imani ba, har sai ya so wa ɗan’uwansa irin abin da yake so wa kansa na alheri”.
Ta yaya ne, mace mai gaba da kishiyarta za ta zama ta so wa mijinta alherin zamansa da kishiyarta? Kuma ina ƙaunar da take wa kishiyarta na samun irin alherin da ita ma take samu daga wajen mijin nasu. Kai wannan kidahumanci da yawa yake!
Ya ‘yan uwa don Allah yanzu a nan riba ce mace mai gaba da kishiyarta ta ci ko kuwa faɗuwa ta yi? Yanzu wane duhun kai ne ya fi mutum ya yi abin da zai hana imaninsa cika? Allah dai ya sauwaƙe, amin.
Bayan haka, an karɓo daga Abdullahi ɗan Umar, daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: “Mumini da yake cuɗanya da mutane, kuma ba ya haƙuri da cutarwarsu”. Bukhari ne ya rawaito shi a littafinsa Adabul Mufrad. Haka kuma Tirmizi da Ibn Majah sun rawaito shi.
A nan kuwa duba da wannan hadisi, muna iya cewa, matar da ta kasa haƙurin zama da kishiya, har ta kai ga mayar da kishiyarta tamkar abokiyar gaba, haƙiƙa ta yi wa kanta asarar ɗimbin alherin da wanda ya cuɗanya da mutane ya kuma yi haƙuri da su yake samu. Allah dai ya tsare mu da shiga duhun kai, amin.

Sannan kuma bugu da ƙari, sau da dama matar da gabarta da kishiyarta ta sa mijinta ya saki kishiyarta, tana yi wa kanta maraba ne da cutar ƙanjamau, domin sau tari mazajen da buƙatarsu ta sha’awa ta kere iya wadatuwa da mace ɗaya, suna halartar dandali-dandali da gidajen da matan banza suke taruwa, domin biyan buƙatarsu ta sha’awa, wanda galibi ta nan ne masu irin wannan halayyar suke samo cutar ƙanjamau, daga nan kuma matansu na aure da suke gida su samu daga wajensu. Allah ya kiyashe mu, amin.
Don haka ‘yan uwa mata sai a yi hattara, a kuma san da wa ya kamata a yi zaman gaba.

Domin karanta cikakken bayani a kan Wani kishi ne mafi bayyana danna nan.

Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Duhun Kai Gaba Da Kishiya wanda Abubakar Abbas ya wallafa shi domin karanta cikakken littafin danna nan

labarin da ya wuceWane Kishi ne Mafi Bayyana?
Labarin na GabaAbubuwan Dake Sa Kishiyoyi Shiri da Zaman Lafiya.