Nasiha Tsakanin Musulmi

0
777

Yin nasiha ga Musulmi a junansu wani babban tsaro ne ga imanin musulmi, ɓarna ba ta yaɗuwa a inda nasiha take aiki, saboda ana murƙushe ta ne tun tana garwashi kafin ta gagara ta zama gobarar daji.

Duk inda mutum ya ga ɗan’uwansa yana aika ta, ko furta wani abu marar kyau, wanda ya saɓa wa umarnin Allah (S.W.T) ƙarara, to lallai ne wannan mutum ya yi nasiha ga wannan ɗan’uwa nasa ta hanya mai kyau, har sai ya tsamo shi daga halaka. Haka idan ya ga ɗan’uwansa ya taƙaita ga barin aikata wani aiki ko wani hali na kirki, to aikinsa ya yi masa nasiha har sai ya dawo da shi, don ya aikata abin da Allah yake so, kuma mutum zai iya yi wa sauran al’umma nasiha ta hanyar yi musu adalci tare da kyautata aikinsa, ko sana’arsa don amfanin jama’a ba tare da cutar da su ba.
Sannan kuma, ya kamata a gane cewa ita nasiha, idan akan yi ta tsakani da Allah, to ba sai lallai wani muhimmin mutum kawai zai yi ta ga sauran jam’a ba, a’a tsakanin Uban da ɗa da wa da ƙani, da mata da miji da shugaba da talaka da ubangida da yaron gida, kowa yana iya yiwa kowa nasiha cikin ladabi da girmamawa, da neman yardar Allah. Da haka ne mutane za su taimaki kansu da kansu, su taya juna biyayya ga Allah.

• Dokoki:

Daga cikin abin dake taimaka wa mutum a kan biyayya ga Allah, da kuma saɓawa son zuciya, har da kafa dokoki waɗanda za su toshe ƙofar saɓon Allah da kafa waɗanda za su ɓullo da hanyoyin bin Allah a rahusa (cikin sauƙi).
Wannan aiki ne na shugabanni tare da sauran jama’ar gari baki ɗaya, wato lallai ne shugabannin su kafa doka, kuma su tsare ta, duk dokar da za su kafa su tabbata wadda ta dace da umarnin Allah ce, kuma duk dokar da ta saɓa umarnin Allah, lallai ne su kawar da ita ko wane ne ya zo da ita, domin idan Allah Ya ba da umarni, wani mutum ya soke umarnin Allah, su ka bi na wannan mutum, to babu shakka sun fifita shi a kan Allah, kuma duk ranar da Allah Ya kama su, shi ba zai iya ƙwatarsu ba Allah Ya gafarta mana. ameen.
Kuma aikin mutanen gari ne da su nemi shugabannin su, a kan su aiwatar musu da dokokin Allah (S.W.T.) kuma su kawar da duk wata doka da ta saɓawa umarnin Allah, sannan su taya shugabannin nasu a kan haka ta kowace hanya shari’antacciya.
Daga cikin dokokin da ya kamata a kafa su ne: Haramtawa Musulmi shan giya, sayar da ita da ɗaukan dakon ta, da bayar da hayar gidanta, ko tallata ta da haramta karuwanci da duk abin da zai taimaka a yi shi, kamar bayyana tsiraici da cuɗanyar maza da mata a wuraren taro da makarantu, da abubuwan hawa, da kaɗaitar namiji da mace marar dalili da tsananta harkar aure da sauransu.
A taƙaice a dai dokokin da za su hana dukkan miyagun ayyuka, irin su cin riba da caca da sauransu.
Sannan su yi umarni da dukkan kyawawann ayyuka, kamar ba da zakka da ayyukan ibada baki ɗaya.
Na san wannan aiki ne jajawur, amma mene aikin mutum a duniya idan ba jan aiki ba? Don haka lallai ne, mu zage dantse mu tunkari kowane aiki mai kyau mu kuma tuna da cewa Allah zai taimake mu a kan kowane aikin alheri. Allah Ya sa mu dace ameen.
Don samu sauƙin aiwatar da waɗannan dokokin. Sai an tanadidi ‘yan sanda ɗa’a, waɗanda za a ba su cikakken horo  na yadda za su yi horo da kyakkyawan aiki da hani ga mummunnan aiki, waɗanda za su bazama cikin gari a ko’ina, idan sun ga ana saɓawa dokar Allah sai su kare ta, ta hanyar ilmantarwa, ko tsawatarwa ko kamawa tare da gurfanarwa a gaban shari’a.
Abu na gaba mafi mahimmanci, kuma wanda zai sauƙaƙe aiwatar da dokokin Allah shi ne, tanadar manhajar ilmi ingantanciya wadda za ta fitar da muminin bawa, salihi, managarci , mai tsoron Allah, sai a tanadi wannan manhaja don aiwatar da ita, a dukkan makarantu na boko da na allo, da na islamiyya.
Tsarin ilmantarwa da tabiyyantarwa ba zai tsaya kan yara ko ɗalibai kawai ba, a’a, har da dukkan jama’ar gari , kowanne a tanadi hanyar da za ta dace da matsayin hankalikansa da kuma ilminsa don ɗora mutane a kan ayyukan imani da tsarkake zuciya, da neman ilmi don samun yardar Allah.
Sai da haka ne, sannan doka za ta yi tasiri, amma don an kafa doka kawai, kuma, an yi shelar ta, wannan ba zai yi tasiri ba a al’ummar da ta daɗe tana cin karenta babu babbaka, ƙarƙashin tsarin da yake ta halatta shan giya da zina da caca da kowace irin kaba’ira.
Daga nan idan muka yi nazari mutum wanda aka haifa daga iyaye masu addini, sannan ya sami tarbiyya mai kyau ta addini, kuma ya rayu tsakanin mutane masu yiwa juna nasiha, kuma a cikin al’umma wadda take da dokoki masu tsare martabar addini, babu shakka za mu ga an sami mutum nagari wanda ya yi sa’ar samun kansa cikin mutane, waɗanda za su taimake shi, su taya shi yin aikin da Allah Ya halicce shi domin sa, ba mutanen da za su yi koyo da shi, ko kuma waɗanda za su taya shaiɗan aikin ɓatar da shi da ƙarfi da yaji ba.

Wannan bayani An ciro shi ne daga littafin Ɗan Adam Kamar Yadda Allah Yake Son sa. wanda M. Aminu Isma’il Sagagi ya wallafa shi domin karanta cikakken littafin danna nan.

labarin da ya wuceNauye-nauyen Rayuwar Aure
Labarin na GabaTarbiyyar Addini
Dr. Aminu Isma'il Sagagi
An haifi Dr. Sagagi a Unguwar Sagagi cikin birnin Kano a 1968 Ya yi PhD a IUA Khartoum 2012 Ya yi aikin koyarwa a Makarantar Munazzama Kura. Ya yi koyarwa a Makarantar koyon Sharia ta Malam Aminu Kano. Ya taba rike Mukamin Mai ba wa Gwamna Shawara a kan Ilimi 2009-2011 A yanzu Malami ne a Sashin Nazarin Addinin Musulinci a Jami'ar Bayero.